Abubuwan da suka kamata ku sani kan marigayi Hulk Hogan

Hoton Hogan kenan lokacin da yake taya Donald Trump yaƙin neman zaɓe a watan Oktoban 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton Hogan kenan lokacin da yake taya Donald Trump yaƙin neman zaɓe a watan Oktoban 2024
    • Marubuci, Steven McIntosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Entertainment reporter
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hulk Hogan, ɗaya daga cikin mafiya shahara a wasan kokawa na rislin, ya mutu yana da shekara 71.

Tauraron wasan da aka haifa da sunanTerry Gene Bollea, ya shahara da farin gashi a kansa da kuma gashin baki, kuma ya rasu ne a gidansa da ke jihar Florida ranar Alhamis.

Hogan ya fara sana'arsa ta kokawa a 1977, amma ya gawurta ne bayan ya saka hannu kan kwantaragi tare da kamfanin shirya wasannin dambe na World Wrestling Federation (WWF) - kafin ya sauya suna zuwa World Wrestling Entertainment (WWE) a 1983.

Daga baya ya sake shahara da shirin talabijin mai suna Hogan Knows Best, wanda aka yaɗa daga 2005 zuwa 2007.

Mai kula da harkokin Hogan Chris Volo ya ce ɗan kokawar ya kamu da bugun zuciya ne a gidan nasa kuma ya rasu a gaban iyalinsa.

Hogan ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump kamfe sosai a zaɓen 2024.

Shugaban ya ce "na yi rashin babban aboki" a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

An yi masa tiyata a wuyansa a watan Mayu, sannan aka yi masa wata tiyatar a zuciya a watan Yuni.

Iyalinsa sun faɗa cikin wani saƙo a shafukan zumunta: "Muna fatan samun sassauci a cikin abubuwan da ya bari masu daɗin ji da gani ga miliyoyin masoya na tsawon shekara 40."

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyon Hulk Hogan yayin kamfe na siyasa

"Ɗaya daga cikin masu nishaɗantarwa mafiya shahara, Hogan ya taimaka wa WWE samun farin jini a shekarun 1980.

"WWE na miƙa ta'aziyyarsa ga iyalin Hogan, da abokansa, da masoyansa."

Ya lashe kambin gwarzon WWE, kuma ya zama fuskar WrestleMania, shirin WWE mafi girma, har karo takwas.

An saka shi cikin rukunin 'yan WWE mafiya daraja a 2005. Daga cikin manyan 'yan'adawarsa akwai Dwayne 'The Rock' Johnson, da 'Macho Man' Randy Savage, da Andre The Giant.

Tauraron rislin Ric Flair ya ce "ya kaɗu matuƙa" da jin labarin mutuwar Hogan.

Shi ma wani abokin gwagwarmayarsa the Undertaker ya bayyana alhini: "Duniyar rislin ta yi rashin gwarzo. Gudummawar da ya bayar ba za ta lissafu ba kuma na gode masa kan hakan."

Hulk Hogan kenan yake riƙe da Tony Atlas a filin kokawa a shekarar 1981

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hulk Hogan kenan yake riƙe da Tony Atlas a filin kokawa a shekarar 1981
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haife shi a jihar Georgia ta Amurka a 1953, inda ya taso har ya zama ɗaya daga cikin mafiya shahara a masana'antar kokawa ta rislin.

Laƙabin "Hulk" da ake yi masa ya samo asali ne daga wani tauraron ɗanwasan talabijin da ake nunawa a lokacin, shi kuma "hogan" Vince McMahon ne, wani mai tallata hajarsa, ya laƙaba masa.

Ya fara shiga kokawar WWF a 1979, amma sai a tsakiyar 1980 ya shahara sosai tare da Andre Giant da 'Rowdy' Roddy Piper.

Ya fara zama fuskar shirin WrestleMania a New York a 1985, inda shi da Mista T suka doke Piper da Paul Ordorff.

Farin jininsa na "Hulkamania" ya jawo shirya finafinai kamar Rocky III, da No Holds Barred, da Suburban Commando, da Mr Nanny, da Santa With Muscles, da wani yanki na fim ɗin Baywatch a 1996.

Shi ma Hogan ya fito a finafinai kamar A-Team, Gremlins 2: The New Batch, da Spy Hard, da Muppets From Space.

A 1985, Hogan ya zama tauraron fim ɗin cartoon nasa na kansa da aka nuna a CBS mai suna Hulk Hogan's Rock 'n' Wrestling.

WrestleMania champion John Cena and Hulk Hogan during 2005 Teen Choice Awards - Show at Gibson Amphitheatre in Universal City, California, United States.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hogan kenan tare da John Cena yayin bikin ba da kyautar Teen Choice Awards a 2005
Hogan ya shahara da farin gashinsa da kuma gashin bakinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hogan ya shahara da farin gashinsa da kuma gashin bakinsa

An taɓa yi wa Hogan ihu a wasansa na baya-bayan nan a watan Janairu.

Ya sha fama da rashin lafiya, akasari waɗanda suka same shi a lokacin da yake yin kokawa.

"An yi min tiyata kusan 25 cikin shekara 10 da suka wuce," in ji shi cikin wata hira da Logan Paul a dandalin YouTube.

"Tiayata 10 a gadon baya, da gwiwoyina, da ƙunƙuru, da kafaɗu duka sai da aka sauya min su - kusan komai da komai."

Hoga ya yi aure sau uku, inda ya haifi 'ya'ya biyu da matarsa ta farko Linda.