'Yadda aka bar ni da gawar mahaifiyata a tsakiyar daji'

- Marubuci, By Mohamed Osman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
"Sun tafi sun bar ni da gawar mahaifiyata a cikin rairayin hamada," in ji Om Salma*, wadda masu safarar mutane suka bari a wani wuri a kan hanyarsu ta zuwa Egypt daga Sudan.
Matashiyar mai shekara 25, mahaifiyarta ta rasu ne bayan motar da suke ciki ta yi hatsari, lamarin ya janyo mahaifiyar ta faɗa waje ta tagar mota.
"Mun yi ƙoƙarin gaya wa matuƙin motar ya rage gudu," a cewar Om Salma. Amma ina! ƙaddara ta riga fata don mahaifiyar mai shekara 65 ta buda kanta ta mutu.
An saukar da Om Salma da ke kuka ba ƙaƙƙautawa daga cikin motar da sauran ƴan uwanta da kayansu.
Masu safarar sun ƙi yarda su ɗauki gawa a motarsu. Haka suka ja motarsu suka tafi suka bar su cikin firgici.
Om Salma da iyalinta na ƙoƙarin tserewa ne daga yakin da ake yi a Sudan, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a matsayin "rikici mafi girma da ke ɗaiɗaita mutane a duniya."
Fiye da mutane miliyan takwas aka tilastawa barin muhallansu tun lokacin da aka fara yaƙin tsakanin dakarun sojin ƙasar da dakarun RSF a watan Aprilun 2023.
Kuma an yi kisan cewa mutane 450,000 sun tsere daga Sudan zuwa Egypt a cikin watanni 10 da suka wuce.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A bara ne wani ƙazamin faɗa ya ɓarke a Khartoum, sakamakon rikici kan madafun iko a tsakanin shugabannin sojin ƙasar. Rikicin da ya bazu zuwa sauran sassan ƙasar kuma ya sa dumbin mutane tserewa daga gidajensu.
A yayin da yaƙin ya kusanto gidansu Om Salma da ke birnin Omdurman, tana iya jin ƙarar harbe-harben bindiga, inda ta ce: "Dole mu bar wurin nan. Mu tseratar da rayukanmu daga haɗari."
Ta ce mutane da dama sun shaida mata cewa "ba zai yiwu ba" ka samu biza a hukumance ka tafi Masar cikin gaggawa, don haka sai ta nemi wani mutum wanda ta biya $300 kan kowane mutum guda domin yin safarar iyalinta zuwa wajen ƙasar ta Sudan.
Safarar mutane abu ne da ake yi a faɗin bakin iyakar Egypt da Sudan wanda ya kai tsawon kilomita 1,200.
Dama can sun taɓa aiki a wuraren saboda haka sun san ko'ina kuma suna da damar samun manyan motoci da suke amfani da su wajen yin safarar mutane.
Om Salma da iyalinta sun je wani gari da ake kira Gabgaba da ke arewacin Sudan. Wuri ne da ya yi suna wajen da ake fara safarar mutane domin tsallaka bakin iyaka, lamarin da ya sa har mazauna wurin ke kiran sa da filin jiragen sama na Gabgaba.
An gaya wa Om Salma cewa za a yi jigilarsu ta bakin iyaka zuwa birnin Aswan da ke kudancin Egypt.
Sai da suka yi tafiyar sa'oi takwas suka tsaya suka kwana a wani wuri kafin hatsarin ya auku.
Yanzu a cikin hamada ga ƙarancin ruwan sha da abinci ga kuma gawar mahaifiyarta, sai ita da ƴan uwanta suka shiga tsaka mai wuya.

Bayan sun shafe sa'io suna jira a cikin hamada, Om Salma ta yi sa'ar tsayar da wata mota, inda ta roƙi wani direba wanda ya ɗauko abinci da kayan lataroni daga Egypt zuwa Sudan da ya ɗauke su da kuma gawar mahaifiyarsu zuwa Abu Hamad, wani wuri da suka taɓa tsayawa a baya.
Sun isa wurin lafiya kuma sun samu binne mahaifiyarta a nan.
