Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lai Mohammed ya gamu da fushin masu amfani da shafukan zumunta
Ministan labaran Najeriya Lai Mohammed ya tayar da kura a shafukan sada zumuntar kasar sakamakon sanarwar da ya fitar cewa da a ce Muhammadu Buhari bai zama shugaban kasar ba da tuni Najeriya ta durkushe.
Sanarwar da ofishin Lai Mohammed ya fitar ranar Lahadi ta bayyana cewa: "Zaman Muhammadu Buhari shugaban kasa a shekarar 2015 ne ya hana Najeriya durkushewa bayan an shafe tsawon lokaci ana shugabanci maras alkibla."
Ministan ya ce Shugaba Buhari ya karbi jagorancin kasar ne a lokacin da "aka mamaye yankuna da dama, a lokacin da garuruwa da biranen Najeriya da dama, ciki har da Abuja, suka zama filin wasa ga 'yan ta'adda kuma a lokacin aka sace arzikin kasar..."
Sai dai tun daga lokacin da aka fitar da wannan sanarwa 'yan kasar musamman a shafin Twitter suke bayyana ra'ayoyinsu a kansu inda galibi suke sukar ministan kan kare gwamnati duk da abin da suka kira gazawar gwamnatin Shugaba Buhari.
Wani mai amfani da Twitter, Daniel Tariwe, ya bayyana cewa Lai Mohammed zai kare gwamnatinsu kodayaushe duk da cewa ta gaza saboda yana cikin wadanda suka gaza.
Sai dai wasu na ganin kalaman Lai Mohammed wata hikima ce ta "janye hankalin 'yan kasar daga tunanin mawuyacin halin da suke ciki."
'Yan Najeriya sun kwashe makonnin baya bayan nan suna caccakar Shugaba Buhari sakamakon karin farashin man fetur da hasken wutar lantarki da tsadar rayuwar, abin da ya sa wani mai amfani da Twitter ya ce kalaman ministan za su iya janye hankulan 'yan kasar daga gare su.
Ya ce: "Idan gwamnatin nan tana son janye hankalin talakawa, sai kawai ta gaya wa Lai Mohammed ya fitar da sanarwa. Daga baya kowa zai yi mamaki."
Shi ma Esmart cewa ya yi Shugaba Buhari "bai hana Najeriya durkushewa ba, ya taimaka wajen durkushewarta. Najeriya ta durkushe a karkashin jagorancin Buhari."
Sai dai wasu da dama sun yarda da kalaman Lai Mohammed suna masu cewa Shugaba Buhari ya hana kasar wargajewar.
Mustapha Musa na cikinsu inda ya ce: "Da dai kam yanzu wasun mu 'yan gudun hijira ne a Nijar, Chadi da Kamaru."
Shi ma Rayhan ya ce: "Haka yake da bai hau mulki ba da talakawa sun tayar da yakin basasa a Najeriya. Saboda sun ce shi ne kadai ya rage mai gaskiya."
A makonnin baya bayan nan jami'an gwamnatin kasar na shan suka bisa wasu kalamansu inda ko a makon jiya ma kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta bayan ya ce an taba sayar da litar man fetur kan naira 600 a shekarar 2013.