Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa biyar da za a dinga tunawa da Sheikh Dahiru Bauchi
Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta girgiza mabiyansa a Najeriya da Afirka ta Yamma baki ɗaya, amma tabbas ba mutum ne da Musulmi za su manta da shi ba.
Shehin malamin da aka haifa a garin Nafada da ke jihar Gombe a watan Yunin 1927, ya shafe shekaru yana karantarwa bisa aƙidar ɗariƙar Tijjaniyya mai ɗumbin mabiya.
Da Asubahin ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba ne Allah ya yi masa rasuwa yana da shekara 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da ƴan watanni.
Garin Nafada, shi ne mahaifar mahaifiyarsa. Ya faɗa wa BBC cewa an haife shi ne a can "kasancewar a al'adar Fulani ana haihuwar ɗan fari a gidan su mahaifiyarsa".
An yi jana'izarsa a birnin Bauchi, kuma Sheikh Sherif Saleh ne ya jagoranci sallar jana'izar.
Cikin waɗanda suka halarci jana'izar har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashin Shettima, da sauran mabiyan malamin da msuka isa Bauchi daga sassan Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Wannan maƙala ta yi nazari kan wasu abubuwa da za a fi tunawa da jagoran.
Yin tafsirin Ƙur'ani da ka
Ɗaya daga cikin baiwar da Allah ya yi wa Sheikh Ɗahiru Bauchi ita ce yin tafsirin Ƙur'ani mai tsarki da ka ba tare da duba littafi ba.
Kodayake babu tabbas cewa shi kaɗai ne ke yin hakan, shi ne fitaccen malamin da aka sani da yin tafsiri da ka, kuma an sha jin sa yana alfahari da wannan baiwar da bakinsa.
Hakan yana ƙara tabbatar da irin kaifin haddar littafin mai tsarki da yake da shi, wadda kuma akasarin 'ya'yansa suka gada.
Yakan gudanar da karatun tafsirin a masallacinsa da ke Tudun Wada a ƙwaryar birnin Kaduna.
Makarantun haddar Ƙur'ani
Za a dinga tunawa da shehin malamin da makarantun koyarwa da haddar Ƙur'ani mai tsarki a faɗin Najeriya da maƙwabta.
Bayanai sun nuna cewa Gidauniyar Dahiru Bauchi na gudanar da ɗaruruwan waɗannan makarantu a Najeriya da wasu ƙasashe a yammacin Afirka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa makarantun haddar Ƙur'ani na gidauniyar sun yaye ɗalibai 140,924 tun bayan kafa su a azuzuwa fiye da 13,000 a arewacin Najeriya.
Daga baya aka fara mayar da makarantun na kwana da zimmar hana yara fita bara.
Fatawar ganin watan azumi da na sallah
Saɓanin fahimta game da fatawar ganin watan azumi da na sallah a arewacin Najeriya ba sabon abu ba ne, musamman yadda mabiya Shi'a suka daɗe suna saɓa umarnin sarkin Musulmi a Najeriya.
Sheikh Dahiru Bauchi na cikin malamai na baya-bayan nan da suka dinga bai wa mabiyansu umarnin saɓa wa fatawar sarkin Musulmi ta ɗaukar azumin watan Ramadana ko kuma na Ƙaramar Sallah.
An samu irin wannan saɓanin a lokuta daban-daban kamar a 2019 da 2020 da 2022. Mafiya yawan Musulmi kan yi ajiye azumi a wata yayin da mabiya malamin kan ajiye a wata rana daban.
Wannan matsaya da malamin ya dinga ɗauka ta sha jawo cecekuce tsakanin al'ummar Musulmi.
Yawan iyali mahaddata Ƙur'ani
A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin ƴaƴan shehin malamin, Bashir Dahiru Bauchi, ya ce yawan ƴaƴan da malamin ya haifa sun kai kimanin 90, sannan yana da jikoki da suka zarce 100.
Babban ɗa namiji na malamin shi ne Muhammad Bello, wanda ya rasu tun yana ƙarami, sai kuma mai bi masa, Dakta Hadi Dahiru Bauchi.
Ya bayyana cewa akwai ƴaƴan malamin sama da 70 waɗanda suka haddace Alƙur'ani, kuma jikokinsa sama da 100 ne suka haddace Ƙur'anin.
Ƙauna da yaɗa Tijjaniyya
Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi ba za ta taɓa cika ba idan ba a ambaci ɗariƙar Tijjaniyya manne da sunansa ba, da kuma maulidin Shehu Tijjani da yake jagoranta duk shekara.
Ana yi masa kallon ɗaya daga cikin mafiya shahara a jagororin ɗariƙar, musamman yadda yake ƙoƙarin tallata ta da koyar da ita.
Sanannen abu ne yadda malamin yake bayar da Tijjaniyya tare da addinin Musulunci duk lokacin da wani wanda ba Musulmi ba ya karɓi Musulunci.
Kazalika, yakan zayyano ɗabi'u da shika-shikan Tijjaniyya ciki - mafi shahara daga shi ne guje wa shan taba sigari.