Hatsari kan hatsari: Yadda matan Gaza ke haihuwa a tagayyare

Aya al-Skafi zaune tana kallon kyamara idonta cike da ƙwalla, sanye da baƙaƙen tufafi da hijabi.
Bayanan hoto, Ƴar Aya al-Skafi, Jenan, ta mutu wata tara bayan haihuwarta saboda likitoci sun kasa samar mata abin da take buƙata.
    • Marubuci, Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
    • Marubuci, Callum Tulley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 7

Duka irin mummunan yaƙin da ke faruwa a Gaza, akan samu haihuwa. To amma sabbin jariran da kuma ƴantayin da har yanzu ke cikin mahaifa na daga cikin waɗanda suka fi shan wahalar yaƙin.

Yayin da ake amun ƙarancin abinci, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kowane ɗaya cikin jarirai 10 da aka haifa ba su kai nauuyin da ake buƙata ba, ko ma ba su isa haihuwar ba.

Haka kuma akwai ƙaruwar ɓarin ciki ko haihuwar jariran babu rai da kuma matsalolin lafiyar jarirai.

A asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza, Malak Brees, wadda a yanzu ke ɗauke da cikin wata bakwai, tana cikin farbagar harin Isra'ila ko umarnin ficewa daga asibitin ko ma rasa jaririnta.

"Ina fargabar haihuwar jaririn da bai isa haihuwa ba a kowane lokaci daga yanzu, saboda ba ni da wadattaccen sinadarin amniotic da zai taimaka wa jaririna ya girma a cikina," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Malak ba ta sa rai da ƙara samun juna-biyu, saboda mako biyu da suka gabata sinadarin amniotic da ke cikinta ya zube da yawa, lamarin da ya ƙara jefa jaririnta cikin hatsari.

"Likitoci sun shaida min cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin abinci da wahala.... sun faɗa min cewa sai yadda Allah ya yi da jaririna, zai iya mutuwa ko ya rayu''.

Yayin da rashin abinci ke sanya masu juna-biyu cikin hatsari, haihuwar kanta na ƙara zama cikin hatsari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mako biyu da suka gabata ne Isra'ila ta fara sassauta dokar hana shigar da agaji Gaza da ta fara ranar 2 ga watan Maris - wanda ta ce tana yi domin matsa wa Hamast lamba.

Ana kuma samun ƙarancin magungunan da aka fi buƙata, ciki har da magungunan rage raɗaɗin ciwo da na tsabta.

A wasu lokutan ayyukan sojojin Isra'ila da raba mutane da gidajensu na sa mata da dama na haihuwa a tantunan ƴngudun hijira ko muhallan da babu magunguna.

''Idan mata sun yi sa'ar zuwa asibiti domin haihuwa, waɗanda suka haihu da kansu akan sallame su sa'a uku zuwa huɗu bayan haihuwa domin su koma gida,'' in ji Sandra killen wata ma'aikaciyar jinya da ke aiki da wata hukumar Amurka, wadda a baya-bayan nan ta yi aiki a asibitin a Gaza.

"Su kuwa matan da ka yi wa tiyata domin cre jariran, akan sallamesu kwana guda bayan yi musu aikin,'' in ji ta.

"Akan sallame su su tafi gida tare da jariransu da a wasu lokuta kan ɗauke da cutukan a halin zaman lafiya ya kamaya a ce sun zauna a asibiti domin samun taimakon likitoci.

"Mafi yawan jarirai a wajen Gaza, akan haife su ƙasa da mako 32, kuma ba su kai nauyin giram 1,400 (3.1lb), Ya kamata a ce suna sashen bayar da kulawa ta musamman , bai kamata a mayar da su gida ba, amma babu wuein ajiye su.''

Wani jariri Bafalasɗine kwance a agadon asibiti a ɗakin bayar da kulawar gaggawa a asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza (30 April 2025)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Asibitin Nasser ya kasance a cike tun bayan da harin Isra'ila ya dakatar da ayyuka a asibitin European

Asibitin Nasser na da sashen bayar da kulawar gaggawa ga jarirai, kuma a cike wurin yake.

