Amrish Puri: Mugu a fim, mai sauƙin kai a zahiri

    • Marubuci, रेहान फ़ज़ल
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, बीबीसी हिंदी
  • Lokacin karatu: Minti 6

A lokacin da Shekhar Kapur ya fitar da fim dinsa mai suna Mr. India a shekarar 1987, sai ya kasance wanda ya taka rawar mugunta a fim ɗin, Amrish Puri, wanda ya fito da sunan Mogambo, ya fi ɗaukar hankalin jama'a fiye da jaruman fim ɗin

Rawar da ya taka ta "Mogambo" ta zama wani babban abin tunawa a tarihin Bollywood.

A cikin littafinsa mai suna 'Pure Evil: The Badmen of Bollywood', Balaji Vittal ya ce: "Mogambo yana da dukkan siffofin da ake buƙata domin rawar mugu a fina-finai, amma ba ya son cin zarafin mata."

Hanyar da yake amfani da ita wajen jan hankalin mutane ta yi kama da ta yara. Yana sa mabiyansa su yi masa gaisuwar 'Hell Mogambo' a irin salon Hitler sannan kuma ya ce kalmar 'Mogambo khush hua' da yake yawan faɗa bayan kowanne fim ya rage tsananin muguntarsa a wajen kallo, har ma wasu suka fara yaba masa.

An haifi Amrish Puri ne a Nawanshahr, jihar Punjab. Ya yi makaranta a BM College, Shimla.

A shekarar 1950, ya koma Bombay, inda ya kasance kafin ya je, 'yan uwansa biyu Madan Puri da Chaman Puri sun riga suna shiga harkar fim.

Amrish Puri, wanda ya shahara da malfarsa ta musamman ya kasance yana da kafaɗa manya kuma dogo ne kuma yana da babbar murya, ya samu damar shiga fim ta farko ne a wajen Alkazi, fitaccen ɗan fim a Indiya.

Wani abokinsa, SP Meghnani, ne ya haɗa shi da Alkazi.

Amrish Puri ya rubuta a cikin tarihin rayuwarsa 'The Act of Life' cewa; 'Alkazi ya ba ni gudunmuwa sosai a harkar fim.

"Ya tambaye ni ko ina sha'awar wasan kwaikwayo. Da na ce e, sai ya fito da labarin fim ɗin ya ce ni ne zan zama jarumi fim ɗin mai suna 'A View from the Bridge."

Daga wannan fim ɗin ne Amrish Puri ya riƙa samun ci gaba a harkokin, har ya samu ɗaukaka da shahara.

Fim ɗin Sakharam Binder

Bayan haka, Amrish ya taka rawar gani sosai a fim ɗin Vijay Tendulkar mai suna Sakharam Binder

Fim ɗin ya kasance labarin wani matashi wanda bai yi aure ba, wanda ya ɗauko wata mace zuwa gidansa suka zauna tare.

A cikin wannan fim ɗin, Amrish Puri ya yi amfani da kalmomi marasa kyau da ake wa kallon batsa.

Amrish Puri ya rubuta cewa: "Na yi matuƙar mamaki ganin mutanen jihar Maharashtra da suka san yadda ake shirya fina-finai tun a baya, amma suka ɗauki wannan fim ɗin a matsayin batsa. Wannan abin taƙaici ne."

Wani jigo kuma masanin wasan kwaikwayo da Amrish Puri ya yi aiki da shi kuma shi ne Satyadev Dubey.

Ya taɓa tunawa da shi yana cewa' "Ba abu mai sauƙi ba ne haɗa aiki da fim kamar yadda Amrish ya riƙa yi. Amma shi ya san yadda yake tsara lokacinsa."

A lokacin da ya fara fim, ko biyansa albashi ba a yi, a ƙarshe ya rage fitowa a wasannin gidan gala saboda ya fi mai da hankali kan fina-finai, amma kafin nan ya riga ya bayar da gudummawa fiye da kowane ɗan wasan kwaikwayo a gidajen galar Indiya.

Dubey ya kuma bayyana ra'ayinsa game da halin tsantsanin Amrish, inda ya ce duk wahalar da ya sha ba ta sa gwiwarsa ta yi sanyi ba.

Shyam Benegal ya ba shi dama a fina-finai

Shyam Benegal ne ya fara ba Amrish Puri dama a fina-finai bayan ya ga basirarsa a wasan daɓe.

