Abin da ya sa yara ke ganin lokaci ba ya sauri kamar manya

Asalin hoton, Edouard Taufenbach and Bastien Pourtout
- Marubuci, Krupa Padhy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC FUTURE
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana tafka wata gagarumar mahawar a gidana kan yaushe ne lokaci yake sauri ko kuma tafiya a hankali.
''Yana tafiya a hankali a cikin mota!'' in ji ɗana
''Ko kaɗan!'' in ji ɗiyata. "Ina abubuwa dayawa kuma bana ganin cewa lokaci na tafiya da hankali, amma watakila a ƙarshen mako idan muna kan kujera muna kallon fina-finai."
Akwai kuma ƴar yarjejeniya tsakaninisu; Dukansu sun yarda cewa kwanaki bayan Kirsimati da ranar zagayowar haifuwarsu suna cikin waɗanbda ke tafiya a hankali idan suka yi la'akari da cewa sai sun jira kwanaki 365 kafin su sake yin waɗannan bukukuwan. Suna ganin shekara na dadewa kafin ta zagayo a shekarunsu.
Lamari ne da zan iya tunawa ni kai na; hutun bazara da ke tattare da wasan ruwa, da tsalle-tsalle a kan ciyawan da ba a dɗe da yankewa ba, ga kayan wanki an shanya a waje yayin da rana ke haskakawa. A irin wannan yanayin, ina ji kamar lokaci na tafiya a hankali.
Teresa McCormack, farfesa a fannin ilimin halayyar ɗanadam a Jami'ar Queensda ke birinin Belfast a Ireland ta arewa, ta yi imanin cewa mu'amular yara da lokaci batu ne da ba a yi nazari sosai a kansa ba. Ta daɗe tana gudnar da bincike kan ko akwai wani abu na daban game yadda yara ke ganin wucewar lokaci, kamar yadda suke lissafin agogonsu ya fita daban da na manya. Amma har yanzu akwai ƙarin tambayoyi fiye da amsoshi kan wannan batun.
"Abin mamaki ne cewa har yanzu ba mu san ainihin amsoshin tambayoyi kamar yaushe ne yara suke da bambancewa tsakanin abin da ya gabata da kuma abin da bai riga ya faru ba, ganin cewa hakan ya tsara duk irin tunanin da muke yi game da rayuwarmu a matsayin manya," in ji McCormack. Ta bayyana cewa duk da cewa ba mu da cikakkiyar fahimta game da lokacin da yara suka fahimci yadda lokaci ke tafiya, mun san cewa tun daga lokacin da suka fara tasowa, yara suna fara gane abubuwan yau da kullun kamar lokutan cin abinci da lokacin kwanciya barci. Ta nanata cewa wannan ba ɗaya ba ne da gane cikakken ma'anar yadda lokaci ke gudana ba.
Manya suna bambanta abubuwan da suke faru a lokuta daban-daban kai tsaye, saboda ilimin da suke da shi na agogo da tsarin kwanar wata. Harshe ma yakan taka rawa a wannan lamarin. "Yana ɗaukar lokaci kafin yara su zama ƙwararrun masu amfani da harshe da ya jiɓanci lokaci, kalmomi kamar 'kafin', da 'bayan', da 'gobe' da 'jiya'," in ji McCormack.
McCormack ta ƙara da cewa fahimtar mu na yadda lokaci ke tafiya yakan dangata ne da lokutan da ak fara buƙatar nu yanke hukunci a kan abubuwan da suka shafi lokaci. "Shin kuna yin tambayar ne yayin da abubuwan ke faruwa ko kuma a bayan sun faru?" Ta ba da misali da mutane da yawa za su iya fahimta. "Tun daga lokacin da aka haifi yarana zuwa lokacin da suka bar gida yanzu kamar ana kiftawar ido ne. Amma a lokacin da kake cikin renon yaran, rana guda ma ba ta wucewa da sauri.''

