Wane ne babban jami'in Hamas da Isra'ila ta kai wa hari a Qatar?

Lokacin karatu: Minti 4

Isra'ila ta kai harin ba-zata kan babban mai shiga tsakani na ƙungiyar Hamas, Khalil al-Hayya, ranar Talata a birnin Doha na ƙasar Qatar.

Kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito wani jami'in gwamnatin ƙasar na cewa wakilan Hamas ɗin da aka kai wa hari sun haɗa da Khalil al-Hayya da kuma Zaher Jabarin, jagorantar Hamas a gaɓar yamma da kogin Jordan.

Hamas ta ce an kashe mabobinta biyar amma ba a yi nasarar kashe manyan jami'an nata.

Lamarin ya janyo suka daga ƙasashen duniya, inda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya ce ''Wannan babban cin mutunci ne ga ƴancin cin gashin kai na Qatar''.

Ita ma gwamnatin Qatar ta mayar da martani da kakkausar suka a kan batun.

Ta ce harin ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa kuma hali ne raggwanci.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Qatar ta ce an kashe wani jami'in tsaronta a yayin harin.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce "akwai cikakkiyar hujjar kai harin" saboda hari ne da aka kai kan manyan shugabannin Hamas da suka kitsa harin ranar 7 ga watan Otkoban 2023 kan Isra'ila."

Mai shiga tsakani na ƙungiyar Hamas

Tun daga farkon yaƙin Gaza na yanzu, Khalil al-Hayya ya kasance babban mai shiga tsakani mai wakiltar Hamas inda ya ke isar da saƙonni da kuma karɓar su tsakanin wakilan Isra'ila da Hamas da kuma wakilan Amurka da Qatar da ma Masar, masu shiga tsakani.

Ya ci gaba da zama jigo a shugabancin Hamas tun bayan kisan Ismail Haniyeh da kuma Yahya Sinwar a bara.

Amma wane ne shi?

An haifi Khalil Ismail Ibrahim al-Hayya, wanda ake wa laƙabi da "Abu Osama," ne a cikin watan Janairun 1960 a Zirin Gaza.

Al-Hayya ya yi digirinsa na farko da na biyu da kuma digirin digirgir duk a fannin shari'ar Musulunci, kuma ya yi suna wajen aikin rajin kare haƙƙin Falasɗinawa a 1980.

Tun daga 1987 da aka kafa Hamas ya ke cikinta. Al-Hayya ya shafe shekara uku a gidan yarin Ira'ila a shekarar 1990 lokacin da aka tuhume shi da ayyukan ta'adanci.

A 2006, ya shiga takarar majalisar dokoki kuma ya yi nasara a ƙarƙashin ƙungiyar Hamas, inda daga baya ya zamo jigon ƙungiyar a zauren majalisar.

Sau biyu ana kai harin bam a gidansa, a 2007 da kuma 2014, a wani yunƙuri na neman kawar da shi.

An kashe ƴan'uwansa da dama a hare-haren biyu. An kuma kashe wasu ƴan'uwan nasa a hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza a matsayin martani ga wanda Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Okoba.

Barazanar kisa daga Isra'ila

A watan Mayun 2025, ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya fito fili ya yi barazanar kashe al-Hayya.

Wakilin na Hamas yana da kusanci sosai da Iran kuma shi ne ya jagoranci tawagar tattaunawa da Hamas zuwa Syria a shekarar 2022, domin ganawa da shugaba Bashar al-Assad.

Maƙasudin tattaunawar shi ne inganta alaƙa da Syria.

A watan Nuwamban 2023 ya jagoranci wata tawaga zuwa Lebanon, inda suka gana da Hassan Nasrallah, sakatare janar na ƙungiyar Hezbollah.

Tun daga watan Okoban 2023, al-Hayya yake jagorantar tataunawa da wakilan Hamas da kuma na Isra'ila. Kuma Qatar ta bai wa ɓangaren siyasar Hamas mazauni tun daga 2012 inda ta ke bayar da gudunmawa wajen sasanci tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi da juna.

Hamas ta ce an kai harin ne kan wakilanta

Hamas ta ce wakilanta da suka halarci zaman tattaunawa a Doha ne Ira'ila ta kai wa hari a ranar Talata, amma sun tsallake. Sai dai ƙungiyar ta ce akwai wasu mambobinta shida da aka kashe a harin, ciki har da ɗan al-Hayya, Humam Al-Hayya, da kuma darakta a ofishinsa, Jihad Labad.

"Muna tabbtar da cewa maƙiyanmu ba su yi nasara ba a ƙoƙarinsu na kisan wakilanmu da suka halarci zaman tataunawar," in ji wata sanarwa da Hamas ta fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa "a bayyane yake cewa Netanyahu da gwamnainsa ba sa fatan a cimma yarjejeniyar sagaita wuta domin samun zaman lafiya".