Da fari mutane ba sa son yi musu magana, amma daga bisani da suka fara kula su, sai Om Salma ta gano cewa ba su ne na fari da irin hakan ta taɓa faruwa da su ba.
Ana yawan samun hatsari saboda yadda masu safarar ke tuƙa motoci a guje don kaucewa hukumomi tare da samun tsallaka bakin iyakar, lamarin da ke kai ga rasa rayuka akai-akai.
Wani mutum da ake kira Ibrahim*, wanda a yanzu yake Cairo, ya ce lokacin da aka yi safararsa, akwai wani mutum da ke tafiya tare da shi wanda ya karya wuyansa kuma daga bisani ya mutu bayan da motar da suke ciki ta yi hatsari.
Ibrahim ya ce mutumin da ya mutu na tafiya ne shi kadai ba tare da wani ɗanuwa ba, kuma duk da nacin da waɗanda aka yi safararsu suka yi na cewa ka da a bar gawarsa, ƴan safarar suka ƙi amincewa inda suka binne gawar mutumin a hamadar.
“Kowa ya firgice, na kalli kabarin da aka binne mutumin daga taga lokacin da muka ci gaba da tafiya, yayin da mata da yaran da ke cikin motar suka ci gaba da kuka,” in ji Ibrahim.
Fashi da sata kuma ya zama ruwan dare. Halima* mai shekara 60, ta ce ta ji wani abin ban tsoro lokacin da aka yi safarar ta tare da danginta a hamadar Sudan kafin ta isa Masar.
“Wasu ‘yan bindiga da suka rufe fuskokinsu guda hudu suka kai mana hari a lokacin da babbar motarmu ta lalace, inda suka yi harbi a iska, suka kuma mari ‘yar ta tare da sace mana kayanmu,” inji ta, kafin su gudu lokacin da wata mota ta zo.
An yi sa'a direban motar ya yarda ya taimaka musu ya wuce da su kan iyaka.
Sai dai Halima ta ce ‘yarta mai shekara 25 ta tsorata da firgita wanda hakan ya yi sanadin mutuwarta washegarin da suka isa Masar.
"Ƴata ta shiga cikin firgici sosai wanda hakan ya sa ta kasa numfashi," in ji Halima, inda ta ƙara da cewa kuma an kasa samun taimakon likita a cikin lokaci.
BBC ta ga kwafin takardar shaidar mutuwarta, wanda ya bayyana matsalolin numfashi a matsayin musabbabin mutuwar.

BBC ta tuntubi gwamnatin Masar don tambayar ko me take yi na magance safarar mutane daga Sudan amma ba mu samu amsa ba.
Abdel Qader Abdullah na karamin ofishin jakadancin Sudan da ke Aswan a kudancin Masar ya shaida wa BBC cewa haramun ne saɓa doka ne a ƙeta iyakokin hamada ba tare da biza ba, kuma hukumomi sun ƙaddamar da wani shiri na gargadi kan illolin da ke tattare da safarar mutane.
Abdullah ya kara da cewa: karamin ofishin jakadancin Sudan da ke Aswan yana aiki tare da gwamnatin Masar don taimakawa wajen gaggauta gudanar da biza, domin a taimaka wajen kara yawan wadanda aka amince da su ƙetare iyakokin hamadar da kuma ba da damar karin mutanen Sudan shiga kasar bisa doka.
A baya, ana barin mata da yara ƙanana shiga Masar ba tare da biza ba amma gwamnati ta kawo sabbin takunkumi bayan ɓarkewar faɗa a Sudan.
Bukatar neman bizar Masar na da yawa a Sudan, saboda mutane na son tserewa rikicin.
Za su iya neman bizar Masar a wurare biyu a Sudan - Wadi Halfa a arewa da Port Sudan a gabas.
Amma yawancinsu sun fi bin hanyar zuwa Wadi Halfa saboda ya fi kusa da Argeen, babban birnin da ke kan iyakar kasa tsakanin Sudan da Masar. Amma kuma kusan babu ababen more rayuwa a Wadi Halfa.
Mutanen da ke neman biza suna bin dogon layi na sa'o'i domin su samu. Bayan neman biza, yana iya ɗaukar watanni don gano ko an sami nasarar samun su.
