Abin da ya kamata ku sani kan kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa

Asalin hoton, Getty Images
Kisan kiyashin Yahudawa ya faru ne lokacin Yaƙin Duniya na Biyu (1939-1945), lokacin da aka kashe miliyoyin Yahudawa saboda aƙidarsu.
Jam'iyyar ƴan Nazi ta Jamus ƙarƙashin jagorancin marigayi Adolf Hitler ce ta kitsa kashe-kashen.
Yahudawa ne manyan waɗanda ƴan Nazi suka kitsa kashewa kuma mafi yawan mutanen da lamarin ya shafa Yahudawa ne. An kashe kusan bakwai cikin duk Bayahude 10 a Turai saboda kabilarsu.
Yan Nazi sun kuma kashe sauran mutane har da yan Roma da masu bukata ta musamman. Sun kuma kama tare da kwace yancin sauran mutane kamar masu neman jinsi da yan hamayyar siyasa. Akasarinsu sun mutu sanadin yadda ake tafiyar da al'amuransu.
Kisan Kiyashi na holocaust misali ne na kisan kare dangi. Kisan kare dangi shi ne kisan gomman mutane da gayya galibi saboda kabilarsu ko addininsu ko kuma kasarsu.
Su wane ne yan Nazi?
Nazi takaitaccen suna ne na kungiyar National Socialist German Workers' Party wato (NSDAP).
Jam'iyyar yan Nazi jam'iyyar siyasa ce a Jamus da aka kafa ta a 1919 bayan yakin duniya na daya.
Ta samu karbuwa a shekarun 1920 yayin da kasar ke fama da tasirin da yakin duniyar ya haifar. Jamus ba ta yi nasara ba a yakin inda aka tilasta mata biyan makudan kudi ga wadanda suka yi nasara.
Akasarin mutane matalauta ne kuma babu isassun ayyukan yi sannan wani dalili daya da ya sa Jamusawa da dama suka koma Nazi shi ne fatan cewa za su kawo sauyi.

Asalin hoton, Getty Images
Yan Nazi suna da kabilanci sannan sun yi amannar cewa abin da suka kira kabilar Aryan ta fi saura muhimmanci. Yan Nazi sun ce dan kabilar Aryan yana da tsatson Jamus. Yan Nazi na tunanin cewa Yahudawa da yan Roma da bakar fata da sauran kabilu ba su kai darajar yan Aryan ba.
Yan Nazi sun ki jinin Yahudawa kuma hakan ya shafi dukkan manufofinsu da ayyukansu.
Suna ganin Jamus kasa ce da ta fi sauran kasashe sannan fifikon da mutanensu ke da shi na nufin za su iya kuma ya kamata su zama a saman sauran mutane. Wannan ne ya sa Jamus ta mamaye tare da kwace ragamar sauran kasashe kafin da kuma lokacin yakin duniya na biyu.
Wane ne Adolf Hitler?
A 1921, wani mutum da ake kira Adolf Hitler ya zama shugaban jam'iyyar.
Sannan a Janirun 1933, an gayyaci yan Nazi su kafa gwamnati bayan da aka zabe su a matsayin jam'iyya mafi girma a wani zabe.
Daga lokacin, jam'iyyarsa ta samu mulki, Adolf Hitler ya shiga kakaba manufofin Nazi a dukkan al'amuran Jamus, sun kwace iko ta hanyar tsoratarwa da cin zarafi.

