Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane mataki Iran ta kai wajen ƙera makaman nukiliya?
- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Isra'ila ta kai wa gomman wurare hari a fadin Iran, ta lalata cibiyar samar da sinadarin Uranium a Natanz tare da kashe kwamandojin soji da wani ƙwararren masanin kimiyya a Tehran.
Bayan kashin farko na hare-hare a daren Alhamis, ministan harkokin wajen Iran ya yi Allah-wadai da abin da ya kira harin ganganci na Isra'ila a cibiyar makaman nukiliyar ƙasarsa. Tuni Iran ta mayar da harin martani Isra'ila.
Abbas Araghchi ya ce Natanz na aiki ƙarƙashin kulawar hukumar da ke sa ido kan makaman nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya (IAEA), sannan kai wa cibiyar hari zai iya haifar da masifa.
Firaiminista Benjamen Netanyahu ya ce Isra'ila ta dauki matakin ne saboda idan ba a dakatar da Iran ba, to za ta ƙirƙiri makaman nukiliya nan ba da jimawa ba.
''Zai iya kasancewa cikin shekara ko watanni,'' kamar yadda ya yi gargadi.
Ko akwai tabbas cewar Iran na ƙirƙirar makaman nukiliya?
Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta tattara bayanan sirri da suka tabbatar mata cewar Iran na shirya samar da sinadaran hada makaman nukiliya.
Kelsey Davenport, shugabar wata ƙungiya mai kula da al'amuran da suka shafi bazuwar makamai mai cibiya a Amurka ta ce Firaministan Isra'ila bai bayar da gamsasshiyar hujjar da za ta tabbatar da cewar Iran za ta ƙirƙiri makaman nukiliya ba.
Ta ce wasu ayyukan Iran game da makaman nukiliya za a yi amfani da su wajen ƙirkirar bama-bamai.
Binciken da hukumomin leken asirin Amurka suka gudanar ya nuna Iran ba ta shirin komai game da kirkirar makaman nukiliya.
A watan Maris din da ya gabata shugaban hukumar leken asiri Tulsi Gabbard ya shaida wa majalisa cewar sinadarin uranium da Iran ke da shi ya kai wani matsayin da bai dace da kasar da ba ta da makaman nukiliya ba.
Ta kara da cewar hukumar leken asirin Amurka ta ci gaba da tabbatar da cewar Iran ba ta da makaman nukiliya kuma jagoran Addini Ayatollah Ali Khamenei bai bayar da umarnin a ci gaba da shirin makaman nukiliyar da ya dakatar a shekara ta 2003 ba.
''Idan Netanyahu ya yi amfani da tsoron bazuwar makaman Iran ne, da sai Isra'ila ta sanar wa hukumar leken asirin Amurka, sai a kai wa cibiyoyin hada makaman nukiliyar Iran gaba daya harin,'' in ji Ms Davenport.
A makon da ya gabata ne hukumar da ke sanya ido kan makamai ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton da ya ce Iran ta tattara sinadarin Uranium da ya kai kashi 60 cikin dari - takaitaccen adadi ya rage ya iya samar da makaman nukiliya 9, don haka akwai fargaba idan aka yi la'akari da cewar za su iya bazuwa.
Hukumar ta kara da cewar ba za ta iya tabbatar da cewa tashin hankali ba zai biyo baya ba game da shirin makaman nukiliyar Iran din ba, saboda Iran ta ki bayar da hadin kai wajen binciken sinadarin Uranium din da aka yi a dakin gwaje-gwaje da ke wasu cibiyoyin nukiliya da ba ta bayyana su ba.
Abin da muka sani game da shirin makaman nukiliyar Iran
A kowanne lokaci Iran na jaddada cewar shirin makaman nukiliyarta na zaman lafiya ne, kuma ba ta taba neman kera makamin nukiliya ba
To amma shekaru 10 da suka gabata wani bincike da Hukumar IAEA ta yi ya gano Iran ta yi wasu ayyuka masu kama da kirkirar makaman nukiliya daga shekara ta 1980 zuwa shekara ta 2003, lokacin da aka dakatar da aikin mai suna ''Project Amad''.
