Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Edo: Shin PDP za ta riƙe kambinta ko APC za ta ƙwace?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar Asabar 21 ga watan Satumba ne za a fafata zaɓen gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya, wanda ake ganin yaƙi ne tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da tsohon Gwamna Adams Oshiomole.
Su biyun ba su cikin 'yan takara, amma sun tsayar da ƴan takara da suke son ganin sun tabbatar da nasararsu.
Za a fafata zaɓen tsakanin jam'iyyu da dama, amma hankali ya fi komawa kan manyan jam'iyyun, inda APC ta tsayar da Monday Okpebholo, PDP kuma ta tsayar da Asuerinme Ighodalo.
Sai kuma Jam'iyyar Labour da Olumide Osaigbovo Akpata ke yi mata takara.
Alaƙar Oshiomole da Obaseki
A zaɓen shekarar 2016, Adamas Oshiomole mai barin gado ya dage kai da fata domin ganin Obasaki ya maye gurbinsa, duk da a lokacin mataimakinsa Pius Odubu yana neman kujerar.
Bayan zaɓen fitar da ɗan takara, inda Obaseki ya doke Odubu, Oshimole ne ya jagoranci tallata shi a ƙananan hukumomin jihar, har aka gwabza zaɓe kuma Obasaki ya doke Fasto Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar PDP a lokacin.
Sai dai ana tsaka da mulkin na Obaseki ne aka fara musayar yawu tsakanin mgaoya bayan Oshiomole da na Obaseki, inda suka zargi gwamnan da ware su.
Komawar Obaseki PDP
Lokacin da zaɓen gwamna na shekarar 2020 ya ƙarato, Oshiomole da Obaseki sun wasa wuƙarsa.
A lokacin Obaseki na neman zangon mulki na biyu ne a Jam’iyyar APC. Amma sai Oshimole ya samu nasara a kansa, inda APC ta cire Obasekin tun a zaɓen cikin gida, kuma ta tsayar da Fasto Ize-Iyamu, wanda Obaseki ya kayar bayan shi ma ya dawo APCn daga PDP.
Hakan ya sa shi ma Obaseki ya ruga wajen PDP domin neman mafaka, inda suka ba shi lema kuma ya yi takara a ƙarƙashinta.
Takarar da Obaseki ya samu a PDP ta ƙara ta’azzara saɓani tsakanin Obaseki da Oshiomole, inda PDP ta riƙa yaƙin zaɓe da taken ‘Edo ba Legas ba ce,”.
Da aka fafata zaɓen ne Obaseki ya samu nasara a karo na biyu bayan kayar da Ize-Iyamu a karo na biyu.
Zaɓen bana
Kasancewar Obaseki yana ƙarƙare zangon mulkinsa na biyu, shi ma ya tsayar da ɗan takarar da yake so ya maye gurbinsa, yayin da shi ma Oshiomole ke da nasa ɗan takarar.
Oshiomole ne yake jagorantar kamfe na ɗan takarar APC Monday Okpebholo, shi kuma Obaseki ke jagorantar yaƙin zaɓen ɗan takarar PDP wato Asue Ighodalo.
A wani ɓangaren kuma, mataimakin Obaseki, wato Philip Shaibu wanda kotu ta mayar da shi bayan an tsige shi, suna cikin rikici mai zafi da gwamnan.
Kabiru Said Sufi, malamin kimiyyar siyasa ne a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma ya ce lallai zaɓen zai yi zafi sosai.
“Akwai yiwuwar zaɓen ya kasance duk wanda ya samu nasara ba zai bayar da tazara sosai ba saboda kowane ɗan takarar manyan jam’iyyun biyu na da abubuwan da yake ganin suna ƙarfafa masa gwiwar samun nasara," in ji shi.
"PDP na ganin ita ta yi mulkin jihar na wasu shekaru da suka gabata, saboda haka suke ganin kamar wannan zai iya ƙara musu ƙarfin gwiwa. Ita ma APC tana ganin wannan a matsayin ƙarfinta saboda tana cewa ai PDP ɗin da ta yi mulki akwai naƙasu musamman saboda rikicin cikin gida tsakanin Gwamna Obaseki da mataimakinsa Philip Shuaibu.”
Masanin siyasar ya ƙara da cewa akwai wasu abubuwa da za su taka rawa a zaɓen.
"Misali, PDP tana ganin ɗan takarar APC bai cancanta ba musamman ganin ba shi da karatu mai zurfi, har suke ta kiraye-kirayen ya zo a yi muhawara a harshen Ingilishi, amma ita APC ta ce wannan ba shi ba ne sanin makamar aiki."
Malam Sufi ya ƙara da cewa zaɓen ya ƙara ɗaukar zafi ne bayan kamfe ya yi nisa, inda a cewarsa suka riƙa sukar juna har ta kai suna taɓa iyalansu da sauran wasu abubuwan da ba su da alaƙa da siyasa.
"Amma duk da haka kowane ɓangare bai yi wasa ba wajen neman ƙuri'a," in ji shi, "kowane ɓangare ya bi jama'a kuma ya tallata ɗan takararsa".
Game ko kasancewar jam'iyyar APC ce take mulki a sama, inda ake tunanin ko za ta saka hannu a zaɓen, Malam Sufi ya ce "su kansu ƴan APC ɗin ba su cika bayyana cewa suna da saman ba".
"Duk da dai a baya-bayan nan ziyarar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya kai Edo ta nuna cewa ba a bar su haka nan ba, duk da haka su a jihar ba su cika nuna cewa sama za ta ƙwace musu ba, wataƙila saboda sanin yadda yanayin zaɓe na jiha yake shi ya sa ba su cika tutiya ba.
"Shi ya sa suke ta kamfe cewa da ƙyar aka ƙwace musu jihar, yanzu kuma sun dawo da ƙarfinsu kuma suna da sanatoci."
Kabiru Sufi ya aminta cewa jiƙaƙƙiyar da ke tsakanin Obaseki da Oshiomole za ta iya yin tasiri a zaɓen.
"Lallai hakan zai iya yin tasiri musamman duba da cewa ana amfani hakan wajen nuna raunin ɗan takarar APC da Oshiomole ya yatsar.
"Suna nuna cewa idan da Oshiomole ba so yake ya ci gaba da mulki ba, ko a cikin jam’iyyar tasa akwai wanda ake ganin ya fi Okpebholo. Suna ta ƙoƙarin nuna wa mutanen jihar cewa wanda aka tsayar yana da rauni sosai."