Shugaban Faransa ya buƙaci Isra’ila ta daina kashe mata da yara a Gaza

Asalin hoton, REUTERS
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce dole ne Isra’ila ta daina kashe ƙananan yara da mata da kuma tsofaffi a Gaza.
Da yake zantawa da BBC, Mista Macron ya ce duk da cewa yana Allah-wadai da ayyukan Hamas, yana sane da ƴancin Isra’ila na kare kanta.
Mr Macron ya ce babu wani dalili da zai sa a jefa bama-bamai kan fararen hula a Gazar, yana mai cewa ita ma Isra'ila za ta amfana idan aka tsagaita wuta.
Ya ce yana sane da cewa Isra’ila tana da ƴancin kare kanta, sannan ya yi kira ga Isra’ila ta daina harba bama-baman.
Ya ce "Mun sani cewa suna da ƴancin kare hakkinsu. Amma muna kira gare su da su daina kai harin bama-bamai a yankin. Yanzu ba lokaci ba ne na nuna yatsa ga juna. Dole ne a ɓullo da hanyoyin sulhu wajen dawo da alaƙa tsakanin abokai. Ga shi yanzu ana ruwan bama-bamai kan jarirai da mata da kuma tsofaffi. Babu wata hujjar yin hakan, don haka muke kira ga Isra'ila ta gaggauta tsagaita wuta.’’
Sai dai a martanin da ya mayar, Firaiminitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kamata ya yi shugabannin duniya su riƙa yin Allah-wadai da Hamas don kuwa idan aka zura ido wata rana tana iya kai hari a biranen Paris ko New York ko kuma wani wajen.
Shugaban Faransan dai ya ce yana fatan shugabannin duniya, ciki har da na Amurka da Birtaniya za su haɗa ƙarfi don ganin an tsagaita wuta a Gaza.










