Abin da ya sa Amurka ta hana wasu 'yan siyasar Najeriya biza

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamantin Amurka ta bayyana dalilan da suka sanya ta hana wasu fitattun 'yan siyasar Najeriya takardar izinin shiga kasar saboda zargin da take yi musu na keta dokokin zabe.

A sanarwar da ta fitar, gwamnatin Amurka ba ta bayyana sunayen 'yan siyasar ba sai dai ta ce suna cikin mutanen da ke karan-tsaye a harkokin zaben kasar.

Hakan na faruwa ne kwanaki kadan kafin gudanar da zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo da ke kudancin kasar, wanda ke cike da zaman ɗar-ɗar.

Amurka ta yi zargin cewa 'yan siyasar na da hannu a rikicin zaben da aka yi a jihohin Bayelsa da Kogi a watan Nuwamba na 2019.

Hana 'yan siyasar biza na nufin ba za a bar su su shiga Amurka ba.

Neman lafiya

'Yan siyasar Najeriya na yawan zuwa Amurka musamma domin a duba lafiyarsu.

Wani kakakin gwamnatin Amurka Morgan Ortagus ta ce hana 'yan siyasar Najeriya biza wata alama ce da ke nuna cewa Amurka ba za ta bar irin wadannan mutane su rika hana ruwa gudu wajen tabbatar da dimokradiyya a kasar ba.

"Mun yi Allah-wadai da tarzoma da barazana da kuma cin hanci da suka illata tsarin dimokradiyyar Najeriya.

''A yayin da zabukan Edo da Ondo suke gabatowa, muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar zabe mai zaman kanta, jam'iyyun siyasa, da jami'an tsaro su tabbatar da tsarin dimokradiyya sannan su gudanar da zabe sahihi," in ji sanarwar da Ortagus ta fitar.

Masana harkokin siyasa irin su Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja sun ce matakin yana da kyawu wajen inganta mulkin dimokradiyya.

"Wannan mataki da Amurka ta dauka na martani ne, a wani bangaren kuma na nuna rashin jin dadinta game da tabarbarewar harkokin zabe a Najeriya inda manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa kan yi karan-tsaye ga harkokin zabe musamman ma magudi da murdiya," a cewar Dr Kari.

Ya kara da cewa hakan wani koma-baya ne ga 'yan siyasar Najeriya wadanda suke "matukar sha'awar zuwa Amurka".

Sai dai ya ce hakan ba zai hana wasu 'yan siyasar kasar yin magudin zabe ba ganin cewa hakan ya zama jiki a gare su kuma za su iya cewa "sun sha zuwa Amurka a baya" don haka ba matsala idan aka hana su shiga a yanzu.

Ba wannan ne karon farko da Amurka take hana wasu 'yan siyasar Najeriya takardar izinin shiga kasar ba.

A wata Yulin 2019, Amurka ta hana wasu 'yan siyasar kasar wadanda suka zarga da magudin zabukan shugaban kasa da na gwamnoni a watan Fabrairu da Maris na 2019.