Imane Khelif: Mace ƴar dambe da ake ‘tababar ko namiji ne’

Lokacin karatu: Minti 8

Sean Kearns

BBC Sport

Imane Kheli

Asalin hoton, Getty Images

An bar 'yan wasan damben boksin na Aljeriya da Japan - Imane Khelif da Lin Yu-ting su shiga gasar Olympic ta Paris duk da cewa an zartar da cewa ba su cancanci shiga gasar wasannin duniya da aka yi ta bara saboda gwajin jinsinsu da aka yi a lokacin ya nuna ba su cancanta ba.

Khelif, 25, ta kai wasan dab da na kusa da karshe na boksin na mata ajin nauyin kilogram 66 bayan ta doke Angela Carini, ta Italiya, yayin da Lin ta kai matakin na wasan dab da na kusa da karshe na mata ajin nauyin kilogram 57 bayan da ta yi nasara a kan Sitora Turdibekova, ta Uzbekistan.

Shigarsu gasar ta Paris ta janyo ce-ce-ku-ce saboda abin da ya faru a 2023 da aka zartar da cewa ba su cancanci shiga gasar ta wasannin duniya ba.

Carini, ta dakata da dambe da Khelif, bayan dakika 46, lamarin da ya sa ake ta sukar kwamitin wasannin Olympic na duniya, saboda barin 'yar damben boksin wadda a bay aka haramta mata shiga wasa saboda yanayin jinsinta.

Carini 'yar Italiya ta ce ta dakata da damben ne domin ta ceci rayuwarta, amma kuma ta nemi gafara daga abokiyar karawa tata ta Aljeriya ranar Juma'a.

Da take magana bayan nasararta, Khelif, ta ce ta je gasar ne domin cin lambar zinariya sabod haka za ta kara da kowa.

Hukumar damben boksin ta duniya (IBA), wadda a baya ita take shirya wasannin boksin a gasar Olympic ta yi suka a kan barin 'yan damben biyu wadanda ake ganin mata-maza ne.

A nan BBC za ta kawo muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da ake magana a kan wannan takaddama.

Mene ne jinsin Khelif a hukumance a lokacin haihuwa? Mace ce ko namiji a halittarta?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A kodayaushe Khelif na shiga gasa ne ta mata kuma hukumar wasannin Olympic ta duniya ta dauke ta a matsayin mace.

An yi rijistar 'yar damben boksin din ta Aljeriya a lokacin haihuwa a matsayin mace , kuma duk tsawon rayuwarta a matsayin mace take, kuma a matsayin mace take damben boksin kuma fasfo dinta ma na mata ne, in ji kakakin hukumar wasannin Olympic ta duniya Mark Adams.

Ya ce: "Wannan ba batu ne mutumin da ya sauya jinsinsa ba, akwai rudanin da ake yi cewa namiji ne yake dambe da mace, lamain ba haka yake ba. A kan wannan batu akwai ittifaki da kuma kimiyyar da ta tabbatar da cewa ba namiji ba ne yake fada da mace."

Khelif ta yi magana a kan yadda ta taso a matsayin mace a Aljeriya, da kuma irin tsangwamar da ta yi fama da ita tana wasan kwallon kafa da maza.

"Kada ka bari wani abu ya hana ka cimma burinka. Burina shi ne in ci lambar zinariya,'' in ji ta, a kalaman da ta yi a watan Maris na 2024.

Ta kara da cewa, "Idan na yi nasara , uwaye da ubanni za su iya alfahari da irin nasarar da 'ya'yansu za su iya samu a rayuwa. Ina son na karfafa wa musamman mata da yara wadanda suke baya a dangi a Aljeriya gwiwa.

Babu wani lokaci ko yanayi da aka taba daukar Khelif ko gabatar da ita a matsayin wani abu da ba mace ba.

Imane Khelif on the left and Angela Carini during their match

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Imane Khelif (hagu) ta doke Angela Carini a gasar Olympics da ake yi a Faransa

Yaya sana'arta ta damben boksin take zuwa yau?

Khelif, mai shekara 25, zuwa yau ta yi shekara takwas tana sana'ar boksin.

'Yar Aljeriyar ta fara fitowa ne a duniya a wasan da ba na kwararru ba tana shekara 19 a gasar damben boksin ta duniya ta mata ta 2018, inda a lokacin ta zama ta 17.