Likitocin asibitin sun ce aiki ya yi musu yaa tun bayan da asibitin European da ke kusa ya daina aiki, sakamakon harin Isra'ila da aka kai ranar 13 ga watan Mayu.

Sojojin Isra'ila sun riƙa kai hare-hare kan asibitoci a tsawon wata 20 na yaƙin, inda suka ce suna kai harin ne kan shugaban Hamas na yankin, Mohammaed Sinwar, da ke ginin ƙarƙashin ƙasa da yake ƙasan ginin asibitin na European.

Haka kuma sojojin na Isra'ila na zargin Hamas da ɓoye mayaƙanta da kayan aikinta a wajen marasa lafiya da waɗanda suka jikkata, wani abu da ƙungiyar ta musanta.

Yayin da a yanzu samun ingantaccen kiwon lafiya ke da matuƙar wahala, da yawa cikin mutum 55,000 da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa suna da juna-biyu a Gaza ba za su iya samun kulawar likitoci a lokacin goyon ciki ba.

"Halin da mata ke tsintar kansu a lokacin haihuwa abu ne mai ban tausayi, Allah ya taimake su," in ji Dokta Ahmad al-Farra, shugaban kula da yara da mata masu juna biyu a asibitin Nasser.

"Suna da yaƙinin cewa jariran da ke cikinsu ba sa samun kulawar da ta dace, kuma su kansu ba sa samu isasshen abinci mai gina jiki, don haka suna sa ran jariran su fuskanci ƙarancin nauyi a lokacin haihuwa ko wasu matsaloli. Wannan ita ce damuwarsu ta farko."

"Matsala ta biyu ita ce bayan haihuwar, suna cikin matuƙar fargabar yadda za su shayar da jariransu, musamman halin da ake ciki na rashin abinci''.

Sandra Killen, ta ƙware wajen taimaka wa iyayen wajen shayar da jariransu

Asalin hoton, Sandra Killen

Bayanan hoto, Ma'aikaciyar jinya Sandra Killen ta ƙware wajen taimaka wa iyayen wajen shayar da jariransu.

Yayin da take share hawaye, Aya al-Skafi na kallon hoton ƴarta, Jenan a wani gini a birnin Gaza.

An haifi jaririyar ta hanyar tiyata a farkon wannan shekara, da fari tana cikin ƙoashin lafiya. Amma da abinci ya fara wahala, mahaifiyarta ta riƙa shan wahalar shayar da ita.

"Bayan hana shigar da agaji, komai namu ta tsaya,'' a cewar Aya.

"Babu fulawa, babu ruwa mai tsafta babu abinci kamar ƴaƴan itatuwa da ganyayyaki da ake buƙata domin ƙara lafiya. A lokacin da halin da nake ciki ya natsananta, ita ma Jenan nata ya ƙara tsananta."

Likitoci sun gano cewa Jenan na fama da matsalar rashin abincin da ruwa, sannan tana da matsalar narkar dsa abinci. Likitocin sun kasa samar mata da abin da take buƙata.

"Na shiga matsananciyar damuwa, har ta kai na ji kamar zan tsala ihu a duniya don nema wa yata taimako'', a cewar Aya.

"Na nemi taimako, amma Allah ne kawai ya amsa, ɗauke ranta da aka yi ne karhsne ciwon.''

A watan da ya gabata ne Jenan ta mutu - bayan wata huɗu da haihuwarta.

Wata Bafalasɗiniya ɗauke da jarirai uku bayan sun tsere daga asibitin al-Shifa a birnin Gaza, ranar 21 ga watan Maris ɗin 2024

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara 18 ne rabin al'ummar Gaza miliyan 2.1

Iyaye da dama na fama da wahalar shayarwa saboda halin da lafiyarsu ke ciki, amma wata ƙungiyar mai mazauni a Scotland mai suna 'Gaza Infant Nutrition Alliance', ta riƙa bai wa likitoci horon yadda za su taimaka.

