'Matar da aka yi wa ƙarin jini sau 36 sanadiyar ɗaukar ciki'

Ma'auratan suna farin cikin ganin ƴarsu ba ta gaji cutar borin jini ta thalassemia

Asalin hoton, Pavan Jaishwal

Bayanan hoto, Ma'auratan suna farin cikin ganin ƴarsu ba ta gaji cutar borin jini ta thalassemia
    • Marubuci, Lakshmi Patel
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Gujarati
  • Lokacin karatu: Minti 3

''Ina ganin fuskar ƴata sai na manta da duk wata wahalar da na sha a sanadiyar ɗaukar ciki da naƙudar," in ji Kinjal Lathi, daga yankin Ahmedabad, inda ta ƙara da cewa, "ni da mijina mun sha kuka."

Da farko Kinjal ta fara cire rai daga samun haihuwa da jin daɗin zama iyaye saboda cutar borin jini ta thalassemia da take fama da ita.

Dole a riƙa mata ƙarin jini duk bayan mako biyu, sannan dole ta bi wasu ƙa'idojin cin abinci da magunguna.

Bayan kuma cutar da take fama da ita, akwai kuma ƙalubalen ɗaukar ciki da take fama da shi.

"Akwai barazana babba ga uwa da abin da ke cikinta. Amma na yanke shawarar cika burina na zama uwa," in ji Kinjal.

Sai dai aka yi wa Kinjal ƙarin jini guda 36 lokacin da take da ciki, amma kuma ta haifa jaririya lafiyayyiya a 12 ga watan Yulin 2019.

Ko bayan haihuwar ma, sai da aka cigaba da yi wa Kinjal mai shekara 25 ƙarin jini, inda ta ce wasu lokutan ma ana mata ƙarin jinin ne, tana kuma shayar da jaririyarta.

Sannan kuma wani abun farin cikin shi ne ƴarta ba ta gaji cutar ba.

Wata ƙwayar halitta ce take samun matsala, wanda ke hana cuɗanyar jini da iska domin samar da jinin da ake kira haemoglobin wanda shi ne ke zagayawa da jini mai ɗauke da sinadarin protein a jiki.

An cigaba da yi wa Kinjal ƙarin jini a asibiti bayan ta haihu

Asalin hoton, Pavan Jaishwal

Bayanan hoto, An cigaba da yi wa Kinjal ƙarin jini a asibiti bayan ta haihu

Yaya cutar thalassemia ke taɓa juna-biyu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba a cika samun irin yadda masu cutar nan, irin Kinjal suke haihuwa lafiya ba, kamar yadda likitan yara, Anil Khatri wanda yake cikin kwamitin kar ta kwana na yaƙi da cutar ya bayyana.

Ya ce bai taɓa ganin haka ba sama da shekara 30 da ya yi yana aikin kula da masu cutar ba, inda ya yi jinyar sama da masu cutar guda 100.

Akwai masu cutar kusan guda miliyan 270 a duniya, kamar yadda ma'aikatar lafiya da walwalar iyali ta bayyana.

Akwai na'ukan cutar da dama, ciki har da wadda ake kira Hemoglobin H disease. Ita ma ta kasu kashi biyu wato nau'in alpha da beta - nau'in beta (TM) ce ta fi illa.

A Indiya akwai yara tsakanin 100,000 zuwa 150,000 da suke ɗauke da cutar.

Ɗaukar ciki ce abu mafi wahala ga mata masu cutar, kamar yadda likitan haihuwa, Umar Khatri, wanda ya yi wa Kinjal jinya.

Idan mace na da juna biyu, jininta yana ƙaruwa, wanda hakan ya sa jikin ke buƙatar ƙarin sinadarin iron domin tallafa wa aiki da yaɗuwar oxygen zuwa ga jaririn.

"A ƙa'ida muna kiran mata masu juna biyu ne su zo dubiya aƙalla sau ɗaya a wata. Amma ita Kinjal tana zuwa ne duk kwana 15, wanda shi ne karo na farko da muke haka," in ji Khatri.

Me ya sa wasu ma'aurata suke zuwa neman shawara kan ƙwayoyin halitta?

Ganin irin halin da Kinjal take ciki ya sa dole mijinta, Naveen Lathia ya shiga damuwa.

Ya ce "ya shiga fargabar rasa matarsa Kinjal." Amma da ta dage tana son haihuwa, duk da barazanar da ke ciki, sai ya fara bincike kan cutar.

Amma bayan binciken da ya yi, sai ya zama bai gano wata mata da ta haifa lafiyayyen jariri ba.

Bayan ta haihu, sai likitoci suka ba Kinjal shawarar ta riƙa cin abincin da aka dafa a gida, kuma ta nisanci wuraren cunkosun mutane, domin a cewar Dr Khatri, masu nau'in cutar ta TM suna kamuwa da cuta cikin sauri.

Yanzu zuwa neman shawara kan ƙwayoyin halitta ya fara zama ruwan dare a tsakanin ma'aurata a India.

Dr Anil Khatri ya shawarci ma'aurata a India cewa kafin su yi aure, su yi gwajin ƙwayoyin halitta, "idan dukkansu suna da cutar thalassemia, bai kamata su yi aure ba."