Shekara daya bayan nan, Khelif ta zama ta 19 agasar matan ta 2019.

Ta yi fitarta ta farko a gasar Olympic a gasar 2020 ta Tokyo. An doke Khelif a damben ajin mata masu nauyin kilogram 60, a wasan dab da na kusa da karshe, inda 'yar wasan Ireland wadda ita ce ta ci lambar zinariya, ta doke ta da ci 5-0.

Daga nan kuma ta zama 'yar damben boksin ta Aljeriya ta farko -cikin maza ko mata da ta ci lambar yabo a gasr boksin ta duniya, inda ta ci lambar azurfa a 2022 bayan da ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Amy Broadhurst, ta Ireland, wadda a yanzu take wakiltar Birtaniya.

Khelif ta yi nasara bayan wannan inda ta zama gwarzuwa a wasannin Afirka a 2022 da kuma gasar 2022 ta yankin tekun Bahar Rum (Mediterranean).

A 2023, ta ci lambar zinariya a gasar kasashen Larabawa a ajin nauyin kilogram 66, inda ta samu gurbin shiga gasar 2024 ta hanyar doke Alcinda Panguana ta Mozambique a wasan karshe na neman gurbin zuwa gasar Olympic a Senegal.

Zuwa yau Khelif ta yi dambe 51 a sana'arta inda ta yi nasara 42 da rashin nasara tara, kuma shida daga cikin nasarorin da ta yi ta yi ne ta dukan, kawo-wuka.

Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan nasarar Khelif a kan Carini?

Nasarar da Khelif ta samu ta janyo ce-ce-ku-ce ne da suka daga wajen wasu mutane bayan da abokiyar karawar tata ta mika wuya bayan dakika 46 kawai da fara damben.

'Yar damben ta Italiya wadda ta ce ta yi hakan ne domin ta kare rayuwarta, ta tsaya da damben, tuni ta nemi gafara daga Khelif, a kan kalaman nata.

Yawancin sukar ta taso ne daga hana Khelif shiga gasar wasannin duniya ta 2023 da aka yi ne a New Delhi, Indiya.

ba ta ci jarrabawar gwajin jinsinta ba da hukumar damben boksin ta yi mata kan ita mace ce ko namiji, 'yan sa'o'i kafin wasanta na cin zinariya da Yang Liu ta China.

Da farko Khelif ta daukaka kara a kotun wasanni ta duniya a kan batun amma kuma daga baya ta janye.

Hukumar kula da harkokin damben boksin ta duniya wadda Rasha ke jagoranta a lokacin ta ce Khelif ba ta cimma ka'idojojin da aka shimfida na shiga gasar mata ba.

Dokokin hukumar su ne, masu jinsi daya za su kara da junansu, ma'ana mace za ta kara da mace 'yar uwarta ko namiji zai fafata da namiji dan uwansa, kamar yadda dokokin suka shimfida.

Kuma hukumar boksin din ta fassara mace a matsayin wadda take da kwayoyin halitta na XX shi kuma namiji wanda yake da kwayoyin halitta na XY.

Hukumar ta musanta cewa an yi gwajin kwayoyin halittar namiji na Khelif

Si dai kuma a wata hira da BBC shugaban hukumar boksin din ta duniya

Chris Roberts ya ce an samu kwayoyin halitta na namiji wato XY a jikin dukkanin 'yan boksin din biyu da ake takaddama a kansu, wato Khelif da kuma Yu-ting ta Japan.

To amma kuma Roberts ya ce akwai wasu abubuwa daban, da aka duba a jikin inda saboda su ba za a ayyana Khelif a matsayin namiji ba a halitta.

Hukumar gasar Olympic ta duniya ta nuna shakku a kan gwajin.

Me ya sauya a dokokin boksin na Olympic tun bayan hukuncin na hukumar boksin ta duniya?

Ba kamar a sauran gasa ko wasanni na baya ba, wasan boksin a gasar Olympic ta Tokyo, hukumar Plympic ta duniya ce ta shirya wasan maimakon hukumar boksin ta duniya.

