Isak ya fi son komawa Liverpool, De Bruyne ya tattauna da San Diego

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaban Newcastle, Alexander Isak da Barcelona ke zawarci zai fi ƙaunar komawa taka leda a Liverpool idan suka shiga neman ɗan wasan Sweden ɗin mai shekara 25 (El Nacional - in Spanish)
Ɗanwasan tsakiyar Belgium mai shekara 33, Kevin De Bruyne, ya tattauna da ƙungiyar gasar MLS, San Diego, game da komawarsa ƙungiyar idan kwangilarsa da Manchester City ta ƙare a ƙarshen kakar wasan bana. (Sun)
Harry Kane mai shekara 31, yana tunanin komawa taka leda a gasar firimiya ta Ingila, kuma ana tunanin ɗan wasan gaban Bayern Munich ɗin ya fi karkata ga Liverpool. (Fichajes - in Spanish)
Chelsea za ta biya Manchester United £5m idan ba ta kammala cinikin ɗanwasan gaban Ingila mai shekara 24 da ke zaman aro a wajenta, Jadon Sancho ba. (Athletic - subscription required)
Tottenham na nazari kan cinikin ɗan wasan tsakiyar Southampton da Ingila mai shekara 19, Tyler Dibling. (Givemesport)
Liverpool na fatan sanya ɗanwasan gefen Scotland mai shekara 19, Ben Doak a ƙa'idojin cinikin ɗanwasan bayan Bournemouth da Hungary mai shekara 21, Milos Kerkez ko kuma ɗanwasan gaban Ghana mai shekara 25, Antoine Semenyo. (Sun)
Liverpool na shirin sayar da ɗanwasan gabanta ɗan ƙasar Uruguay mai shekara 25, Darwin Nunez a ƙarshen kakkar wasan bana. (Football Insider)
Tottenham za ta shiga tattaunawar tsawaita kwangilar ɗanwasanta ɗan ƙasar Uruguay, Rodrigo Bentancur, yayin darahotanni ke alaƙanta shi da komawa AC MIlan. (TBR Football)
Ɗanwasan bayan Ingila mai shekara 18, Caleb Kporha na shirin barin Crystal Palace a ƙyauta, a ƙarshen kakar wasan bana. (Football Insider)
Ɗanwasan bayan Aston Villa mai shekara 32, Tyrone Mings zai shiga kwamitin daraktocin shirya gasar Euro 2028 domin rtaimakawa wajen gudanar da gasar cikin nasara. (Telegraph - subscription required)














