Me ya janyo taƙaddama tsakanin Nasiru El Rufai da SDP?

Asalin hoton, El Rufai/x
Wata sabuwar dambarwar siyasa ta ɓarke a jam'iyyar SDP bayan dakatar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i da jam'iyyar ta yi.
Wani bangare da ke ikirarin shi ne halastaccen shugabancin jam'iyyar ne ya dakatar da shi na tsawon shekaru 30 saboda zargin bayyana kansa a matsayin ɗan jam'iyyar, duk da an dakatar da shi a baya.
Malam Nasiru El Rufai dai ya koma jam'iyyar SDP bayan ficewa daga jam'iyyar APC.
To sai dai kuma El Rufai na daga cikin gaggan ƴan siyasar da suka kafa haɗakar ADC ƙarƙashin shugabancin Sanata David Mark, inda suka amince da za su ƙalubalanci shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Matakin SDP
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar ta SDP, Araba Rufus Aiyenigba ya fitar, jam'iyyar ta gargaɗi mambobinta da yin kowace irin alaƙa da Malam Nasiru El Rufai wanda ta ce ba ya wakiltar ta.
"Mun kori El-Rufai tare da haramta masa ayyana kansa a matsayin ɗan jam'iyyarmu ta hanyar amfani da sunanmu ko alamarmu ko ma duk wani abu da jiɓance mu tare da haramta masa tallafa wa da kuɗi ko nuna goyon baya gare ta ko duk wata hanyar shiga a dama da shi a jam'iyyar SDP, har zuwa shekaru 30," in ji sanarwa.
Jam'iyyar ta ce ta ɗauki matakin korar Nasiru El Rufa'i ne daga SDP bayan wani taron ƙoli da ta gudanar inda ta yi alawadai da irin halayyar tsohon gwamnan na zamar mata ƙadangaren bakin tulu wanda ya ƙi barin jam'iyyar alhali kuma ya shiga jam'iyyar haɗaka.
Wane martani El Rufai ya mayar?
Har kawo yanzu dai, toshon gwamnan na jihar Kaduna bai ce uffan ba dangane da wannan kora. Sai dai magoya bayansa a jam'iyyar ta SDP, sun mayar da martani inda suka ce korar ta saɓa da kundin tsari.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sai ku duba ku gani cewa yana cikin kundin tsarin mulkin SDP? Saboda haka akwai ganganci ma ga waɗanda suka yi wannan furuci cewa sun dakatar da Malam Nasiru wai shekara 30. Ke nan wannan ba abun yadda ba ne ba abin amincewa ba ne," in ji Hon Abdullahi Mai Kano wani na hannun damar El Rufai a SDP.
Dangane kuma da cewa da SDP ta yi Malam Nasiru El Rufai ba shi da katin zama ɗan jam'iyyar, Hon Abdullahi Mai Kano ya ce ba gaskiya ba ne.
"Ka je mazaɓar Unguwar Sarki a Kaduna ka bincika. Nan ce mazaɓarsa kuma daga nan ya fito. Sunansa ma a sabuwar rijista da aka yi shi ne na farko. Sannan katin jam'iyyarsa yana ɗauke da lamba 35001."
Ya kuma yi ƙarin haske kan zargin da jam'iyyar ta SDP ta yi cewa Malam Nasiru El Rufai yana neman wargaza jam'iyyar kasancewarsa ya raba ƙafa tsakanin SDP da ADC.
"Ba su da wata hujja kan wannan abu da suka yi. Shi Malam Nasiru El Rufai ya zo wannan jam'iyya da zimmar a fito a gyara wannan jam'iyya ta SDP amma kuma suna ganin su ba haka suke so ba. Saboda haka har yanzu malam Nasiru ɗan jam'iyyar SDP ne," Hon Abdullahi Mai Kano.
Sharhin Masani
Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja kuma masanin kiyyar siyasa a Najeriya ya ce al'amarin bai zo musu da mamaki ba.
"Abin da hakan ke nuna shi ne kusan duk jam'iyyu ba ma na adawa ba kawai akwai masu faɗa aji - su ne suke yarjewa wani ya shiga jam'iyyar ko ya fita ko zai kai labari ko ba zai kai labari ba. Kuma hakan babban naƙasu ne ga tafarkin dimokraɗiyya.
Shi kansa shugaba Tinubu ana raɗe-raɗin yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar SDP," In ji Farfesa Kari.











