Abu huɗu da za ki yi la'akari kafin ci gaba da hulɗa da tsohon saurayinki

    • Marubuci, Emily Holt
  • Lokacin karatu: Minti 4

Rabuwar masoya na da wahala a soyayya - yanayi ne na rabuwa da mutumin da ba kya ɓoye masa komai a rayuwarki.

Don haka wasu ke ganin ci gaba da hulɗa da juna bayan rabuwar soyayya ya fi komai zafi.

“Ban san mutane masu yawa da suka ci gaba da hulɗa da tsoffin samarinsu bayan rabuwar soyayya ba,'' a cewar Olivia Petter, mawallafiyar fitaccen liffafin soyayyar nan mai suna ''Millennial Love''.

Amma ta ce hakan ba yana nufin ba a samu ba, sai dai ba su da yawa.

Don haka ne ma ta bayar da wasu shawarwari na abubuwan da za ku yi la'akari kafin komawa ci gaba da soyayyar.

Ta lissafo wasu abubuwa huɗu da ta ce ya kamata ki yi la'akari da su wajen ci gaba da hulɗa ko yanke alaƙa da tsohon saurayinki.

1. Yaya ƙarfin soyayyarku kafin rabuwar?

“Tana da wani saurayi da a baya ta sha romon soyayya da shi, amma daga bara suka koma mutunci bayan rabuwar soyayyar,'' kamar yadda Olivia ta shida wa BBC.

Ta ce “Shaƙuwar da muka yi a baya baya ta taimaka wajen yafewa juna tare da zama sabbin abokai a yanzu ba tare da wata damuwa kan abin da ya faru a baya ba,''.

To sai dai ta ce har yanzu ba su zama abokai na ƙut-da-ƙuta ba, ana dai abotar sama-sama.

Mai horars da masoya soyayya, Kate Mansfield ta ce soyayyar da ba ta yi ƙarfi ba, ba ta da wasu matsaloli masu yawa, don haka mayar da ita abota ba zai zamo da wahala ba.

To amma ta ce soyayyar da ta yi ƙarfi na ƙunshe da wasu abubuwan da ba za manta da su ba don haka mayar da ita abota na da matukar wahala ''ya dai danganta da karfinta''.

Kate ta ce “Ya danganta da yadda soyayyar ta zo ƙarshe, da wanda ke da laifi wajen rabuwar, laifinku ne duka ko na ɗaya ne? Duka waɗannan na da tasiri wajen sake hulɗar masoya bayan rabuwarsu''.

2. Kun yafe wa juna?

Babbar matsalar da ke hana sake hulɗa da juna bayan rabuwa ita ce rashin rafiya.

“Ya kamata ku shirya wa rabuwar, ba kawai ku rabu bagatatan ba,'' a cewar Kate.

Yana da kyau ku fahimci cewa ko akwai wata halayya da ɗabi'a guda da dukkanku ke da ita, kamar son shan gahawa ko zuwa bakin teku ko zuwa yawon shaƙatawa ko zuwa asibiti duba marasa lafiya, tun kafin ku fara soyayya.

''Inda ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan abubuwan ne suka haɗa ku a soyayya, to akwai yiwuwar sake hulda tsakaninku ko bayan rabuwa''.

Ƙwararriyar mai horas da soyayyar ta ce ''amma idan sha'awar junanku ce ta sa kuka fara soyayyar tun da farko, to zai yi wahala ku iya sake hulɗa bayan rabuwa'', in ji ta.

Haka kuma yana da matuƙar muhimmanci ku yarda da kanku kan dalilin da ya sa za ku ci gaba da kasancewa abokai.

''Sake hulɗa ko abota bayan rabuwar masoya zai yiwuwa kawai idan akwai yarda da juna, kuma babu wata ɓoyayyiyar manufa tsakaninku'', in ji Kate.

3. Tsawon wane lokaci aka shafe bayan rabuwar?

Abu ne mai wahala komawa abota bayan rabuwar masoya.

"Yana da kyau ku ɗan samu lokaci domin manta abubuwan da suka faru na ɓacin rai tare da nazarin rayuwar da za a ɗora,'' a cewar Olivia.

Fitacciyar mai wasan barkwancin nan kuma mawallafiya, Rosie Wilby ta ce ta ci gaba da abota da tsohuwar masoyiyarta bayan rabuwarsu.

Ita da tsohuwar masoyiyarta mai suna Donna sun rabu ne bayan mutuwar mahaifiyarta, sannan gobara ta cinye mata komai a gidanta.

Ta ƙara da cewa sun rabu da juna ne kawai tsawon mako uku.

"Wannan lokacin kawai muka ɗauka, saboda dama mun saba da juna, don haka muna buƙatar juna,'' in ji ta.

Amma shekara 25 bayan rabuwarmu, yanzu ''Donna ta zame mini tamkar ƴar'uwa''.

4. Sabon saurayinki ba shi da matsala da hakan?

Idan har kun yanke shawarar ci gaba da hulɗar abota da tsohon saurayinki, yana da kyau ku sanar wa junanku yadda abotar taku za ta kasance, musamman idan ɗayanku ya fara wata soyayyar a gefe, ko ma ya yi aure, a cewar Kate.

Amma idan sabon saurayinki ko ma mijinku bai gamsu da hulɗarki da tsohon saurayinki ba, Kate ta ce yana da kyau ku haƙura.

“Wannan na da matuƙar muhimmanci, ko saboda tsaron aurenki,” in ji ta.

Olivia ta ce mata na ɗaukar tsohuwar budurwar mijinsu ko saurayinsu a matsayin babbar barazana a gare su, musamman idan ba ta yi aure ba.

'Cutarwa ke hana sake hulɗar masoya'

Kate ta ce idan ba a yi rabuwar mutunci ba, wataƙila ɗaya ya cutar da ɗaya, zai yi wahala a koma wata hulɗa bayan rabuwa.

“A wasu lokuta abubuwan da suka faru lokacin rabuwar masoya shi ke sa a rufe babin hulɗa tsakani,'' in ji Kate.

Ita kuwa Olivia cewa ta yi "ba zan iya sake hulɗa abota da mutumin d aya cutar da ni a a lokacin da muke soyayya ba.''

Ta ƙara da cewa ƙawayenta da dama sun yanke alaƙa da tsoffin samarinsu.