Wasu mata sun shigar da ƙara saboda rashin basu damar zubar da ciki

.

Wasu mata biyar da suka ce an hana su damar zubar da ciki a jihar Texas ta Amurka, duk da cewa sun ce rayuwarsu ta fuskanci haɗura daban-daban, sun shigar da ƙarar jihar kan haramta musu zubar da ciki.

Texas ta haramta zubar da ciki har sai in akwai buƙatar lafiya ta gaggawa kan haka, inda likitocin da aka kama da laifi ake yanke musu hukuncin ɗaurin shekara 99 a gidan yari.

A cikin ƙarar da matan suka shigar, sun ce likitoci suna kin zubar da ciki ko da akwai buƙatar lafiya a ciki saboda tsoron hukunci.

A cikin wata sanarwa, ofishin Antoni Janar na jihar Ken Paxton, ya ce zai zartas da dokokin jihar da aka amince da su.

Cibiyar kare haƙƙin mata a fannin haihuwa, ta shigar da ƙarar a madadin matan guda biyar – Ashley Brandt da Lauren Hall da Lauren Miller da Anna Zargarian da kuma Amanda Zurawski – da kuma wasu jami’an bayar da agajin lafiya guda biyu.

Cibiyar ta ce wannan ne karon farko da mata masu ciki suka ɗauki mataki da kansu kan adawa da dokar haramta zubar da ciki da aka zartas a faɗin Amurka tun bayan da Kotun Kolin ƙasar ta cire kariya da kundin tsarin mulki ya bai wa masu zub da ciki a bara.

"A yanzu, abu ne mai haɗari mace ta ɗauki ciki a Texas,’’ in ji Nancy Northup, shugabar cibiyar.

.
Bayanan hoto, Nan, masu rajin kare hakkin masu zubar da ciki ne ke zanga-zanga a Texas.

A lokacin da Ms Northup ke wajen majalisar dokokin jihar Texas a Austin a ranar Talata – biyu daga cikin matan da suka shigar da ƙarar – sun bayyana labarai marasa daɗi na yadda suka rasa juna biyu da suke ɗauke da shi a baya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar ƙarar da suka shigar, an faɗa musu cewa abin da suke ɗauke da shi ba zai rayu ba, amma ba a basu damar zubar da ciki, abun da suka kwatanta da “tsarin lafiya mai inganci” a faɗin ƙasar da kuma jihar kafin dokar haramcin ta fara aiki a Texas.

Ms Zurawski, mai shekara 35, ta ce ta samu juna biyu bayan magani da likitoci suka yi mata tsawon wata 18. Cikin nata ya fara girma kafin nan aka gaya mata cewa ya zube wanda kuma tuni dama ita da mijinta suka riga da saka wa jaririn suna Willow.

"Duk da cewa mun rasa Willow, likitan da ke kula da ni bai iya kawo wani ɗauki ba a lokacin da zuciyarta ke bugawa ko kuma har jami’an asibiti suka zo suka ce rayuwata na cikin haɗari,’’ in ji Mis Zurawski.

A tsawon kwana uku da ta kwashe cikin mawuyacin hali a asibiti, an tilasta wa Mrs Zurawski zama a asibiti har sai da jikinta ya kai wani mataki – wanda irin yanayin ne in mace ta shiga, sannan doka ta ba da damar a zubar da ciki.

Mrs Zurawski ta ɗauki kwana uku cikin ɗakin bayar da agajin gaggawa, inda ta bar asibiti bayan mako ɗaya. Lamarin ya janyo mata wahala wajen ɗaukar ciki na gaba.

Sai da sauran matan guda huɗu suka fice daga Texas, kafin su samu damar zubar da ciki.

Ɗaya daga cikin matan, Mrs Miller, ta ce “Bai kamata ‘yan siyasa su zamo su ke da iko da tsarin kiwon lafiya ba tare da sun san yanda magani yake ba ko kuma muhimmancin zubar da ciki a rayuwar mai juna biyu.

"Ta ya ya za a ce zan iya zubar da cikin ƙare, amma ba zan iya zubar da nawa ba?”

Cikin biyu daga cikin matan na wani mataki da ke nufin ba su samu matsala a kwakwalwarsu ba, a cewar ƙarar.

Waɗannan labaran kaɗan ne daga cikin irin wahalhalu da mata ke fuskanta,’’ in ji Mrs Northup.

A cikin wata takarda ɗauke da korafe-korafensu mai shafuka 91, suna buƙaci Texas ta sake duba batun dokar haramta zubar da ciki la'akari da irin barazanar lafiya da mata masu ciki ke fuskanta.

"Ba abin mamaki ba ne, yanda likitoci ke ƙin karɓar mata don zubar musu da ciki ko da waɗanda ke cikin tsananin buƙatar agajin lafiya na gaggawa duba da barazanar rasa lasisinsu na aiki da cin tara ta dubban daloli da kuma ɗaurin shekara 99 a gidan yari,’’ a cewar ƙarar.

A cewar wani bincike da wata cibiya ta gudanar a bara, ta ce kashi 61 na Amurkawa sun ce ya kamata a halasta zubar da ciki ta kowane yanayi, duk da cewa kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa wasu mutane ba sa goyon bayan haka.

Dokar Texas wadda ke ƙarƙashin ikon jam’iyyar Republican, tana sahun gaba kan adawa da zubar da ciki, inda ta zama jiha ta farko da ta zartas da dokar ta haramcin zubar da ciki kwata-kwata.

Nan gaba kaɗan, jihar za ta zama gida kuma wajen ce-ce-ku-ce kan zubar da ciki: ana sa ran wani lauya a Texas ɗin zai yanke hukunci kan wata ƙara a kan magungunan zubar da ciki a makon nan.

Lauyan wanda tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ya naɗa a lokacinsa, mai suna Matthew Kacsmaryk, zai yanke hukuncin cewa ko ɗaya daga cikin kwayar maganin wadda ake amfani da ita wajen zubar da ciki mai suna Mifepristone – za a ci gaba da sayar da ita a Amurka.