Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta samu tsohon shugaban Amurka da laifin cin zarafin lalata
Masu taya alƙali hukunci sun samu tsohon shugaban Amurka Donald Trump da laifin auka wa wata mai rubuta sharhi a mujalla, da lalata a wani kantin sayar da kaya na birnin New York a shekarun 1990.
Sun kuma samu Donald Trump da ɓata wa E Jean Carroll suna a watan Oktoban 2022 a kafar sada zumuntarsa mai suna Truth, inda ya bayyana zarge-zargen nata a matsayin "damfara".
Matar mai suna E Jean Carroll, 'yar shekara 79, ta ce Trump ya auka mata ne a kantin Bergdorf Goodman da ke unguwar masu hannu da shuni ta Manhattan a ƙarshen 1995 ko kuma a farkon 1996.
A cewarta, sun ci karo da juna a lokacin da suka je kantin sayayya.
Daga nan, sai ta yi zargin cewa Trump ya nemi jin ra'ayinta sa'ar da zai sayi rigar mama da ɗan kamfai don wata mace daban, inda cikin tsokana ya nemi ko za ta gwada don ganin dacewar kyawun tufafin.
Sai dai suna shiga ɗakin canza tufafi, Carroll ta yi iƙirarin cewa hamshaƙin mai arziƙin gine-ginen ya auka mata, inda ya tokare ta a bango, kuma ya ci zarafin ta.
Carroll, wadda ta riƙa wallafa sharhi mai taken "Ask E. Jean" a mujallar Elle daga 1993 zsuwa 2019, ta yi iƙirarin cewa ta yi ƙoƙari, ta tunkuɗe Trump bayan an sha "matuƙar gaganiya".
Ba ta kai rahoton zargin wannan al'amari ga 'yan sanda ba, kamar yadda takardar ƙorafinta ta nuna, saboda ta yi matuƙar "gigicewa kuma ta yi fatan kada ta ɗauki kanta a matsayin wadda aka yi wa fyaɗe".
Masu taya alƙali yanke hukuncin dai sun ce ba su samu Donald Trump da laifin yi wa E Jean Carroll fyaɗe ba.
Sai Trump ya biya matar diyyar $5m
Duk da haka, sun nemi tsohon shugaban na Amurka ya biya diyyar jimillar kuɗi har dala miliyan biyar ga E Jean Carroll saboda yin amfani da ƙarfi da kuma ɓata mata suna.
Wannan ne karon farko a tarihi, da aka taɓa samun wani shugaban Amurka da auka wa mace da lalata.
Kafin a karanto hukuncin kotun, E Jean Carroll ta zauna shiru, cikin tsakiyar lauyoyi.
Ta riƙe hannuwan lauyoyinta, lokacin da ake karanto hukuncin, inda ta zura idanu gaba, tana kuma ɗan sunkuyar da kai lokacin da masu taya alƙali hukunci suka ba da sanarwar cewa sun samu tsohon shugaban na Amurka da laifin ɓata mata suna.
Ta yi tattausan murmushi a lokacin da suka ce gaba ɗayansu sun yarda, sai Trump ya biya ta diyyar dala miliyan biyar.
Bayan masu taya alƙalin hukuncin sun tashi sun bar kotun ne kuma, sai lauyan Trump, Joe Tacopina ya miƙe, ya je wurin Carroll inda ya yi musabaha da ita.
“Ina taya ki murna," ya ce mata. "Allah taimaka, shi kenan?”
Martanin Trump a kan hukuncin
Donald Trump dai ya mayar da martani a kan hukuncin, inda ya rubuta saƙonsa da manyan baƙaƙe a kafar sada zumuntarsa ta Truth.
"KWATA-KWATA BAN SAN MA WACE CE WANNAN MATAR BA. WANNAN HUKUNCI, ZUBAR DA MUTUNCI NE - CI GABA DA GAGARUMIN BI-TA-ƘULLI NE MAFI GIRMA A TSAWON ZAMANI!", tsohon shugaban Amurkan ya ce.
Daga bisani, ɓangaren tsohon shugaban na Amurka ya fitar da wata sanarwa, wadda ta nanata iƙirarin da aka saba ji na cewa "bi-ta-da-ƙulli" ne a kan Donald Trump daga jam'iyyar Dimokrat.
"Kada a raba ɗaya biyu, ɗaukacin wannan shari'ar bogi, wani yunƙurin siyasa ne a kan Shugaba Trump saboda a yanzu shi ne gawurtaccen ɗan siyasar da ke kan gaba, kuma za a sake zaɓar sa Shugaban Amurka."
"Ci gaba da tozarta gagarumin Tsarin Mulkinmu don cimma muradin siyasa abin ƙyama ne kuma ba za a lamunci hakan ba," sanarwar ta ci gaba da faɗa.
"Ƙasarmu tana cikin gagarumar masifa, idan za a cika kotuna da jerin iƙirari, ba kuma tare da wata hujja ko shaida ko wanda ya gani ba, don samun maki a siyasance."
Ɓangaren Trump ɗin ya kuma ce za su ɗaukaka ƙara kan wannan shari'a.