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da shugaban Jamus Hindenburg ya mutu a 1934, Hitler ya ayyana kansa a matsayin mai mulkin kama karya ko 'jagoran Jamus'.
Abu uku mafi muhimmanci ga Hitler da yan Nazi su ne:
- Daukakar Jamus
- Bauta wa mai mulkin kama karya, Adolf Hitler
Jam'iyyar ta yi amfani da abubuwan farfaganda domin janyo hankalin mutane su goyi bayansu. Sun gudanar da manyan taruka sannan lasifikoki da aka dasa a wuraren jama'a suna kwarmata sakonnin Nazi.
Mene ne kisan kiyashi na Holocaust?
Holocaust abu ne da ya soma da nuna wariya a kan Yahudawa sannan ya kare da kisan miliyoyin mutane saboda kabilarsu. Tsari ne da ya zama mummuna da tafiya ta yi tafiya.
Zaluncin Nazi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga lokacin da suka fara mulki a 1933, Nazi ta zalunci mutane da ba su ga girmansu a matsayin mutane ba - galibi Yahudawa.
Sun bijiro da dokoki da suka nuna wariya gare su sannan suka kwace musu hakkokinsu. Ba a barin Yahudawa su shiga wasu wurare sannan an haramta musu yin wasu ayyukan.
Sun kuma soma kafa sansanoni inda suke iya tura mutanen da suke tunanin "makiyan kasar ne" domin kulle su tare da tilasta musu yin aiki. Wannan ya kunshi Yahudawa da duk wani da ba ya goyon bayan su.
An kafa sansani na farko da ake kira Dachau a Maris din 1922 a wajen birnin Munich.
Tsakanin 1933 da 1945, yan Nazi sun samar da fiye da sansanoni 40,000 a yankunan da suka mamaye.
Wasu sansanonin na aiki ne, wasu kuma a matsayin na wucen gadi domin tantance fursunoni sannan wasu - na farko a cikinsu da aka bude a 1941 - za su zama na wanzar da kisa, inda Nazi ke iya kashe mutane da yawa.
Masu gadin sansanonin sun kashe galibin mutane ba tare da wani dalili ba sannan wasu da dama sun mutu sakamakon mummunan yanayin da suke ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Yan Nazi sun kuduri aniyar kwace ragamar tafiyar da rayuwar kowa.
A 1934, an samar da wata doka ta yaki da munafunci wadda ta ce laifi ne a yi wata zolaya a kan yan Nazi.
An haramta waka ta Jazz, an sake rubuta litattafan da ke dauke da manufofin Nazi, an saka hotunan Hitler a ko ina sannan an lalata litattafan da ba a rubuta su ba a yanayin da yan Nazi suke so.
A 1935, an rufe gidajen jaridu 1,600 sannan wadanda aka kyale an ba su damar su buga labaran da yan Nazi suka amince da su ne kawai.
Sun kafa wasu kungiyoyi na matasa da ake kira Matasan Hitler (ga samari) da BDM (ga yanmata), don su zama masu akidar Nazi da ke bauta wa Hitler yayin da suke tasowa. Ana nuna koya wa maza akidun Nazi ana kuma sa su yi tanadin yaki, su kuma mata ana koya musu girki da dinki.

Asalin hoton, Getty Images
Harin Jamusawa da kisan miliyoyi
Wata muhimmiyar rana ita ce 9 ga watan Nuwamban 1938 lokacin da aka ga wani dare da aka ga mummunan tashin hankali a kan Yahudawa.
Ana kiran yanayin Kristallnacht - 'daren fasassun gilasai' - saboda dukkan gilasan da aka farfasa daga shagunan da aka kai wa samame da suka warwatsu a kan tituna.
An kashe Yahudawa 91, an kama 30,000 inda aka tura su sansanonin horaswa da lalata wuraren ibada 267.
A ranar 1 ga watan Satumban 1939, Jamus ta yi mamaya a Poland abin da ya jawo yakin duniya na biyu.
An tilasta wa Yahudawa a Poland yin rayuwa a kebabbun wurare da ake kira na marasa galihu inda ake nuna musu rashin kulawa sannan an kashe mutane da dama.
Yanayin wuraren ya yi muni kuma galibi sun rasa rayukansu saboda cuta da yunwa.

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa 1940, yan Nazi suna neman hanyar da za su iya kashe gomman mutane a kankanin lokaci domin kawar da al'ummar Yahudawa.
Sun bijiro da tsarin kafa sansanonin kisa inda suke iya kashe mutane da dama. Wannan ne abin da suke kira 'maslaha ta karshe'.
A karshen 1941, aka kafa sansani na farko da ake kira Chelmno a Poland.
Akwai sansanoni shida jumulla a yankunan Poland da ke karkashin Nazi: Auschwitz-Birkenau (mafi girma) sai Belzec da Chelmno da Majdanek da Sobibor da Treblinka.

Asalin hoton, Getty Images
Yan Nazi da kawayensu sun kuma kafa sansanoni a wajen Poland (a Belarus da Serbia da Ukraine da Croatia) inda dubban mutane suka mutu.
Tsakanin 1941 da 1945, an kashe mutane a wani yanayi da duniya ba ta taba gani ba.
An kama miliyoyi an kuma cunkusa su a jiragen kasa zuwa sansanonin inda ake tilasta musu su yi aiki ko a kashe su.
Su wa aka kashe ko aka ci zalin su a kisan kiyashin Holocaust?
Mun san mutanen da abin ya shafa sun hada da:
- Yahudawa
- Al’ummar kabilun Romani da Sinti
- Al’ummar Slavic, mazaunan Tarayyar Soviet da Poland da Yugoslavia
- Mutane masu nakasa
- ‘Yan luwadi
- Bakaken fata
- Mabiya akidar Jehovah Witness
- ‘Yan adawar siyasa
Ta yaya aka kawo karshen kisan kiyashin Yahudawa na Holocaust?
Yayin da dakaru masu yaki da Jamus a yakin duniya na biyu - wato dakarun Burtaniya da Amurka da Tarayyar Soviet da kawayensu - suka fara kutsawa cikin yankunan Turai da ‘yan Nazi ke iko da su sai suka fara cin karo da sansanonin.
Lokacin da alamu suka bayyana karara cewa za a yi galaba a kansu, sai ‘yan Nazi suka fara yunkurin boye alamun da za su bankado ta’asar da suka aikata ta hanyar lalata sansanonin.

