Ko shigar da abinci Najeriya zai samar da mafita ga tsadar rayuwa?

..

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da wasu matakai uku na kawo sauki ga halin matsi da al'ummar kasar suke ciki.

Daya daga cikin matakan shi ne, gwamnatin za ta fito da tan 42,000 na abinci daga rumbunan ma'aikatar harkokin noma da nufin kawo sauki ga halin matsin rayuwa da al'ummar kasar ke fama.

Bayan nan gwamnatin ta ce ta tattauna da masu kamfanonin sarrafa shinkafa a fadin Najeriya inda suka amince su fito da tan 60,000 domin sayar wa al’umma fadin kasa.

Mataki na uku da gwamnatin ta ce za ta iya dauka idan har matsalar ta faskara shi ne na shigar da abinci daga kasashen waje domin magance tsadar abinci a Najeriya.

Shin ko me wadannan matakan ke nufi? Wane tasiri za su yi? Sannan ta ya ya za su sauya tsadar rayuwar da mutane ke fuskanta?

Abubuwan da wannan makalar za ta duba ke nan.

Wani masanin tattalin arziki da harkar samar da abinci, Dr Muhammad Suleiman Kani, kuma malami a kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayyar da ke Kano, ya ce daukar irin wannan matakin abu ne mai kyau da zai kawo wa jama'a sauki ga hali na tsananin matsi da suke ciki.

Ya ce duk lokacin da kasa ta fuskanci irin wannan matsi, to gwamnati tana bijiro da wasu dabaru na kawowa jama'a sauki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ya ce kayan abincin da gwamnati ta yi magana "ba wai kyauta za ta bai wa yan Najeriya ba."

Ya ce abin da gwamnatin za ta yi shi ne za ta yi rangwami ne a kan farashin kayan abinci inda ya ba da misali da idan farashin kayan abinci ya kai dubu goma, toh gwamnati sai ta siyar a kan dubu bakwai ko dubu takwas.

Kenan "gwamnati ta ba da tallafi a kan kayan abinci a cikin Najeriya." kamar yadda kwararren ya bayyana.

Ya ce matakin zai tallafa wa jama'a ganin yadda har yanzu albashin ma'aikata ba sauya ba duk da halin da ake ciki sannan dan kasuwa shi ma yana fuskantar koma-bayan ciniki saboda mutane na fama wajen samun kudin da za su shiga kasuwa.

Ya ce tsugunu ba ta kare ba a damar da gwamnati ta bayar na ba da dala ga duk mai son shigar da abinci daga wasu kasashen kasancewar dalar ta yi karanci a babban bankin Najeriya.

"Domin duk wanda zai siyo abinci a waje, ko dai ya canza naira zuwa dala, ko naira zuwa CFA, ko zuwa me ka canza naira, idan ka siyo abincin ba za ka sayar da shi a kan sauki ba." in ji Dr Kani.

Dr Muhammad Suleiman Kani ya ce matukar gwamnati na son kawo sauki toh kamata ya yi gwamnati ta haramta shigar da duk kayan da za a iya samu a Najeriya.

A cewarsa, idan gwamnati ta dauki wannan mataki, ya kamata ta hanzarta tayar da komadar kamfanoni da wutar lantarki domin su tsaya da kafafunsu.

Ya kuma yi kira ga shugaban kasa ya tashi tsaye wajen yin abin da ya dace domin fitar da Najeriya daga kangin da take ciki.

A cewar masanin, ya kamata gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar wa jama'a bayan janye tallafin man fetur na kara albashi da inganta walwalar al'umma da tayar matatar mai ta Fatakwal.

Yadda gwamnati za ta aiwatar da tsarin

A cewar kwararren kan samar da abinci, tsarin shigar da abinci daga wasu kasashen hanya ce mai kyau sai dai akwai bukatar gwamnati ta sa ido domin tabbatar da cewa tsarin ya tafi sumul kalau ga amfanin yan kasa.

Ya ce "dole hukumomin tsaro su sa ido saboda dabi'ar yan Najeriya, za a iya shigar da kayan abincin sai ka ga wasu tsirarun mutane sun debe abincin an sauya buhu, sun kai shi kasuwa ana kuma cinikinsa."

Ya kuma ce bai kamata gwamnati ta sake kuskuren bayar da abincin ta hannun gwamnoni ba, kasancewar irin wannan tsarin a baya, bai yi nasara ba.

Dr Kani ya ce a yi amfani da kasuwannin da ake da su da kuma cibiyoyin gwamnati na harkar abinci, sannan a yi tsarin a bude, "babu maganar gwamnoni ko yan majalisa."

Ya ce gwamnati ta aiwatar da abin da kanta sannan ta saka yan farar hula da za su sa ido kan yadda tsarin ke tafiya domin tabbatar da an yi shi bisa gaskiya.

Tsarin zai shafi 'yan kasuwa...

Dr Muhammad Kani ya bayyana cewa tsarin na gwamnati zai iya shafar harkokin yan kasuwa inda ya ce a wasu kasashe kamar Amurka gwamnati tana siyan kayan abinci sai ta rage farashinsu a duk lokacin da aka gama harkokin noma.

Ya ce tsarin bai tsaya iya nan ba, Saudiyya ma tana aiwatar da irin tsarin.

"A Saudiyya, akwai lokacin da idan kaya suka yi yawa sai ta gayyato manoma, ta ce kada su yi noma," tana tambayar nawa ce ribarsu sai ta dauki ribar ta basu.

"Saboda idan ya yi yawa ya wuce hankali za a yi asara, za ku noma ba ku ci riba ba." kamar yadda ya ce.

A cewar masanin, daukan wannan tsarin zai kawo gasa kuma zai sa wadanda suke samar da abin na cikin gida suma su karyar da farashin kayansu.

Matsalolin da ka iya yi wa tsarin tangarda

Masanin ya ce rashin isassun rumbuna ka iya kawo tarnaki ga matakin shigo da kayan abincin saboda rashin tanadin wuraren da za a ajiye su wanda hakan zai iya jawo lalacewarsu.

Ya kuma a yanzu gwamnatin ba ta da kayan abincin a kasa, a yanzu ne za ta shigo da su kuma abin tambayar a cewarsa shi ne da wane kudi za ta siyo kayan?

Ya ce ma'ana dole sai gwamnati ta ciwo bashi domin sayo kayan abincin.