Waɗanda suka rasa matsugunansu kuma masu kuɗi kaɗan suna jira a Wadi Halfa don jin labari game da bizar tasu, suna kwana a duk inda za su iya, a makarantu da ke kusa ko a kan tituna.
Om Salma, wadda har yanzu ta kuduri aniyar ficewa daga Sudan, ta yanke shawarar gwada bin halastacciyar hanya da doka ta amince da ita a yunkurinta na biyu inda ta yi tafiya zuwa Port Sudan don neman biza a karamin ofishin jakadancin Masar da ke can.
Amma bayan jira na wata biyu, sai ta hakura ta sake zaɓar hanyar da doka ta haramta.
An dai hana mutane da yawa biza wanda kuma ba za su iya jira ba, saboda haka suka yanke shawarar kashe ɗan kuɗin da suke da shi kan mai fasa kwauri don fitar da su daga ƙasar.
Om Salma ta ce ta koyi darasi daga mugunyar yunkurin da ta yi na farko, inda ta tunkari wani dan fasa kwauri na daban.
"Mun shafe kusan kwanaki shida a cikin hamada," in ji ta, kafin muka yi nasarar tsallake kan iyaka zuwa kudancin Masar.

Da zarar sun isa Masar, halin da 'yan ciranin Sudan ke ciki bai kare ba. Idan ba su da matsayin 'yan gudun hijira ko kuma ba za su iya tabbatar da cewa suna da ƙarfin nema ba, za a iya fitar da su.
Wajen neman matsayin ƴan gudun hijira, dole ne su yi tafiya zuwa Alkahira ko Alexandria.
A cibiyar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da ke birnin Alkahira, dubban bakin haure 'yan kasar Sudan, galibinsu mata da ƙananan yara ne ke tsaye cikin dogayen layukan da suke jiran rajistar sunayensu da kuma karɓar abin da aka fi sani da katin rigakafin cutar shawara.
Halima ta ce "ta tsaya a cikin sanyi na tsawon sa'o'i, saboda ta samu ta haɗu da waɗanda za su ba ta matsayin ƴar gudun hijira da zai ɗauki tsawon wata hudu kafin ya fito".
"Samun katin rigakafin cutar shawara, wanda za ku samu da zarar kun kasance ƴan gudun hijirar Majalisar Dinkin Duniya, zai ba ku damar samun aiki bisa doka kuma ku karbi kudade na kowane wata daga Majalisar Dinkin Duniya," in ji ta.
Ko da yake wata 'yar gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya mai rijista, Ibtessam*, ta gaya mini ba abu ba ne mai sauƙi.
An yi safarar Ibtessam daga Sudan zuwa Masar a bazarar da ta gabata tare da tsararraki uku na danginta, 17 daga cikinsu, ciki har da iyayenta da 'ya'yanta.
Sai dai ta ce duk da cewa tana da katin rigakafin cutar shawara, ba ta samu wani kudi ba tun zuwanta a watan Yuni.
"Ban san yadda zan iya ciyar da iyalina ba, mijina ya rasu, ina da kudin haya da kudin makaranta da ban biya ba kuma babu mai taimaka mana."
Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR Christin Bishay ta amince da bacin rai da wahalhalun da bakin haure na Sudan ke ciki a Masar amma ta ce hukumar na fuskantar karancin kudade.
"Mun fadada karfinmu da kaso 900 don haka dole ne mu ba da fifiko kuma mu yi tunani kan ko wane ne ya fi buƙatar taimako", ta kara da cewa: "Mun kafa ayyukan kiwon lafiya a kan iyaka tare da taimakon Red Crescent na Masar."
Rayuwa ba ta da sauƙi ga baƙin haure Sudanawa a Masar, kamar Om Salma, wadda dole ne ta sami wurin zama da ɗan taimako ko kuɗi.
Ta gaya mani cewa tana cikin damuwa game da gaba, tana da burin komawa ƙasarta wata rana, amma saboda rikicin Sudan, tana tsoron hakan ba laile ya taɓa faruwa.