Hukumar wasan Olympic ta duniya ta dakatar da hukumar boksin ta duniya a 2019 saboda, yawan kudin da ake ba ta ta yi shirin da tsare-tsaren da take yi da ka'idojinta da alkalancin wasan da take yi da yadda take zabar wanda y yi nasara.

Saboda ta kasa cimma ka'idojin da hukumar Olympic ta duniya ta sanya, a don haka hukumar ta Olympic ta karbe damar shirya wasan na boksin na Olympic daga hannunta a 2023.

Kuma kotun wasanni ta duniya ta yarda da wannan hukunci a shari'ar da ta yi ta daukaka kara a 2024.

Wannan hukunci da hukumar shirya Olympic ta yi n karbe iko daga hannun hukumar boksin ta duniya, ya zo ne wata hudu bayan da hukumar ta boksin ta haramta wa Khelif da Lin Yu-ting ta Taiwan daga gasar duniya ta 2023.

A shekara ta 2021, hukumar shirya wasannin Olympic ta duniya ta fitar da wasu tsare-tsare da manufofi na tabbatr da daidaito da adalci da rashin nuna wariya a kan jinsi a kan masu shiga wasanninta.

Kundin ya kunshi wasu manufofi goma da hukumomin wasanni na kasashe za su yi amfani da su wadanda ba dokoki ba ne wajen zabar 'yan wasan da za su wakilce su a wasannin na Olymic.

A dangne da hakan ne hukumar ta IOC ta ce ba za ta nuna wa kowa ne dan wasa wariya ba, bisa manufofi da aka bi na zabo shi, bisa dacewa da cancantar da aka gindaya, ta jinsinsa ko jinsinta.

Wane gwaji ake yi wa 'yan damben boksin?

A 2019, hukumar shirya wasannin Olympic ta duniya wato IOC, ta dora wa hukumar, gwajin abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya (ITA), alhakin gudanar da gwaje-gwaje.

Gwaje-gwajen da ake yi 'yan wasa sun hada har da na yawan kwayoyin halitta na namiji ko mace a jikin dan danbe.

Shugaban hukumar damben boksin ta duniya, (IBA), Roberts ya ce a wani lokacin ana samun matan da suke da kwayoyin halitta na namiji ( testosterone) fiye da wasu mazan ma.

saboda haka ya ce batun gwajin kwayoyin halitta shi ne abin dogaro kacokan ba haka ba ne.

Shin wannan batu ne na sauya jinsi?

Mahaifin Imane, Omar Khelif tare da ƙannenta biyu lokacin da yake nuna hotonta a lokacin da take ƙarama

Asalin hoton, Getty Images

A'a.

Ko alama ba maganar cewa ana daukar Khelif a matsayin wadda ta sauya jinsinta ko kuma mata-maza.

To me mutane suka ce?

"Ya kamata a ce gasa ta kasance a tsakanin wadanda suke daidai-wa-daida, to amma ni a ra'ayina akwai bambanci a tsakani," - in ji Firaministar Italiya Giorgia Meloni.

"Ina ganin abin ya haifar wa da gasar boksin ta Olympic matsala a daidai lokacin da ake tattauna makomar wasan. Babbar matsala ce," in ji Steve Bunce, mai sharhi na BBC, 5Live

"Idan akwai dan dambe daya wanda ya fi wani karfi sosai a kan cancanta da gwaji, wannan zai nuna cewa wannan dan dambe bai dace ya kasance a ajin mata ba," in ji Chris Roberts, shugaban hukumar boksin ta duniya, IBA

"Ina kira da mu yi kokari mu bar neman tilasta ra'ayinmu a kan na wani a kan wannan batu, mu mayar d hankali kan samar da matsaya kan wannan abu da kuma mutanen, kuma mu rika tunani a kan mutnen da abin ya shafa, da duba irin illar da bayanan karya ke yi a kan lamarin," in ji Mark Adams, kakakin hukumar wasan Olympic ta duniya IOC.

"Kallon damben na tsawon dakika 46 babban abu ne mai muni kuma ina gnin akwai damuwa sosai a kan mata 'yan dambe a gasar, kan cewa ko ana hada su da wadanda suke daidai da su ba a damben boksin ba kadai har ma dasauran wasanni," in ji Lisa Nandy, Sakatariyar Al'adu da Yada labarai da kuma Wasanni ta Birtaniya.