Iran ta ci gaba da wasu shirye-shirye har zuwa shekara ta 2009-lokacin da kasashen yamma suka bankado cibiyar samar da sinadari ta Fordo, wadda ake ginawa a karkashin kasa-to amma bayan wannan ba a sake gano alamun kirkirar makaman nukiliya ba in ji hukumar.
A shekara ta 2015 Iran ta kulla yarjejeniya da wasu manyan kasashe 6 inda ta amince da ka'idojin akan shirinta na nukiliya, sannan ta bayar da dama jami'an hukumar IAEA suke sanya wa ayyukanta ido don ta samu saukin takunkumin da kasar ke fama da radadinsa.
Sai dai Shugaba Trump ya fice daga yarjejeniyar lokacin wa'adin mulkinsa na farko a shekara ta 2018, ya ce yarjejeniyar ba ta hana fitar bama-bamai ba daga nan kuma ya sake lafta wa kasar takunkumi.
Iran ta mayar da martani ta hanyar karya ka'idojin da aka sanya mata, musamman wadanda suka shafi sinadarin uranium.
Karkashin yarjejeniyar ba za a sake yin sinadarin uranium a Fordo ba tsawon shekaru 15.
Sai dai Iran ta koma aikin inganta uranium da kashi 20 cikin dari.
A ranar Alhamis ne shugabannin kasashe 35 na hukumar IAEA suka ayyana Iran a matsayin wadda ta karya ka'idar fid da makamai a karon farko cikin shekaru 20.
Iran ta ce za ta mayar da martanin matakin da aka dauka a kanta ta hanyar kafa sabuwar cibiyar sarrafa sinadarin Uranium a "wuri maitsaro" sannan za ta sanya na'urorin zamanin da za ta yi aiki da su a cibiyar sarrafa sinadarin uranium ta Fardo.
Wace irin lalatawa Isra'ila ta yi wa cibiyar makaman nukiliyar Iran?
A ranar Juma'a rundunar sojin Isra'ila ta ce harin farko ta sama ya lalata dakin da ke karkashin kasa na Natanz, mai kunshe da muhimman na'urorin da suke bayar da damar aikin.
Shugaban Hukumar IAEA Rafael Grossi, ya shaida wa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya cewar an lalata injin da ke samar wa cibiyar karkashin kasar mai an kuma lalata na'urorin da suke samar da hasken lantarki a Natanz.
Cibiyar Kimiyya da Tsaron kasa da kasa mai hedikwata a Amurka ta ce lalata PFEP na da matukar muhimmanci saboda an yi amfani da wurin wajen samar da sinadarin uranium har kashi 60 cikin dari.
Ms Davenport ta ce harin da aka kai wa Natanz zai hana Iran "ci gaba da shirinta na tsawon lokaci", amma a yanzu ba za a iya tantance irin koma-bayan da ta gamu da shi ba.
Daga baya ranar Juma'a, Iran ta sanar da hukumar ta IAEA cewa Isra'ila ta kai hari cibiyar sarrafa sinadarai da kuma cibiyar fasahar nukiliya ta Isfahan.
Sojojin Isra'ila sun ce wani hari da suka kai Isfahan ya "rushe sashen sarrafa sinadarin karfe uranium da na'urori da dakunan gwaje-gwaje.
"Matukar Fordo za ta ci gaba da aiki, Iran za ta zama barazana. Tehran na da zabin mayar da cibiyar sarrafa uranium wani boyayyen wuri" in ji Ms Davenport.
Shi ma Firaiministan Isra'ila ya bayyana cewar za su ci gaba da kai hare-hare har sai sun kawar da barazana.
To amma fa wannan buri ne mai wahalar cika in ji Ms Davenport.
"Hare-hare za su iya lalata cibiyar makamai, kaiwa masana kimiyya hari ba zai kankare fasahar nukiliya daga Iran ba.
Iran na iya sake gini cikin gaggawa musamman a yanzu don ta ci gaba da inganta sinadarin uranium'', kamar yadda ta kara bayyanawa.