Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Trump ya dakatar da shirin Isra'ila na kashe Ayatollah
- Marubuci, Seher Asaf
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaban Amurka ya ƙi amincewa da shirin Isra'ila na kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda majiyoyi uku suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS News, abokiyar hulɗar BBC.
Rahotanni sun ce Shugaba Trump ya shaida wa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa kashe Khamenie "ba shawara ce mai kyau ba." Trump bai fito fili ya yi magana kan batun ba.
Tattaunawar ta faru ne bayan harin da Isra'ila ta ƙaddamar kan Iran a ranar Juma'a."
A lokacin wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Netanyahu bai fayyace kai-tsaye ko Trump ya ƙi amincewa da shawarar kashe Ayatollah ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
"Akwai rahotannin da dama kan tattaunawar da ake cewa an yi amma kuma ba gaskiya ba ne, ba zan shiga cikin irin wannan maganar ba," in ji Firaiminstan Isra'ila.
"Amma zan iya shaida muku cewa ina ganin mun yi abin da ya kamata. Za mu yi abin da ya dace kuma ina tunanin Amurka na sane da abin da ya dace gare ta, amma ba na son na shiga cikin wannan batun."
Wani jami'in Isra'ila ya shaida wa CBS News cewa "a ƙa'idance" Isra'ila ba ta kashe "shugabannin siyasa, muna mayar da hankali ne kan nukiliya da kuma sojoji. Ba na tunanin ya kamata a bar duk wanda ke yanke hukunci kan waɗannan abubuwa ya shaƙata."
A ranar Juma'a ne Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin nukiliya da ma wasu wurare a Iran. Tun daga lokacin ne ƙasashen biyu suka ci gaba da musayar wuta tsakaninsu, inda aka shafe dare na uku ana irin haka.
A wani bayani da ya wallafa ta shafinsa na sada zumunta - Truth - kan rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, Trump ya ce "Ya kamata Iran da Isra'ila su cimma matsaya", ya kara da cewa zai yi koƙarin ganin ɓangarorin biyu sun tsagaita wuta, "kamar yadda na yi tsakanin Pakistan da Indiya" - inda yake nuni da rikicin da ya faru tsakanin ƙasashen biyu a baya-bayan nan.
Lokacin da ya tattauna da manema labarai kafin yin balaguro zuwa ƙasar Canada domin taron ƙashen duniya bakwai mafiya ƙarfin arziƙi (G7), Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tallafa wa Isra'ila sannan ya ki cewa komai kan ko Amurkar ta buƙaci Isra'ila ta daina kai wa Iran hari.
A baya an tsara ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar taƙaita ayyukan nukiliyar Iran tsakanin ƙasar da Amurka ne a ranar Lahadi, sai dai an sanar da soke tattaunawar kwana ɗaya gabanin ranar da aka tsara.
Iran ta shaida wa Qatar da Oman cewa ba za ta yi wata tattaunawa ba yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai mata hare-hare, kamar yadda wani jami'i ya bayyana wa kafar dillancin labarai ta Reuters a ranar Lahadi.
Shugaba Trump, a ranar Asabar ya ce "babu abin da ya haɗa Amurka da harin da ake kai wa Iran".
"Idan kuma Iran ta kai mana hari ta kowane irin yanayi, za mu yi amfani da dukkanin ƙarfin sojin Amurka a kanta yadda ba a taɓa gani ba a tarihi,' kamar yadda ya ce.