Halin da jihohin Najeriya za su shiga idan gwamnatin tarayya ta hana su kason kuɗi daga Abuja

Sababbin takardun Naira

Asalin hoton, CBN

Bayanan hoto, Hukumar rarraba arzikin ƙasa ta ce ta raba wa gwamnatin tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi naira tiriliyan 1.298 a watan Oktoban 2024
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Umarnin da wata kotu ta bayar a ranar Laraba da ke hana gwamnatin tarayya bai wa jihar Rivers kasonta daga lalitar rabon arzikin ƙasa ya jawo muhawara tsakanin masu nazari a ƙasar.

Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa babban bankin Najeriya CBN umarnin, ta na mai cewa gabatar da kasafin kuɗin da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Kazalika, alƙaliyar ta ce kuɗaɗen kason da gwamnan yake karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa Oktoba ya saɓa doka, kuma dole a dakatar da shi.

Hakan dai ta taɓa faruwa a shekarar 2004, lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya riƙe kason ƙananan hukumomi na gwamnatin jihar Legas da ke kudancin ƙasar saboda ƙirƙirar sababbin ƙananan hukumomi 37.

Rahotonni na cewa Gwamna Fubara ya ɗaukaka ƙara game da hukuncin babbar kotun da ta ba da umarnin daina bai wa jiharsa kason kuɗin.

Babban abin da ya fi jan hankalin masu lura da al'amuran yau da kullum shi ne irin halin da jihohi za su shiga idan babu kaso daga gwamnatin Abuja.

Me doka ta ce game da tsarin kasafta arzikin ƙasa?

Harkar kasafta arzikin ƙasa tsakanin matakin gwamnati uku a Najeriya na cikin kuɗin tsarin mulkin ƙasar.

Ayar kundin mulkin ta tanadi cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki kashi 52.68 cikin 100, gwamnatocin jiha su ɗauki kashi 26.72, ƙananan hukumomi kuma su samu kashi 20.60 cikin 100 na arzikin da ƙasa ta samu duk wata.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sannan ana bai wa kowace jiha nata kason ne gwargwadon girman ƙasarta, da yawan al'umma domin cim ma daidaito tsakanin jihohin ƙasar 36 - ban da Abuja babban birnin tarayya.

Sai dai a watan Disamban 2004 kotun ƙoli ta yi fatali da matakin Obasanjo na hana ƙananan hukumomin Legas kasonsu, inda ta ce ya saɓa wa kundin tsarin mulki. Amma sai a 2007 tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Yar'Adua ya mayar wa Legas kuɗin nata sama da naira biliyan 10.

Amma a wannan karon, kotun tarayya na cewa ne 'yanmajalisar da gwamnan Rvivers ya gabatar wa kasafin kuɗinsa ba su ne cikakkun 'yanmajalisa ba, amma gwamnan ya yi hakan ne saboda shi ma yana kallon sauran 'yanmajalisar a matsayin haramtattu saboda sun fice daga jam'iyyar da aka zaɓe su a tutarta.

Yanzu dai za a zuba ido don ganin hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke game da lamarin, kuma duk wanda hukuncin bai yi wa daɗi ba zai iya zuwa kotun ƙoli, wadda ta yi watsi da irin matakin a 2004.

Hukumar rarraba arzikin ƙasa ta ce ta raba wa matakan gwamnatin uku naira tiriliyan 1.298 a watan Oktoban nan bayan an same su a watan Satumban da ya gabata.

Ta ce an samu ƙarin kashi 7.9 cikin 100 idan aka kwatanta da tiriliyan 1.203 da aka raba a wata kafin wannan.

Jihohi biyar kacal

Wani rahoto da cibiyar BudgtIT ta fitar a watan Oktoban 2024 ya nuna cewa jihohin Najeriya 31 sun dogara ne kacokam kan kason kuɗin da suke samu daga gwamnatin tarayya.

Rahoton binciken ya sanya jihohin Rivers, da Legas, da Anambra, da Kwara, da Cross River a matsayin jihohin da su kaɗai ne ba su fiya dogaro kan kuɗin da suke karɓa daga kasonsu na gwamnatin tarayya ba a 2023.

"Hakan na nufin halin da za a shiga [idan babu kason kuɗi daga Abuja] ba zai ma misaltu ba," in ji Malam Abubakar Aliyu, wani masanin tatalin arziki.

"Ba za a iya biyan albashi ba, ba za a iya biyan 'yan kwangila ba, ba za a iya samun kuɗin gudanar da gwamnati ba," a cewarsa.

Cibiyar BudgIT ta ce waɗancan jihohin biyar ne kaɗai ke da yiwuwar iya gudanar da harkokinsu da iya kuɗin da suke samu a cikin gida idan da a ce za su rayu ba tare da kaso daga gwamnatin tarayya ba.

"Sauran 31 dole ne sai sun gyara hanyoyin samun kuɗinsu kafin su iya yin wata rayuwa ba tare da kasafin kuɗi daga Abuja ba," a cewar binciken BudgIT.

Jihar Kano da ta fi kowa yawan al'umma a arewacin Najeriya ta karɓi naira biliyan 16.328 a matsayin kasonta na watan Yulin 2024.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya ce daga watan Nuwamba mai zuwa yawan albashin da jihar ke biya zai kai kusan naira biliyan bakwai duk wata - saboda sabon mafi ƙanƙantar albashi na N71,000 da za ta fara biya.