Zanga-zanga biyar da ƴan arewacin Najeriya suka yi kan matsalar tsaro

A ranar Talata ne mazauna wasu yankuna a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya suka fita kan tituna domin nuna ɓacin ransu kan hare-haren ƴanbindiga, abin da ya jawo mutuwar wasu daga cikinsu.
Aƙalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Malumfashi yayin zanga-zangar bayan jami'an tsaro sun buɗe wuta, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Zanga-zangar na zuwa ne bayan wani hari ranar Litinin da ya jawo kisa da kuma sace kusan mutum 20 a yankin.
Fusatattun matasan da suka fita zanga-zangar sun toshe babbar hanyar Funtua zuwa Katsina, inda suka dinga nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.
Katsina na ɗaya daga ckin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fuskantar hare-haren 'yanfashin daji masu garkuwa da mutane, da ɗora wa mazauna ƙauyuka harajin kayan gona.
An sha yin irin wannan zanga-zanga a jihohi maƙwabta kamar Zamfara, da Kaduna, da Neja, wadda mazauna yankuna ke kukan neman ɗauki daga hukumomi.
Mun duba wuraren da aka yi irin wannan zanga-zanga kan matsalar tsaro a baya-bayan nan da kuma dalilin da ya sa mutane ke ɗaukar matakin yin ta.
Zanga-zangar mata a Zamfara

Asalin hoton, Mai Biredi TV
Jihar Zamfara na maƙwabtaka da Katsina, kuma ana ganin ayyukan 'yanfashin daji na baya-bayan nan ya faro ne daga can.
A watan Agustan 2025 ɗaruruwan mata tsofaffi da masu shayarwa suka gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga.
Matan waɗanda suka fito daga garin Jimrawa na yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, sun koka kan yadda suka ce ƴanbindiga na ci gaba da addabarsu ta hanyar sace mutane, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a lokacin.
Zanga-zangar matan na zuwa aƙalla mako biyu bayan wasu zanga-zanga biyu da aka gudanar a birnin na Gusau, bayan da masu zanga-zangar suka yi iƙirarin cewa hare-haren ƴanbindigar sun kashe fiye da mutum 100 a ƙauyukan Mada da Ruwan Baure da Fegin Baza da Lilo da kuma Bangi.
Ƙaramar hukumar Kaura Namoda na daga cikin ƙananan hukumomin jihar da hare-haren yanbindiga ke ci gaba da addaba.
Mazauna jihar sun ce rashin hanyoyi masu kyau na kawo wa jami'an tsaro tarnaƙi wajen isa yankunan, lamarin da ke bai wa ƴanbindigar damar cin karensu babu babbaka.
Zanga-zangar #SaveTheNorth

A ranar 10 ga watan Disamban 2021 - wadda ta yi daidai da Ranar 'Yancin Ɗan'adam - gamayyar ƙungiyoyin arewacin Najeriya suka taru a dandalin Unity Fountain da ke Abuja domin kokawa kan matsalar tsaron.
Masu zanga-zangar sun yi amfani da maudu'ai iri-iri kamar #SaveTheNorth, #NorthernLivesMatter, #EnoughIsEnough, domin jan hankalin duniya kan kashe-kashen da 'yanfashin daji da masu iƙirarin jihadi ke yi a jihohin arewacin ƙasar.
Jami'an tsaro sun yi yunƙurin tarwatsa su da farko, amma daga baya aka ƙyale su suka shiga cikin dandalin kuma aka hana su fita daga cikinsa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar, Zainab Ahmed, ta ce sun fita ne domin abin ya ishe su.
"Mun zo ne mu faɗa wa gwamnatin Najeriya cewa Arewa na zubar da jini kuma abubuwan sun ishe mu haka. Mun gaji da binne mata da maza da yara saboda kashe-kashen 'yanfashi."
Mazauna Malumfashi
Garuruwan da ke cikin ƙaramar hukumar Malumfashi mai maƙwabtaka da jihar Kano sun daɗe suna kokawa game da hare-haren 'yanbindiga.
Wannan ta sa a watan Yulin 2024 suka fusata kuma suka tare manyan hanyoyin Katsina zuwa Funtua, da Malumfashi zuwa Kano, da Marabar Kankara zuwa Katsina domin nuna ɓacin ransu.
"Yanzu haka akwai ɓarayi kusan 300 a garin Bindigau da Dan Kartau, wallahi yanzu haka ɓarayin suna can. Yanzu akwai gawar fiye da mutum 12 da muka kasa ɗkkowa saboda su," kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa.
"Sun gallabe mu, ko noma sun hana mu yi. Abin da muke nema shi ne gwamnati ta ta taimake mu," in ji wani mutumin.
Zanga-zanga a Musawa da Matazu
A watan Agustan 2023 ma al'ummomi a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu na jihar Katsina sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a yankunansu.
Mutanen yankunan ɗauke da kwalaye sun yi ta rera waƙoƙin kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki.
Mutanen yankin sun koka musamman kan yadda 'yan bindiga ke ci gaba da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun addabe su ba dare ba dare, inda suke sace mutane da dukiyoyinsu.
A wannan karon har da mata a cikin mutanen da suka halarci zanga-zangar ta lumana.
Zanga-zangar Gonin Gora
Yankin Gonin Gora na ɗaya daga cikin unguwannin da ke yawan yin zanga-zangar da kan kai ga toshe hanyoyi saboda nuna ɓacin rai game da hare-haren 'yanbindiga.
Ɗaya daga cikin irin wannan zanga-zangar ta faru ranar 20 ga watan Yunin 2021, inda suka toshe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Babban abin da ke jan hankali game da zanga-zanga a Gonin Gora shi ne datse ɗaya daga cikin manyan hanyoyi mafiya yawan zirga-zirgar ababen hawa a Najeriya, kasancewarta ta hada manyan biranen ƙasar biyu.
Masu zanga-zangar sun ce sun ɗauki matakin ne bayan mahara sun kashe mutum ɗaya a garin nasu tare da sace wasu 21 kwana ɗaya kafin haka a Kakau da Gonin Gora.
Su ma mazauna yankin Unguwar Magaji sun rufe hanyar a daidai yankinsu, wadda ke da yawan matafiya.
'Dalilin da ya sa muke yin zanga-zanga'
A mafi yawan lokaci masu zanga-zangar kan ce suna yi ne domin jawo hankalin gwamnati ta kawo musu ɗauki.
Sai dai akan soki matasan da cewa suna tauye haƙƙin matafiya duk lokacin da suka toshe hanya.
"Muna roƙon matafiyan su ma su ba mu haɗin kai saboda su ma ba tafiyar kwanciyar hankali suke yi ba," a cewar wani mai zanga-zanga a garin Malumfashi.
"Mun rasa yadda za a yi abin ya kai ga hukumomi, idan ba haka [toshe hanya] muka yi ba zai kai gare su ba."










