Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Edo: Tasirin zaben kaɗaici ga tsarin dimokradiyyar Najeriya
Bisa al'ada a Najeriya akan hada zaben shugaban kasa ne da na gwamnoni a lokaci guda, sai dai akwai wasu jihohi shida, wadanda ba sa bin wannan tsari na zaɓe gama-gari, ciki har da jihar Edo da ake sa ran za a yi zaben gwamna a ranar Asabar mai zuwa.
Jihohi shida ne a Najeriya suka zama ƙi-taro, wadanda ba sa tafiya da sauran jihohin kasar 30 a lokutun da ake babban zaɓe.
Wato zaɓen da ake hada na shugaban kasa da gwamnoni da kuma 'yan majalisar dokoki. Kuma daga cikin guda shidan, jihar Kogi da takwararta ta Bayelsa ne 'yan tagwaye wadanda ke hada biki.
Abin nufi akan yi zaben gwamnoninsu ne a lokaci guda. Amma ragowar huɗun, wato da jihar Ekiti, da Anambra, da Edo da kuma Ondo kowacce da ranarta.
Mista Nick Dazang shi ne daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na hukumar zaben Najeriya, wanda ya ce bai-daya ake zaben a dukkan jihohin Najeriya 36 a farkon komawar kasar ga turbar demokuradiyya, amma daga bisani shari'a ta raba.
"Da Kogi, da Bayelsa, da Anambra, Ondo, da nan Edo da kuma Ekiti, a baya idan an tuna kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci cewa gwamnonin jihohin shida za su riƙa kammala wa'adin mulkinsu a lokaci da ya sha bamban da sauran jihohin ƙasar nan."
'Karon farko da zan yi zabe ke nan'
Ga wasu mazauna waɗannan jihohi, kewa kan rufe su a duk lokacin da ake gudanar da babban zabe, inda ala tilas ake taƙaita musu kaɗa ƙuri'a ga zaɓen shugaban kasa da ƴan majalisun dokokin tarayya.
Sukan yi zaben gwamna daga baya, kamar yadda al'ummar jihar Edo za su yi a ranar Asabar mai zuwa.
Wasu daga cikin jama'ar jihar sun bayyana cewa suna Allah-Allah Asabar ta zo, ciki har da wani matashi da zai yi zaɓe a karon farko, wanda ya ce jinkirta zaben abin nan ne da 'yan magana kan ce wani hanin ga Allah baiwa ne, saboda ya ba shi damar cika shekarun kada kuri'a.
"Gaskiya wannan shi ne karo na farko da zan yi zaɓe, kuma ina godiya ga Allah da ya ba ni damar ganin wannan rana."
Irin wannan zabe na kadaici kamar yadda masana da masu lura da al'amura ke cewa, yakan bai wa mahukunta damar yin kyakkyawan shiri ga zaben, musamman ma tanadin isassun jami'an tsaro don samar da kariya.
Amma kuma wasu na zargin cewa ba a nan gizo ke saƙar ba, saboda yawan jami'an tsaron bai hana tashin hankali a jihohin Kogi da Bayelsa ba a zaben gwamnan da aka yi a watan Nuwamban bara.
Wasu ma na zargin cewa raba zaben kan bai wa masu mulki damar amfani da ƙarfi wajen tanƙwara shi yadda suke so, amma suna musanta wannan zargin.