Ya fito a fim ɗin Manthan da Nishant da Bhoomika, wanda hakan ya haɗa su a matsayin manyan abokan aiki a harkar fim.

Amrish ya fara fim ne yana kusan shekara 40.

A wata hira, Benegal ya ce: "Na saba ganin wasanninsa tun kafin na na saka shi a cikin fim ɗin Nishant. "

Ya ƙara da cewa: "A fim ɗin Mandi ya taka rawa sosai. Kuma a lokacin da ake ɗaukar fim ɗin Sardari Begum, ya tallafa wa matashiya Smriti Mishra ta hanyar ƙarfafa mata gwiwa."

Amrish kansa ya amince cewa yin aiki tare da Shyam Benegal ne ya ɗaga darajarsa a harkar fim.

A cikin tarihin rayuwarsa ya rubuta cewa: "Shyam mutum ne da yake da cikakken hangen abin da yake son nuna wa a kowanne shiri, kuma ba ya yarda a tsoma baki cikin shirinsa. Amma hakan ba yana nufin ba ya karɓar shawarwari ba. Abin da kawai yake so shi ne a sanar da shi duk wata gyara kafin a yi."

Ya ƙara da cewa: "Shyam da Govind Nihalani duk sun san abin da suke buƙata daga gare ni, ni kuma na san yadda za su gabatar da ni. A wurinsu kawai nake samun manyan rawar da nake takawa masu ma'ana.

Amrish Puri ya yi aiki a wasanni da fina-finai da yawa na Vijay Tendulkar, inda saurin aikinsa da muryarsa da jajircewarsa a fim ɗin Sakharam Binder suka burge marubucin.

Ya kuma kira wani daraktansa, Girish Karnad, "mafi kwararewar marubucin falsafa".

A fim ɗin Kaadu, rashin iya harshen Kannada ya zama ƙalubale gare shi wanda hakan ya saka aka rage rawar da zai taka, kuma fim ɗin ya samu karɓuwa sosai a kasuwa.

Rawar da ba za a manta da ita ba

Amrish Puri yana da baiwa ta musamman wajen a fim.

Abokin aikinsa kuma darakta, Govind Nihalani, ya ce a fim ɗin Tamas, ya taka rawar dattijo Sikh mai ƙarfin hali.

Subhash Ghai, shahararren darakta, shi ne ya fara ba shi matsayin mugun a fim ɗin Krodhi.

A wurin ɗaukar fim, yana ajiye abota a gefe, inda yake ɗaukar darakta a matsayin jagora.

A lokacin ɗaukar fim ɗin Yaadein, Ghai ya tsawata masa, amma Amrish bai ji haushi ba. Daga baya, Ghai ya ji kunya har ya je ya nemi afuwarsa.

Tara agogo da takalma

Ana cewa Amrish Puri ne ya sa askin ƙwal-kwabo ya zama abin kyan gani a Indiya.

Da farko yana da gashi mai yawa, amma darakta Rakesh Kumar ya shawarce shi ya aske kansa don rawar da zai taka a fim ɗin Dil Tujhko Diya a matsayin Dada.

An ce fim ɗin zai kammala cikin wata ɗaya da rabi, amma ya ɗauki shekara ɗaya da rabi kafin ya fito.

Daga baya sai ya koma saka hular malfa, kafin ya fara tara na'ukan hula daban-daban.

Baya ga hula, yana sha'awar tara takalma da agogo. Ya bayyana cewa yana da wahalar samun takalmin da ya dace da ƙafarsa, shi ya sa a wani lokaci da ya je Agra ya saya takalma guda 65 lokaci guda.

Har ma idan yana yin fim ya ga takalmi mai kyau, sai ya roƙi darakta ya ba shi kyauta.

A jimilla, Amrish Puri ya fito a fim ɗari uku da goma sha shida (316).

Fim ɗin Netaji Subhash Chandra Bose, The Forgotten Hero na Shyam Benegal ne fim na ƙarshe da ya yi.

A ƙarshen rayuwarsa ya kamu da cutar sankarar jini, inda ya rasu a ranar 12 ga watan Janairun 2005 yana da shekara 73.

Ba a cika samun 'yan fim da aka ba lambar girmamawa ta Sangeet Natak Akademi ba, amma shi ya samu wannan karramawa a shekarar 1979 saboda gudummawarsa a harkar wasan kwaikwayo.