Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane gurbi Eze zai buga a Arsenal?
Sayen Eberechi Eze ya canza tunanin magoya bayan Arsenal baki ɗaya.
Gunners ta yi namijin ƙoƙari a wannan lokacin a kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo, inda ta saya ƴan'wasa shida kan fam miliyan 190 tun kan fara kakar tamaula ta bana.
Daga cikin ƴan'wasan har da Viktor Gyokeres kan fam miliyan 64 da Martin Zubimendi kan fam miliyan 60, sai dai sayen Eze da ta yi, wanda hakan ya sa magoya baya na ganin ita ce kan gaba a cefane mai amfani.
Wani babban al'amari shi ne yadda Arsenmal ta sha gaban abokiyar hamayyarta Tottenham Hotspur, wadda tun farko ta ƙulla yarjejeniyar shiga ciniki da Crystal Palace da Eze sa'o'i kafin Gunners ta shiga zawarcin ɗan wasan.
Ta yaya Arsenal ta yi nasarar sayen Eze?
Lamarin ya faru ne tsakanin ƴan sa'o'i, inda tun da sanyin safiyar Laraba alamun suka nuna cewa mai shekara 27 ya kusn kammala komawa Tottenham da taka leda.
To sai dai ba a kai ga kammala cinikin ba, kuma dalilin shi ne wasan da Palace za ta kara na cike gurbin shiga Europa Conference Legue da Fredrikstad ranar Alhamis, hakan ya kawo tsaiko ga Tottenham.
Ita dai ƙungiyar Selhurst Park ta so Eze ya buga mata karawar saboda mahimmancinsa a kakar, kuma ba sa buƙatar rabuwa da shi ba tare da maye gurbinsa ba.
Kociyan Palace, Oliver Glasner a lokacin da ya gana da ƴan jarida ya ce Eze da Marc Guehi, waɗanda ake akakantawa da za su bar mu ''sun mayar da hankalinsu kan ci gaban ƙungiyar''.
Ko an kawo Eze ya maye gurbin Kai Havertz?
Arsenal ta yi atisaye a filinta ba tare da Kai Havertz ba, Daga baya aka sanar cewar ɗan kasar Jamus ya ji rauni a gwiwa, kenan zai sha jinya.
Duk da cewar ba a tantance kwanakin da zai yi jinya ba, Arsenal ta kwan da sanin abin da ya kamata ta yi?
Sa'o'i tsakanin a yammacin Laraba, Arsenal ta fara zawarcin Eze, wanda a baya ta daɗe tana saon ɗauka.
Daman Eze yana ƙaunar Arsenal a zuciyarsa, wadda ya fara daga makarantar horon tamaula ta ƙungiyar, saboda haka hukunci ne mai sauki da ɗan wasan ya ɗauka.
Daga can yammaci labari ya karaɗe ko'ina, yayin da ake cewa Tottenham ba ta da wani zaɓi na canja matsayin da ɗan ƙwallon ya ɗauka, saboda yadda yake ƙaunar Gunners.
Hakan dai ya sa Eze ya ƙi amincewa ya koma Tottenham - hakan ya ƙara masa martaba da ƙima a idon magoya bayan Arsenal.
Wata tambayar ita ce me ya sa Arsenal sai daga ƙarshe-ƙarshe ta saya Eze?
Arsenal tana kallon Eze a matakin mai buga lamba 10 a kuma lokacin Ethan Nwaneri ya tsawaita kwantiran ci gaba da taka leda a Emikraters kaka da yawa, hakan ya sa ta yi ta taka tsantsa kan gurbin da zai buga mata ko da ta mallake shi.
To sai dai raunin da Havertz ya ji ne ya sa Arsenal ta yanke hukuncin tana da buƙatar sayen Eze a kakar nan.
Eze bai buga wa Palace karawar cike gurbin shiga Europa Confrence League, inda Glasner ya ce Eze ba shi da ƙoshin lafiya.
Ranar Asabar da Arsenal za ta karɓi baƙuncin Leeds United a mako na biyu a Premier League, an sanar da Gunners ta kammala sayen Eze har ma aka gabatar da shi gaban magoya baya a Emirates.
