Yadda ake rufe makarantu a Najeriya saboda satar ɗalibai

Tun bayan da ƴanbindiga suka sace ɗalibai a makarantun sakandare na jihohin Kebbi da Neja wasu jihohi da gwamnatin tarayya suka ɗauki matakan rufe wasu makarantun ƙasar.
Hukumomin sun ce sun ɗauki matakin ne kan damuwar da ake da ita game da yadda matsalar sace ɗalibai ta sake kunno kai a Najeriya.
A ranar Alhamis da dare ne wasu ƴanbindiga riƙe da makamai suka far wa sakandiren da ke jihar Neja tare da sace ɗalibai fiye da 300 da malamansu 12.
Kafin wannan, 'yanbindiga sun sace ɗalibai mata 25 a wata sakandare da ke garin Maga na ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a ihar Kebbi, amma biyu sun kuɓuta daga ciki.

Matakan rufe makarantun sun haifar da ɗimuwa da firgici tsakanin al'uumar ƙasar, amma hukumomi na cewa shiri ne na kauce wa jefa yara da iyayensu cikin alhini.
Wasu makarantun sakandiren gwamnatin tarayya

Asalin hoton, Tunji Alausa/X
Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantun haɗaka na tarayya 41 da ke ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatan ilimin ƙasar ta fitar ta ambato ministan limin ƙasar, Tunji Alausa na bayar da izinin rufe makarantun haɗakar 41 na tarayya, ba tare da ɓata-lokaci ba.
Ministan ya ce sakamakon sabon ƙalubalen tsaro da ya kunno a wasu sassan Najeriya dole a ɗauki matakin da ya dace kuma a matsayin wani kandagarki.
Sanarwar ta kuma buƙaci shugabannin makarantun da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar wa tareda bin wannan umarni sau da ƙafa.
Ko da yake sanarwar ta yi nuni da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, sai dai ba ta sanar da ranar da za a buɗe su ba.
Makarantun sakandiren Katsina

Asalin hoton, Dikko Radda/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe duka makarantun sakandiren faɗin jihar saboda dalilai na tsaro da satar ɗalibai a wasu jihohi.
Kwamishinan ilimi na jihar Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne saboda abubuwan da ke faruwa a maƙwabtan jihohi na satar satar ɗalibai.
''Kan haka ne muka ƙara tsananta matakan tsaron da muke ɗauka a makarantunmu, Bahaushe na cewa idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta shafa wa naka ruwa'', in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, bayan komai ya daidaita za su umarci ɗaliban su koma makarantun domin rubuta jarrabawar ƙarshen zango, wadda ita ce dama yanzu ta rage.
Ya ce matakin ya shafi duka makarantun sakandire da ke faɗin jihar, ban da na furamare, kodayake ya ce su ma idan hali ya yi za su rufe su.
''Mun yi haka ne saboda ɗaukar matakan kariya, bai kamata ba kana jiyo matsala a nesa sannan ka tsaya ta ƙaraso inda kake'', in ji shi.
Makarantun Filato

Asalin hoton, Caleb Muftwang
Ma'aikatar ilimi ta jihar Filato ta bayar da umarnin rufe duka makarantun jihar na furamare da sakandire sakamakon ƙaruwar matsalar satar ɗalibai a ƙasar.
Hukumar Ilimi a matakin farko ta jihar, PSUBEB ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin matakin kariya ga ɗaliban jihar.
Ma'aikatar ilimin jihar ta ce matakin na wucin-gadi ne kuma ya zama dole, la'akari da halin da ake ciki.
Cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta buƙaci duka masu ruwa da tsaki a harkar makarantu su yi biyayya wa umarnin.
Matakin ya shafi duka makarantun sakandire na ƙananan sakandire da na furamare.
Sace mutane don neman kuɗin fansa da 'yan bindiga kan yi a Najeriya dai, ya zama wata gagarumar matsalar da ke matukar ci wa jama'a tuwo a ƙwarya a wurare da dama na ƙasar.
Duk kuwa da cewar hukumomin ƙasar na cewar suna ɗaukar matakai, matakai kai matsalar da ma halaka wasu daga cikin manyan ƴanbindiga da suka addabi jihohin Sokoto, da Zamfara, da Katsina, da Kaduna, da Kebbi, ma tsalar na ci gaba da yi wa jami'an tsaron na najeriya abun da hausawa ke cewar bugun kiɗan ƴan amada.
A baya-bayannan an samu dawowar hare-hare kan makarantu da sace ɗalibai bayan kwashe kimanin shekara guda da samun sauƙin al'amarin.










