Mece ce cutar anthrax kuma ta yaya take kisa?

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a ranar Litinin, ta bayar da rahoton ɓullar mura mai tsanani ta anthrax a wasu ƙasashe da ke gabashi da kudancin Afirka.

WHO ta ce fiye da mutum 1,100 ne ake zargi sun kamu da cutar, an tabbatar da mutum 37 da suka kamu da cutar, sai mutum 20 da suka mutu a baya-bayan nan a Kenya da Malawi da Uganda da Zambia da Zimbabwe.

WHO ta bayyana cewa cutar ta zama annoba a ƙasashen inda kuma ake samun ɓarkewarta lokaci zuwa lokaci duk shekara.

Daga cikin ƙasashen biyar, Zambia ce ta fi fuskantar ɓarkewar cutar fiye da sauran ƙasashen, inda cutar ta bazu a Larduna tara daga cikin 10.

Zambia ta ba da rahoton mutum 684 da ake zargi sun kamu da cutar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba. An tabbatar da cutar ta kama mutum 25 sai wasu huɗu da ska mutu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar.

Ya cutar anthrax ke shafar bil adama?

Sunan cutar ya samo asali daga anthrakis, kalma ta Girka da ke nufin kwal saboda cutar anthrax da ke shafar fata na janyo rauni ga fata.

Cutar da ta shafi numfashi ta fi shafar dabbobi amma tana iya shafar bil adama idan suka yi mu'amala da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka sha abin da dabbobin ke samarwa.

Ƙwayar cutar Bacillus anthracis ce ke haddasa cutar kuma tana rayuwa cikin ƙasa tsawon shekaru kafin ta shiga jikin dabbobi idan suka ji rauni ko suka yanke.

Alamomin cutar anthrax

Cutar anthrax na bayyana ne ta daya daga cikin hanyoyi uku, in ji WHO:

  • Wadda ke shafar fata: inda ake iya ɗauka idan aka ji ciwo. Wannan ce hanyar da aka fi ɗaukar cutar sai dai ba ta da haɗari sosai. Alamarta na somawa ne da ƙurji a jikin fata sai ya zama maruru. Wasu suna fama da ciwon kai da ciwon gaɓoɓi da zazzaɓi da amai.
  • Wadda ke shafar ciki na soma nuna alamomin da suke kama da na cin abinci mai guba sai dai tana iya ta'azzara zuwa matsanancin ciwon ciki da aman jini da kuma gudawa mai tsanani.
  • Wadda ke shafar numfashi - ita ce mafi tsanani kuma tana somawa ne da kamar mura daga baya ta rikide zuwa rashin iya numfashi yadda ya kamata.

Yadda cutar anthrax ke iya kisa

Mutane da suka kamu da cutar na buƙatar kulawar likitoci. Ana iya yi wa mutanen da suka kamu da cutar magani. Cutar tana yin sauƙi idan aka sha maganin kashe ƙwayoyin cuta musamman penicilin, sai dai akwai buƙatar a soma ba su kulawa da zarar sun kamu da cutar.

Rashin maganin na sa kusan kashi 20 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar anthrax ta fata su mutu, in ji hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa a Amurka. Sai dai idan aka yi magani yadda ya kamata, kusan duka marasa lafiyar da suke fama da cutar anthrax ta fata su kan rayu.

Cutar anthrax ta ciki wadda ke farawa idan aka yi amfani da naman dabbar da ta kamu - a mafi yawan lokuta na haifar da asarar rai. Fiye da rabin marasa lafiyar da ke fama da irin wannan cutar suna mutuwa idan ba su samu kulawa ba. Sai dai idan aka basu kulawar da ta kamata, kashi 60 cikin 100 na marasa lafiyar suna rayuwa, in ji hukumar.

Ana ganin cutar anthrax ta numfashi a matsayin wadda ta fi kisa wadda ake samu idan aka shaƙi wasu ƙwayoyin cuta. Cutar na janyo asarar rai a mafi yawa lokuta idan ba a sami kulawa sosai ba amma idan aka dage da yin magani, kusa kashi 55 cikin 100 na masu fama da cutar suna rayuwa, in ji hukumar ta CDC.

Yadda ake iya amfana daga cutar anthrax

Abu ne mai yiwuwa a iya mayar da cutar ta anthrax a matsayin wani makami saboda ana sauƙin gano ƙwayoyin cutar anthrax a ban ƙasa ana kuma iya haɗa su a ɗakin gwaje-gwaje kuma suna iya daɗewa a raye, in ji CDC.

Akwai buƙatar a samu manya-manyan kayan aiki da kuma nemo asalin ƙwayar cutar da ke haifar da anthrax domin fara gwaji.

Ana iya sakinsu ba tare da kowa ya sani ba. Ana iya sa ƙwayoyin cutar cikin hoda da abin feshi da abinci da ruwa amma ba a iya ganinsu cikin sauƙi ko jin ƙanshinsu ko ma ɗanɗana su cikin sauƙi.

A wani hari a shekarar 2001, an aike da cutar athrax ga ofisoshin ƴan siyasa da gidajen yaɗa labaran Amurka, ƴan kwanaki bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumba.