Me soke amfani da harshen uwa wajen koyar da ƴan firamare ke nufi?

Hoton wasu yara 'yan firamare suna tafiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekara uku da suka wuce aka ɓullo da tsarin koyarwar da harshen uwa saboda tunanin cewa yara sun fi koyo a cikin harshen
    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Najerita ta soke tsarin nan da ta ɓullo da shi shekara uku da ta wuce wanda ake taƙaddama a kan - na koyar da yara 'yan firamare da harshen uwa, inda yanzu za a koma kamar da - tsarin koyar da 'yan firamaren cikin harshen Ingilishi.

Minista Ilimi na ƙasar Tunji Alausa, ya ce shirin ya gaza cimma manufar da ta sa aka ɓullo da shi , saboda haka an daina amfani da shi nan take.

Ya ce a yanzu za a koma amfani da harshen Ingilishi wajen koyar da yara tun daga makarantun ƙasa da firamare har zuwa jami'a.

Tsohon Ministan Ilimi na ƙasar, Adamu Adamu ne ya ɓullo da tsarin, bisa dalilin cewa yara sun fi fahimtar ilimi sosai ta harshen uwa.

..

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin, tsohon ministan ya kafe cewa yara sun fi gane abin da ake koya musu, idan aka koyar da su ta harshen da suka taso da shi a gida - wanda bincike da nazarce-nazarce da dama na Majalisar Ɗinkin Duniya sun tabbatar da hakan.

Tsarin ilimi na Najeriya na fama da matsaloli da dama, kamar rashin malamai masu inganci, rashin wadatattun kayan koyarwa, rashin wadataccen albashi ga malamai, da yawan yajin aiki.

Duk da cewa kashi 85 cikin ɗari na yara suna zuwa makarantar firmare, to amma ƙasa da rabin wannan kashi ne ke kammala karatun sakandire.

Ƙididdigar Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna cewa yara miliyan 10 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya - wanda hakan ya zarta na duk wata ƙasa a duniya.

Da yake sanar da soke tsarin tare da komawa na da, a babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja, Dr Alausa ya yi nuni da yadda ake samun sakamako maras kyau a yankunan da suke amfani da tsarin na koyarwa da harshen uwa.

Ministan ya bayar da alƙaluma daga sakamakon jarrabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma (WAEC), da na hukumar shirya jarrabawa ta Najeriyar, (Neco), da kuma na jarrabawar shiga jami'a (Jamb).

Soke tsarin kai tsaye da gwamnati ta yi ya janyo ra'ayoyi daban-daban, wasu na suka wasu kuma na yabawa, a tsakanin masana harkar ilimi da masu sharhi da kuma iyaye.

Ra'ayin ƙwararru

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Waɗanda suka yaba wa gwamnati a kan matakin, sun nuna cewa tsarin yana da matsala kuma ya taimaka wajen ƙara faɗuwar darajar ilimi.

Wasu kuma na ganin an yi gaggawar soke shirin, inda suke cewa irin wannan gagarumin sauyi na buƙatar tanadi sosai wajen horar da malamai, da samar da littattafai cikin harshen da sauran kayan koyarwa, da kuma tsawon lokaci ana aiwatar da shi kafin a yanke hukunci a kansa, a kuma fara ganin tasirinsa.

Masanin harkar ilimi Dr Aliyu Tilde, ya yaba da matakin soke tsarin da cewa Najeriya ba ta kai ga ɗaukar irin wannan mataki ba na koyarwa da harshe uwa.

Ya ce: "Shin Najeriya tana da ƙwararrun malaman da za su koyar a gomman harsunan gida da ake da su a ƙasar? Amsar ita ce a'a. Sannan kuma dukkanin manyan jarrabawar da ake yi kamar WAEC, da Jamb, ana yinsu ne a cikin Ingilishi ba a harshen uwa ba.

Tilde ya bayyana hakan ne a hira da BBC, inda ya ƙara bayani da cewa: "Ina ganin abin da ya kamata a yi wajen bunƙasa makarantunmu shi ne a kawo ƙwararrun malamai.''

Banbancin ra'ayi:

Sai dai kuma wani mai sharhi kan al'amarun jama'a, Habu Dauda, yana da saɓanin ra'ayi.

“Ina ganin an soke tsarin cikin gaggawa, maimakon a bayar da isasshen lokaci a ga yadda zai kasance zuwa gaba.

Shekara uku ta yi kaɗan matuƙa a yanke hukunci kan irin wannan babban sauyi - kamata ya yi gwamnati ta ƙara zuba jari a tsarin," kamar yadda ya sheda wa BBC.

..

Asalin hoton, Getty Images

Me iyaye ke faɗi?

Wata uwa da take da 'ya'ya biyu a firamare, Hajara Musa, ta ce ta goyi bayan soke tsarin, domin a cewarta yanzu yara za su koyin Ingilishi tun suna ƙanana.

Ta gaya wa BBC cewa,'' Ingilishi harshe ne na duniya da ake amfani da shi a ko'ina, kuma ina ganin ya fi dacewa yaran nan su fara amfani da harshen tun daga fara karatunsu maimakon su jira har sai sun girma.''

Wannan muhawara na nuni da irin ƙalubalen da ake fama da shi a Najeriya kan yadda za ta iya ciyar da ɗimbin al'adunta gaba da kuma ɓukatar aiwatar da tsari a ƙasa da kuma tsarin tattalin arziƙi na duniya inda ake amfani da harshen Ingilishi yawanci.