Gurbin da zai buga
Babba tambaya ga kociyan Arsenal, Mikel Arteta ita ce - a wani gurbin Eze zai ke buga wa Gunners tamaula.
Eze ɗaya ne daga kaɗan ɗin ƴan'wasa da za ka iya kwatanta shi da mai taka leda da ban da salon wasu ƴan ƙwallon.
Kuma hakan ne ya sa sayen ɗan'ƙwallon da Arsenal ta yi yake da manufa.
Arsenal ta ci karo da koma-baya a salon wasan da take bugawa, hakan ya sa yanzu ta canja tsari a kakar nan ta yadda take saurin raba ƙwallo kuma da sauri yadda za ta riƙa kai hare-hare ga abokiyar hamayya ba ƙaƙƙautawa.
Eze da ban yake da sauran ƴan'wasan Arsenal da ke buga mata gurbin gaba, saboda haka tana zaɓi da yawa a koda yaushe.
Ko da yake yana da wahala a canja gurbin ƙyaftin Martin Odegaard a matakin lamba 10.
To sai dai sayen Eze da ta yi a bana, zai bai wa Arsenal dama da yawa da take buƙata, wadda ke fatan lashe babban kofi a ƙarshen kakar nan.
Gurbin gaba daga gefen hagu, shi ne ake ganin Arsenal tana da bukatar ɗan'ƙwallo, wajen da Gabriel Martinelli ke bugawa ke nan, wanda ke fama da yawan rauni da jinya.
Wakilin BBC, Umar Irfan ya ce ''Eze zai riƙa buga gurbin gaba daga gefen hagu sosai a bana."
Haka kuma Eze zai iya tafiya ta tsakiyar fili da zarar mai tsare baya daga gefen hagu zai ke jan ƙwallo zuwa gaba a lokacin wasanni.
Eze yadda ya ƙware a raba ƙwallo a lokacin ba-ni-in-ba-ka a cikin runtsi ya sa ya zama abin zaɓi ga Arsenal idan wannan salon ta zaɓa za ta buga.''
''Yadda Eze ya gwanace a iya jan kwallo da gudu da bayar da fasin mai amfani, hakan zai taimaka wa Gyokeres cin ƙwallaye cikin ruwan sanyi.
''Idan Arsenal ta zaɓi salon kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa, ke nan tana buƙatar Odegaard da Eze daga cikin masu taka leda daga tsakiya.
Sannan Eze zai iya buga tsakiya daga barin hagu a salon Gurners na 4-4-2, yana yawan sauka ya tare ƙwallo kamar yadda yawanci Palace take amfani da shi a gurbin.
Yaya maghoya baya suka ji da sayen Eze?
A wata hira da aka yi da shi a BBC a cikin watan Mayu, Eze ya ce dalilin salon taka ledarsa, saboda masu kallonsa, kuma yana ƙaunar yake saka su farinciki.
Wannan shi ne sakon da duk wani mai goyon baya yake son ji.
Eze ya yi kaurin suna a Palace. Ya ci ƙwallo 40 ya kuma bayar da 28 aka zura a raga a wasa 169 a ƙungiyar.
Daga ciki da ba za a manta ba har da ƙwallon da ya ci Manchester City da suka lashe FA Cup a cikin weatan Mayu.
Wannan alama ce da ake ƙaunar ɗan wasan wanda ya taaaka rwar gani a ƙungiyar Selhurst Park, kuma da ƙyar ka samu ɗan wasan ko magoyin baya da ya ji haushin zaɓin Eze, saboda rawar da ya taka da abin da ya yi a Palace.
Tuni magoya bayan Arsenal ke ƙaunarsa, saboda ya zaɓi ya taka leda a Gunner, wadda yake ƙauna tun yana matashi maimakon abokiyar hamayya Tottenham
Lokacin da Eze ke murnar lashe FA Cup a kafar sada zumuntarsa a Instagram, bayan cin kofin, ya saka hoton Ian Wright wanda ya buga wa Palace FA Cup.
Eze yana da rigar Palace iri daya da ta Wright kuma yanzu zai bi sahun tsogon gwarzon wanda ya zama babban masoyi a Arsenal - kuma zai yi fatan ya samu wannan matsayi na kashin kansa.