Asalin hoton, Edouard Taufenbach and Bastien Pourtout
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bincike ya gano cewa kowane ɗanadam yana fara la'akari da tsawon lokaci da kuma saurin tafiyar lokacin ne a nasa matakin da ya bambanta da na kowa. Yara ƙanana da ba su kai shekaru shida ba suna ganin suna iya fahimtar yadda darasi ke wucewa a cikin aji, alal misali, amma akan dangata hakan da yanayin tunaninsu ne fiye da ainihin yadda lokacin ya ke. Waɗannan abubuwa guda biyu suna cin karo da juna ne a wani mataki na gaba lokacin da yara suka fahimci haɗin tsakanin gudu da kuma tsawon lokaci.
McCormack ta kawo ƙarin abubuwa biyu a da suke taka rawa a yadda yara ke ganin lokaci. "Ɗaya shi ne tsarin tunaninsu ba iri ɗaya da na manya ba ne," in ji ta. "Za su iya zama masu rashin haƙuri kuma jira na masu wahala," in ji ta. "Hakanan yana iya kasancewa da alaƙa da yanayin kulawar su. Duk lokacin da ka ke kula da wani abu ko kuma sa ido a kan lokaci sai ka ga baya tafiya da sauri, duk lokacin da ka ke sa ran abu ya zo da wuri sai ka ga yana tafiya a hankali.''
An ga babban misali na wannan lamari a lokacin kullen Korona, inda masu bincike suka gano cewa mutane sun ga raguwar saurin tafiyar lokaci da ke da alaƙa da ƙarin damuwa, da samun ƙarancin abubuwan yi.
Hakanan yana yiwuwa a iya kwatanta wannan lamari ta hanyar kallon fim - fina-finai masu ban tsoro na iya sa lokaci ya yi kamar yana tafiya a hankali, alal misali, kamar kallon hotunan da ke ba mu haushi. Wani bincike ya nuna cewa abubuwan da ba su da daɗi, kamar tafiya a cikin jirgin ƙasa mai cunkoso, shi ma ana jin kamar yana ɗaukar tsawon lokaci fiye da asalin nisar tafiyar.
Har ila yau, akwai wani lamari na tabarbarewar gaɓoɓin jiki yayin da muke ƙara tsufa wanda kuma zai iya shafar yadda mu ke yanke hukunci kan yadda lokaci ke tafiya, a cewar Adrian Bejan, farfesa a fannin injiniya a Jami'ar Duke da ke birnin Durham, a Jihar North Carolina. Ya yi ƙoƙari ya bayyana maƙasudin fahimtarmu game da lokaci ta hanyar wani bincike da aka ƙirƙiro a 1996 kan "Physics of Life" wanda aka sani da "construction law".
Wannan, in ji shi, yana nufin yadda mu ke sarrafa abubuwan da mu ke gani da idannun mu da kuma mu ke mu'amalla da su da sauran gaɓoɓin jikin mu yana raguwa a yayin da mu ke ƙara girma kuma shekaru suka fara cim mana.
Wannan yana haifar lamarin d za mu ji kamar cewa lokaci yana tafiya a hankali a tunanin mu yayin da mu ke karɓar sakonni a dunƙule ba kamar yadda ya ke lokacin d mu ke yara ba.

Asalin hoton, Edouard Taufenbach and Bastien Pourtout
Akwai kuma wani abu da ke faruwa ga yawancin mu yayin da muke ƙara tsufa - rashin sauyi a yadda mu ke gudanar da al'amurn mu na yau da kullum na matuƙar tasirin kan yadda mu ke ganin lokaci na tafiya. Bincike ya gano cewa ƙarin matsi domin gudanar da al'amura kan lokaci, da gajiya da al'amuran yau da kullun a cikin rayuwar mutum, da kuma yadda mutum ya kasance mai tunanin abubuwan da za su faru nan gaba, saɓanin rayuwa a yanayin sha yanzu magani yanzu, sai a ga kamar lokaci na tafiya da sauri.
Abin da kuke yi a halin yanzu na da tasiri kan yadda ku ke kallon tafiyar lokaci, kuma hakan bai da alaƙa da shekarun da mu ke da su.
A lokacin da mu ke gudanar da ayyuka da ke buƙatar mu yi tunani sosai sai a ga cewa lokaci na tafiya da sauri domin a lokacin akwai abubuwa dayawa da za su ɗauke wa mutum hankali.










