Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi daga fitowa zuwa faɗuwar rana

Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ke cika kwana uku da rasuwa ranar Lahadi, BBC ta tattaunawa da iyalansa don jin irin rayuwar da ya dinga gudanarwa a kullum daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 shahararren malamin ya rasu a wani asibiti da ke Bauchi, kuma aka yi masa jana'iza a ranar Juma'a.

Dubban mutane suka halarci jana'izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima.

Fitowa zuwa faɗuwar rana

BBC ta tattauna da ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Naziru Dahiru Bauchi, wanda ya zayyana abubuwan da fitaccen malamin ya saba yi daga asubahi zuwa dare.

  • Raya dare: Kamar yadda ɗan marigayin ya tabbatar, Shiekh Dahiru Bauchi yana raya dare cikin ibada da bautar Allah. Malamin yana shafe dare wajen karatun Alƙur'ani mai girma da salloli da wurudi, musamman Salatul Fatihi. ''Ya faɗa wa babban yayanmu, Dr Hadi, ya ce masa ban san sau nawa na yi sallar asubahi da alwalar Isha ba,'' in ji Naziru Dahiru Bauchi.
  • Sallar Asubahi: Idan Asuba ta yi, Shiekh Dahiri Bauchi yana fita masallaci domin yin sallah, inda yake yin limanci tare da sauran ƴaƴa da almajirai da kuma sauran jama'ar gari.
  • Lazimi: Bayan kammala sallar asubahi, Shehin malamin yana zama ya yi lazimi sosai har zuwa lokacin da gari zai fara wayewa.
  • Sauraron labarai: Naziru Dahiru Bauchi ya ce idan ya kammala lazimi, babban malamin yana sauraron rediyo a kullum safiya domin shi mutum ne mai son sanin halin da ƙasa da kuma duniya ke ciki.
  • Gaisawa da baƙi: Bayan kammala jin labarai, malamin yana ware lokaci domin gaisawa da baƙi waɗanda suka sauka a gidansa da ma waɗanda suka sauka wani waje amma an yi sallar asubahi tare da su a gidan nasa.
  • Hutawa: Da hantsi kuma Shiekh yana komawa cikin gida domin samun bacci domin hutawa. Kafin ya kwanta ''a mafi yawan ranaku yana shan fura sannan ya kwanta bacci har zuwa ƙarfe 11 na safe.
  • Karin kumallo: Idan ya tashi daga bacci, marigayin yana yin karin kumallo, ya shirya sannan ya gana da mutanen cikin gida.
  • Zaman farfajiya: Bayan sallamar mutanen cikin gida, shehin malamin yana fita wata farfajiya da aka ware inda yake zaman karatu da kuma ganawa da baƙi da sauran almajiransa.
  • Azahar zuwa La'asar: Malamin ya kasance yana komawa cikin gida bayan sallar Zuhr, amma ba kowacce rana ba. Wasu ranakun yana zarcewa da harkokin karatu da karɓar baƙi har zuwa sallar Asr. Mafi yawan lokaci yana komawa cikin gida ne kamar ƙarfe 4:30 zuwa 5:00.
  • Bacci: Idan ya koma cikin gidan, shehin malamin yana sake kwantawa domin ya ɗan samu bacci har kusan faɗuwar rana.
  • Fita sallar Magariba: Idan ya tashi dab da faɗuwar rana, malamin yana sake shiri domin fita masallaci, inda yake limacin sallar Magriba.
  • Wazifar bayan Magariba: Malamin ya saba a duk bayan sallar magriba zai jagoranci wazifa da ake yi a cikin masallacinsa.
  • Karatun Alƙur'ani: A kullum marigayi Sheikh Dahiru Bauchi yana jagorantar karatun Alƙura'ni izu biyu a cikin masallaci, wato bayan an kammala wazifar da ake yi bayan sallar Magriba. Amma daga baya da shekaru suka ja, sai ya fara cewa a bar karatun izu biyun har sai bayan an yi sallar Isha'i tukun saboda masu uzuri.
  • Sallar Isha: Malamin yana limancin sallar Isha'i a masallacinsa, da kuma gudanarda addu'oi bayan sallar.
  • Lokacin iyali: Bayan sallar Isha'i ''Maulana bai cika ɓata lokaci a waje ba, yana komawa cikin gida domin samun lokaci tare da iyalinsa.'' in ji Naziru Dahiru Bauchi. A wannan lokaci ne kuma yake cin abincin dare. Zai ci gaba da kasancewa cikin gida tare da iyali har zuwa dare ya raba, inda zai tashi ya sake duƙufa ibada kamar dai yadda aka yi a daren da ya gabata.

Ranar Sheikh ta ƙarshe a rayuwarsa

Karatun Alkur'ani da ƙaunar manzon Allah

Naziru Dahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa daga cikin abubuwan da suka ɗauka a jerin ɗabi'un marigayi mahaifin nasu babu wanda suka fi riƙo da shi kamar karatun Alƙur'ani mai girma da kuma soyayyar manzon Allah.

Ya ce a iya sanin da suka yi wa mahaifinsu, ko hira ake yi a cikin gida, sai aka samu wata gaɓa da kowa ya yi shiru, to ''Maulana zai tashi ne da karatun Alƙur'ani.''

''Saboda da haka mun ɗauki wannan tarbiyya kuma mun yi riƙo da ita har abada.'' in ji Nasiru Dahiru Bauchi.

Ya kuma bayyana yadda mahaifin nasu ya sanya su a kan tafarkin soyayyar manzon Allah da yi masa salati a kowanne lokaci. Kamar yadda shi ma suka tashi suka same shi yana yi a koda yaushe.