Babban birnin da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a cikinsa

Asalin hoton, Reuters
A birnin Port-au-Prince rayuwar al'umma na cikin ƙunci tare da hatsari.
Ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke gogayya da juna sun hana babban birnin Haiti zaman lafiya ta hanyar yin garkuwa da mutane, da aikata fyade, da kuma kisa.
Zubar da jinin mutane ya zama ba komai ba a wajen 'yan bindigar.
Domin kuwa matuƙar ka shiga yankin da ɗaya ɓangaren ke iko da shi to ba lallai ne ka iya fita da ranka ba.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na ƙasar sun ce masu ɗauke da makamai na riƙe da iko tare da addabar akalla kashi 60 cikin 100 na babban birinin ƙasar da kewayenta.
Sun kewaye birnin, inda suke riƙe da ikon titunan ciki da wajen birnin.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce 'yan bindigar sun kashe akalla mutum 1,000 tsakanin watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara.
Babu shugaba a ƙasar (an kashe wanda yake kan mulki), babu majalisar dokoki, kuma Firaministan ƙasar Ariel Henry, mai samun goyon bayan Amurka ba zaɓarsa a ka yi ba, kuma ba fitacce ba ne sosai a ƙasar.
Mutanen ƙasar na fama da matsalolin rikice-rikice.
Kusan rabin al'ummar ƙasar miliyan 4.7 na fama da matsananciyar yunwa.
A babban birnin kusan mutum 20,000 ne ke fama da matsalar yunwa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
cutar amai da gudawa ta kashe mutane masu yawa sakamon ayyukan 'yan bindigar.
Akwai lokaci na musamman da 'yan bindigar ke fita domin kame mutane, sa'o'in da suke yawan kama mutane su ne sa'o'in da mutane ke fita wuraren sana'o'insu da safe, daga ƙarfe 6:00 zuwa 9:00 na safe.
Akan kama mutane da yawa a kan hanyoyinsu na zuwa aiki, wasu kuma da yamma ake kama su a lokacin da suke kan hanyar komawa gida tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 6:00 na yamma.
Wajen ma'aikata 50 ne ke zaune a wani otal saboda suna tsoron tafiya gidajensu, domin kuwa ƙalilan ne ke iya zirga-zirga a birnin da zarar maraice ta kawo jiki.
Garkuwa da mutane
Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da ƙaruwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban wannan shekara an samu rahotonnin sace mutane kusan 1,107.
Ga wasu 'yan bindigar, sace mutanen ya zame musu babbar hanyar samun kuɗin shiga.
Akan biya kuɗin fansa tsakanin dala 200 zuwa dala miliyan ɗaya.
Akan sako waɗanda aka kama idan iyalansu sun biya kuɗin fansa bayan sun sha baƙar wahala.
Dukan maza tare da yi wa mata fyade
Gedeon Jean na cibiyar bincike na hukumar kare hakkin ɗan adam ya ce akan daki maza tare da ƙona su da ruɓaɓɓun robobi.
Yayin da mata ƙananan yara ke fuskantar fyaɗe. Wannan hali kan jefa 'yan uwa cikin mawuyacin halin neman kuɗin fansar da za su karɓo 'yan uwansu.
A wasu lokuta masu garkuwar kan kira 'yan uwa matan a waya a lokacin da suke tsaka da yi musu fyaden.
'Yan sanda sun shaida mana cewa sun yi artabu da masu garkuwa da mutanen a lokacin da suka yi yunƙurin sace wani mutum.
'Yan bindigar sun gudu da ƙafafunsu ɗaya daga cikinsu ɗauke da muggan raunuka.
Wani kwararren ɗan sanda wanda bai yadda a ambaci sunansa ba ya ce sun yi musayar wuta da 'yan bindigar, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu.
Ya ce birnin bai taɓa fuskantar dagulewa kamar wannan ba.

A cikin garin a wannan safiyar Francois Sinclair wani ɗan kasuwa mai shekara 42, ya ji ƙarar bindiga a yayin da yake maƙale cikin cunkoson ababen hawa.
Ya ga mutane ɗauke da makamai cikin motoci biyu da ke gabansa, dan haka ya shaida wa direbansa cewa da ya juya cikin sauri. To amma a ƙoƙarinsu na juyawa, sai aka tsayar da su.

"Kafin na ankara sai naji harbi a jikina, kuma nan da nan jini ya watsu ko'ina cikin motata'' kamar yadda ya shaida mana a lokacin da yake zaune kan gadon asibin ƙungiyar likotoci ta Duniya 'Medicins Sans Frontieres' (MSF).
"Sun harbe ni a kafaɗa, kuma ba ni kaɗai ba ne a cikin motar'' ya faɗa a yayin da bandeji ke naɗe a hannunsa.
Da aka tambaye shi ko ya taɓa tunanin barin garin domin gujewa rikicin? Sai ya amsa da cewa ''fiye da sau dubu''
''Ban ma samu damar kiran mahaifiyata a waya domin shaida mata abin da ya faru da ni ba, saboda ta tsufa. Yadda abubuwa suke a nan gwara ka fice daga ƙasar idan ka samu dama, to amma mutane da dama ba su da inda za su je.

Dakunan kwanciyar marasa lafiya na asibitin cike yake da mutanen da harbin bindiga ya raunata.
Claudette, wadda ke da sabon bandeji a ƙafarta ta hagu ta shaida mana cewa yanzu ba za ta taɓa yin aure ba tun da ta zama nakasasshiya.
Kwance kusa da ita Lelianne ce wata yarinya ce mai shekara 15 wadda aka harba a cikinta.
"Mun fita ni da mahaifiyata domin neman abin da za mu ci, a lokacin da muke tsaka da tafiya sai naji wani abu, a lokacin ne na faɗi ƙasa na fita daga hayyacina, ban ma sake sanin abin da ke faruwa ba, sai ganina na yi a asibiti'' in ji Lelianne.
'Yan bindiga ne ke iko da birnin
A lokacin da Jean Simson Desanclos ya isa unguwarsu a yankin da ke ƙarƙashin 'yan bindigar, bai tarar da kowa daga cikin iyalansa ba, sai wata motar gidan nasu wadda ya tarar da ita a ƙone.
An kai ƙonannun gawarwakin matarsa da na 'ya'yansa biyu zuwa mutuware.

Matar tasa Josette Fils Desanclos, mai shekara 56, ta ɗauki 'ya'yan nata biyu a mota inda za ta kai ɗayar Sarhadjie, mai shekara 24 makaranta, tare da kai ɗayar mai suna Sherwood Sondje, shagon sayayya a shirye-shiryen bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta, a lokacin da take gab da cika shekara 29 a duniya.
Duka 'yan matan kamar mahaifin nasu sun karanci fannin shari'a a jami'a, kuma su ne kaɗai magadansa.
"Ranar 20 ga watan Agusta na rasa komai nawa, ba iyalaina kaɗai aka kashe ba, a wannan rana kusan mutum takwas aka kashe, wannan kisan kiyashi ne'', in ji shi.

Gwamnatin ƙasar Haiti dai na kiraye-kiraye ga hukumomi da ƙasashen duniya da su taimaka mata wajen dawo zaman lafiya a ƙasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta tattauna game da buƙatar kai sojojin da ba nata ba, to sai dai babu wata ƙasa da ta bayyana ra'ayin jagoranta, ko bayar da gudunmowar sojojinta.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce ƙungiyoyin 'yan bindigar na faɗaɗa ikonsu saboda yadda aka kasa gudanar da zaɓe a ƙasar.











