Yadda tsutsa ke shiga cikin ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
Tsutsosin cikin ɗan'adam suna janyo matsala matuƙa.
Suna iya shiga jiki ta hanyar shan ruwa ko cin abincin da ya gurɓace, da kuma wasu abubuwa da ke janyo su.
Alamomin sun haɗa da ganin dogayen tsutsotsi a bahaya, da ciwon ciki da kuma ƙaiƙayin dubura.
Ana iya zuwa gwaji bayan ganin waɗannan alamomi.
Suna kuma da rukuni daban-daban da gurbin da suke zama a cikin ɗan adam.
Kowanne daban yake da ɗan'uwansa.
Yadda suke shafar lafiyarmu ma ya bambanta.
Wasu daga cikin tsutsosin na shiga ta hanyar ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya ake yaɗa tsutsar ciki?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana iya kamuwa da cutar tsutsar ciki ne ta hanyar taɓa abubuwa da ke ɗauke da datti ko ma rashin wanke hannu yadda ya kamata.
Haka kuma ana iya kamuwa da cutar ta hanyar cin abinci ko shan ruwan da ya gurɓata.
Yin ba-haya a waje na iya janyo cutar saboda idan bahayar ta buce, za ta iya shiga cikin ƙasa, inda mutane kan cire amfanin gona ba tare da sun sani ba wanda kuma zai gurbata abincin.
Za a iya yaɗa ta a muhallan da ba su da tsafta da kuma banɗaki. Har ila yau ana iya kamuwa da cutar ta hanyar cin nama da kuma kwan da ba a dafa ba da ke ɗauke da tsutsosin.
Yara da dama na kamuwa da cutar tsutsar ciki. Hakan yana faruwa bayan da tsutsosin suka shiga cikin jiki tare da hayayyafa. Suna janyo ƙaiƙayi a dubura da sauransu.
Waɗannan ƙwayayen da tsutsosin ke yi na yaɗuwa zuwa jikin tufafi, kayan girki, wuraren kwanciya, abinci da kuma banɗaki.
Suna shiga jiki ta hanyar taɓa waɗannan abubuwa da kuma sanya hannun da ya taɓa su cikin baki. Wasu ƙwayayen kan shafe makonni biyu a ciki.
Don haka, ya kamata yara su riƙa wanke hannayensu akai-akai.
Abin da za ku yi don kauce wa tsutsar ciki
- A riƙa wanke hannu kodayaushe da kuma yanke farce.
- A riƙa wanke hannu kafin cin abinci, bayan shiga banɗaki da kuma bayan canzawa yara tufafi.
- A koyawa yara yadda za su wanke hannayensu akai-akai da kuma wanka kowace rana.
- A wanke abin goge baki kafin da kuma bayan gobe baki.
- A dinga wanke towel da zanin gado da ruwa mai zafi.
- A riƙa tsaftace ɗakin girki da kuma banɗakuna.
- A riƙa shan tsaftaccen ruwa.
- A wanke ganyayyaki da kuma kayan lambu sosai kafin a ci.
- Kada a bar yara su riƙa a wasa kusa da ba-hayar karnuka da kuma maguna.
- Mutane su guji tafiya babu takalmi a wurare mara tsafta.
Illolin tsutsar ciki
Akwai alamomi da dama waɗannan idan mutum ya ji su zai gane cewa yana fama da cutar tsutsar ciki da suka haɗa da:
- Ciwon ciki
- Tashin zuciya
- Yawan amai
- Gudawa tare da jini
- Yawan shiga bayi da fitar baya
- Kasala da rashin kuzari