Asalin hoton, Getty Images
Sun tursasa wa fursunonin yaki da suke a raye a Poland su taka a kafa zuwa sansanonin da ke cikin Jamus.
Fursunoni da dama sun mutu a lokacin wannan tafiya mai tsananin wahala.
Sai dai ‘yan Nazi sun kasa boye shaidun abubuwan da suka aikata, inda ba da dadewa ba duniya ta gano munin wannan kisan kiyashi.
Majdanek ne sansani na farko da aka kwato a shekarar 1944.

Asalin hoton, Getty Images
Mutanen da suma isa domin ‘yantar da sansanonin sun bayyana yanayi mai matukar muni da suka tarar.
Da dama daga cikin wadanda aka tseratar daga sansanonin sun mutu daga baya saboda rashin lafiya sanadiyyar azabar da suka sha a lokacin da suke a daure.
Hatta bayan yakin rayuwa ta yi musu matukar wahala.
Da dama daga cikin wadanda suka rayu sun iske wasu mutanen na rayuwa a muhallansu, wasu kuma sun gaza samun matsuguni.
Kasashen duniya ba su nuna aniyar karbar irin wannan dandazon ‘yan gudun hijira ba saboda yawansu.
Ko an hukunta ‘yan Nazi kan Kisan kiyashi na Holocaust?
A ranar 11 ga watan Disamban 1946 Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da hukuncin cewa kisan kiyashi zai zamo cikin manyan laifuka a tsari na dokar kasa da kasa.
Adolf Hitler ya kashe kansa kafin a kai karshen yakin, saboda haka babu yadda za a yi ya fuskanci shari’a.
Tun bayan kawo karshen Yakin duniya na biyu, an rika gurfanar da manyan ‘yan Nazi a gaban shari’a bisa laifukan da suka aikata.
Ko a baya-bayan nan, cikin watan Yulin 2015, wata kotu a Jamus ta yanke hukunci kan wani tsoho mai shekara 94 a duniya, Oskar Groening bayan samun shi da laifi kan abubuwan da ya aikata, wanda ya kasance mai gadi ne a sansanin Auschwitz.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai ba za a iya hukunta dukan masu hannu a lamarin ba.
‘Yan Nazi da dama sun buya bayan kawo karshen yakin kuma ba a iya gano su ba, wasu kuma sun mutu kafin a gano cewa sun aikata laifukan.
Ta yaya ake tunawa da Kisan kiyashin Holocaust?
A yanzu duniya ta amince da girman laifin da aka tafka a lokacin Kisan kiyashi na Holocaust kuma ya zamo misali na irin mummunan hali da Kisan kiyashi ke haifarwa da kuma bayyana irin dabi’u da ke iya haifar da shi.
To amma abin bakin ciki shi ne Holocaust ba shi ne kadai kisan kiyashi da ya faru a tarihin duniya ba.
An kashe miliyoyin mutane a Cambodia da Rwanda da Bosnia da Darfur, kawai saboda kabilarsu.
A ranar 27 ga watan Janairu na kowace shekara, al’umma a Burtaniya na tunawa da kisan kiyashi na Holocaust.
Ana tunawa da lamarin a wannan rana ce kasancewar a irin ranar ce cikin shekarar 1945 dakarun Tarayyar Soviet suka ‘yanta sansanin kisan kiyashin ‘yan Nazi mafi girma na Auschwitz-Birkenau.

Asalin hoton, View Pictures
Ana tunawa da Kisan kiyashi na Holocaust ne ba domin jimamin miliyoyin mutanen da aka kashe a wancan lokacin kawai ba, har ma da sauran mutanen da aka kashe a wasu kashe-kashen kiyashin da aka aiwatar a fadin duniya.
Yana tunatar da mutane muhimmancin hakuri da juna, hakuri da addini ko bambance-bambance da ke tsakanin al’umma, da kuma guje wa yada kalamai na kiyayya.
Yana kuma tunayar da mu abubuwan da suka faru a lokacin ma Holocaust ta yadda za mu hana sake faruwar wani abu makamancinsa a nan gaba.
Gidauniyar ranar tunawa da kisan kiyashin Holocaust ta yi bayanin yadda ranar ke kasancewa ta “yin aiki tare domin samar da yanayi na tsaro a gaba”.










