Real Madrid ta kai wasan karshe a Champions League na bana

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta kai zagayen karshe a Champions League na bana, bayan da ta doke Bayern Munich 2-1 ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Bayern Munich ce ta fara cin kwallo ta hannun Alphonso Davies, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Daga baya ne Joselu ya farke, sannan ya kara na biyu daf da za a tashi daga wasan, inda hakan ya sa ta kai wasan karshe da cin 4-3 gida da waje.

Ranar Talata Bayern Munich da Real Madrid suka tashi 2-2 a wasan farko a Allianz Arena zagayen farko a daf da karshe.

Da wannan sakamakon Real Madrid za ta kara da Borrussia Dortmund a wasan karshe ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Dortmund ta kai wannan matakin bayan da ta yi nasara a kan Paris St Germain da cin kwalla 2-0 gida da waje.

Real Madrid, wadda ta lashe La Liga na bana na 36 ranar Asabar, na fatan daukar Champions League na 15 jimilla.

Ita kuwa Dortmund ta dauki babban kofin zakarun Turai daya, shi ne a 1996/97, bayan da ta doke Juventus 3-1 ranar Laraba 28 ga watan Mayun 1997.

Wannan shi ne karo na uku da Dortmund za ta buga wasan karshe a Champions League, bayan da ta lashe kofin a 1996/97 da kuma 2012/13 a Wembley.

Dortmund ta yi rashin nasara a wasan karshe a Champions League a hannun Bayern Munich da cin 2-1 ranar Asabar 25 ga watan Mayun 2013.

·