Faransa ta samu gurbin buga gasar Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta samu gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2024 duk da saura wasa bibiyu ya rage a cikin rukni.
Ranar Juma'a Faransa ta je Netherlands ta yi nasara da ci 2-1 a karawar rukuni na biyu.
Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallo biyu, na farko a minti na bakwai da fara wasa a Amsterdam, sannan ya zura na biyu a raga a zagaye na biyu.
Netherlands ta yi nasarar zare kwallo daya ta hannun Quilindschy Hartman, saura minti bakwai a tashi daga fafatawar.
Kenan kungiyar da Didier Decchamps ke jan ragama ta lashe dukkan wasa shida na cikin rukuni da maki 18.
Faransa ta bi sahun wadanda tuni suka samu gurbin buga gasar da za a yi a shekara mai zuwa da suka hada da Belgium da Portugal da mai masaukin baki Jamus.
Netherland, wadda ta yi rashin nasara tana mataki na uku da tazarar maki uku tsakaninta da Girka ta biyu a teburi na biyu.