Nurse Sandra Killen, wadda ta ƙware wajen hada madarar jarirai tana aiki tare da ƙungiyar.

"Muna ba da shawarar shayar da jarirai, ko da a lokacin da iyaye mata ke fama da rashin abinci mai gina jiki sai dai idan suna fama da rashin abinci mai gina jiki," in ji ta.

"Sau da yawa iyaye mata da aka ba su madara, sukan dogara da shi, nonon su yana raguwa sannan ba su da damar yin amfani da madara, ko kuma ba su da ruwa mai tsabta."

Yanzu ta koma gida a Amurka, Sandra ta ba da labarin wasu abubuwan ban tausayi da ta fuskanta a Khan Younis da kuma a asibitin shahidan al-Aqsa da ke tsakiyar garin Deir al-Balah.

Wata da ta taɓa haihuwa a karon farko ta ziyarci asibiti kafin ta haihu, amma harin da Isra'ila ta kai ta sama ya sa ta haifi jaririnta ita kaɗai tare da mijinta a sansaninsu.

Kwanaki biyar tana fama da wahalar shayar da jaririnta. Lokacin da aka tashi lafiya zuwa asibiti, lokaci ya yi da za a ceci jaririnta.

Jomana Arafa kwance a gadon asibiti bayan ta haifi tagwaye.

Asalin hoton, Family handout

Bayanan hoto, An ɗauki wata mata tare da jariranta biyu tagwaye kwana uku kafin kashe su a wani harin Isra'ila.

Tallafa wa iyala na daga cikin al'adun al'ummar Gaza, amma a sansanonin 'yan gudun hijira, yawancin mata ba sa samun tallafin da suka saba samu daga 'yan uwa da abokan arziki yayin da suke da juna da kuma bayan ahihuwa.

Yayin da ta yi aiki har sau biyu a Gaza a shekarar da ta gabata, Sandra tana ba da shawarwari ga mata daga nesa. Ta kasance kusa da wata mai sayar da magunguna, Jomana Arafa, a lokacin da take da ciki da tagwaye.

"Na haihu ta hanyar titaya, kuma alhamdulillahi, ni da jariraina muna cikin koshin lafiya," in ji Jomana a cikin sakon murya da turanci wanda ta aika da hotuna a watan Agustan da ya gabata. Ta sanya wa tagwayen (Namiji da mace) sunaye Asser da Aysal.

Amma farin cikin Jomana da iyalinta ya kasance na ɗan gajeren lokaci.

Bayan kwana uku, mijinta, Mohamed Abul-Qomasan, yana ƙoƙarin karɓo wa tagwayen takardun haihuwa, sai ya samu labarin cewa an kashe matarsa, da jariran da kuma surukarsa, a wani harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai a sansaninsu da ke Deir al-Balah.

'Yan jarida a asibitin shahidan al-Aqsa sun ɗauki hoton Mohamed a lokacin da ya faɗi a tsakar ginin asbitin.

A lokacin rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta da masaniya kan lamarin, inda ta ƙara da cewa ta ɗauki "matakan soji ne kawai", tare da ɗaukar matakan takaita cutar da fararen hula.

Ga Sandra, mutuwar Jomana, mahaifiyarta da sababbin jarirai "ya kasance mai ban tsoro fiye raɗaɗi". "Har yanzu ina tunanin hakan, kuma ina kuka," in ji ta.

A Gaza, ga mafi yawan mata, juna-biyu da haihuwa sun kasance lokaci na ɗokin jira da jin daɗi amma yanzu lokaci ne na damuwa da tsoro.

Maimakon fatan begen sabuwar rayuwa, jarirai tamkar na zuwa ne domin ɗanɗana raɗaɗin rayuwa.