An raba maki tsakanin Man United da Man City a Premier

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta tashi 0-0 da Manchester City a wasan mako na 31 a Premier League da suka fafata ranar Lahadi a Old Trafford.

Wasa na uku a bana da suka kece raini a tsakaninsu kenan:

Premier League ranar Lahadi 6 ga watan Afirilun 2025

  • Man Utd 0 - 0 Man City

Premier League ranar Lahadi 15 ga watan Disambar 2024

  • Man City 1 - 2 Man Utd

Community Shield ranar Asabar 10 ga watan Agustan 2024

  • Man City 1 - 1 Man Utd

Da wannan sakamakon United tana mataki na 13 a teburin Premier League da maki 38, bayan cin wasa 10 da canjaras takwas aka doke ta 13 daga ciki a kakar nan.

Kenan damar da ke gaban United ita ce a Europa League wasan zagayen farko da za ta fafata da Lyon ranar Alhamis.

Ita kuwa City mai maki 52, bayan karawa 31 tana mataki na biyar a teburin Premier League, wadda ke fatan samun gurbin Champions League a baɗi.

Sai dai City za ta kece raini da Crystal Palace a wasan mako na 32 a Etihad ranar Asabar 12 ga watan Afirilu.

Daga nan ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta je Everton a wasan mako na 33 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 19 ga watan Afirilu.

United kuwa za ta je Newcastle United ranar Lahadi 13 ga watan Afirilu a wasan mako na 32, bayan ta kammala fafatawa da Lyon ranar Alhamis a Europa.