Ko ganawar manyan ƴan adawa a Najeriya na tayar da hankalin APC?

Lokacin karatu: Minti 5

Ziyarce-ziyarce da ganawar da fitattun ƴan siyasa da ke hamayya da jam'iyya mai mulki a Najeriya, ke yi na ci gaba da haifar da hasashe dangane da alƙiblar siyasar ƙasar a 2027.

Masu fashin baƙi sun alaƙanta ziyarce-ziyarcen da ganawar da fitattun ƴan siyasar ke yi da buɗe fagen siyasar ƙasar ta 2027 wanda suka ce zai yi zafi bisa la'akari da cewa ƴan adawar na ƙoƙarin yin irin abin da ya faru a 2015, duk da cewa jam'iyyar da ke mulki yanzu ta banbanta da ta lokacin.

BBC ta yi duba kan wasu ziyarce-ziyarce da ganawa da fitattun ƴan siyasar suka yi a baya-bayan nan da kuma ko hakan zai yi tasiri a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ganawar Atiku da Cif Obasanjo

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya kai wa tsohon uban gidansa kuma shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun, a ranar Litinin.

Atiku Abubakar ya sami rakiyar fitattun ƴansiyasa da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da kuma sanata Abdul Ningi, ɗan majalisar dattawa daga jihar Bauchi.

Duk da cewa ganawar ta sirri ce sannan kuma babu wanda ya yi bayani dangane da abubuwan da ƴan siyasar suka tattauna, amma ganawar na zuwa ne a daida lokacin da jam'iyyun hamayyya ke ƙara fito da hanyoyin haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakaninsu domin tunɓuke jam'iyya mai mulki ta APC daga mulki a 2027.

Masu lura da al'amura dai na yi wa ziyarar kallon wani yunƙuri ne na ƙara neman sulhu da goyon baya da Atiku ke son samu daga Cif Obasanjo wajen tunkarar jam'iyya mai mulki ta APC a 2027.

Sai dai kuma kawo yanzu babu cikakken bayani da tabbaci dangane da ko Atiku Abubakar zai sake yin takara a 2027.

Kwankwaso da Aregbosola

A ƙarshen makon nan ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas.

A shafinsa na X Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun adawa ke kira da haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027.

A watan Oktoban 2024, jam'iyyar APC a Jihar Osun ta dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam'iyya da sukar shugabannin jam'iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande.

Ganawar ƴan siyasar biyu na nuni da yiwuwar alamar ƙulla haɗaka tsakanin Kwankwaso da Aregbesola a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027.

El Rufa'i ya kai ziyara ga ofishin SDP

A watan Maris na 2024 ne tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya kai wata ziyara zuwa hedikwatar jam'iyyar SDP a Abuja.

Hakan ne ya janyo raɗe-raɗi tsakanin al'ummar Najeriya cewa tsohon gwamnan na shirin ficewa daga jam'iyyar APC tun bayan tsamin da alaƙarsa ta yi da shugaba Bola Tinubu.

Mai magana da yawun El Rufa'i, Muyiwa Adeleye ya ce ziyarar da El Rufa'i ya kai hedikwatar SDP ramako ne kan ziyarar da shugaban jam'iyyar ya kai wa tsohon gwamnan, inda ya ƙara da cewa babu siyasa a al'amarin.

A baya-bayan nan ne kuma Malam Nasiru El Rufa'i a wani taro a Abuja na neman haɗin kan jam'iyyun hamayya, ya caccaki jam'iyyar APC inda ya bayyana ta da marar alƙibla.

Ziyarar Peter Obi ga SDP

Shi ma ɗan takarar shugabancin Najeriya a 2023 na jam'iyyar LP, Peter Obi ya kai irin ziyarar da El Rufa'i ya kai ofishin SDP, wani abu da ya sa abokan hamayya da masu sharhi kan al'amura ke ganin akwai yiwuwar ficewar Obi daga LP wadda ke cike da rikicin shugabanci.

Lokuta daban-daban Peter Obi ya gana da ƴan takarar shugabancin ƙasar a 2023 kamar Atiku Abubakar da Rabi'u Kwankwaso.

Ko a watan Mayun 2024 sai da Atiku da Peter Obi sun gana da manufar haɗakai.

Atiku, wanda ya yi wa jam'iyyar PDP takarar shugabancin kasa a zaben 2023, ya ce ganawarsa da Peter Obi, watau dan takarar jam'iyyar Labour na nufin su dunkule waje guda.

Wane tasiri ganawar za ta yi?

Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna ya ce lallai wannan ganawa da ziyarce-ziyarce da jagororin hamayya ke yi ka iya tayar wa da jam'iyya mai mulki hankali.

"Ai irin wannan haɗaka aka yi har da shi Tinubun wajen tabbatar da kayar da jam'iyyar PDP mai mulki a lokacin. Wannan kukan kurciyar ne ga jam'iyya mai mulki kimanin shekaru biyu gabanin zaɓe. Tasirin hakan shi ne ƴan adawa ka iya haɗa gangamin da zai iya kai wa da wahalar da jam'iyya mai ci. Kuma hakan zai bai wa jam'iyyar ta APC damar ɗaukar matakan da ta saba wajen daƙile yunƙurin adawa." In ji Farfesa Tukur Abdulƙadir.

Sai dai farfesa Tukur ya ce "akwai sauran runa a kaba bisa la'akari da jin-kai da jagororin hamayyar suke taƙama da shi. Kowanne a cikin masu son haɗe kan za ka ga sun fifita kansu sannan ba sa tunanin hakura su bi wani. Amma idan kowanne ya cire kuɗayi da girman kai suka yi amfani da dabaru irin na baya akwai yiwuwar ƙalubalantar APC. Amma yana da wuya yin hakan." In ji Farfesa.

Shi ma farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja ya ce ganawar ta jagororin hamayyar na nuni da cewa an fara siyasar kakar zaɓen 2027 mai zuwa gadangadan kuma lallai hakan na aikewa da saƙo ga jam'iyyar APC.

"Lallai ko wannan bai sa cikin APC ya ɗuri ruwa ba to zai gyara mata zama duk da cewa dai ita APC ba za ta tsaya ta kalle su ba. Kuma mu a mahangar siyasa, muna ganin wani saƙo ne wannan babba idan yan hamayya za su yi kwamba domin tunkarar zaɓen 2027 wanda ka iya yin zafi sosai. Matsalar dai a nan ita ce su jagororin hamayyar kansu ba a haɗe yake ba a wannan buƙatar.

Dangane kuma da ko za a samu haɗakar jagororin hamayya irin wadda aka samu a 2015, lokaci ne kawai zai iya tabbatar da hakan." In ji Farfsesa Kari.

Taron tsintsiya babu shara - APC

Mai magana da yawun jam'iyyar APC, Malam Bala Ibrahim ya ce "ko a jikin jam'iyyar APC."

Yayin wani martani da ya yi a hirarsa da BBC, Bala Ibrahim ya ce "ai kana damuwa ne a lokacin da ka ga mutane masu farcen susa suna haɗa kai. Amma waɗannan masu ziyarce-ziyarce da ganawar ai tsaron tsintsiya ne da aka ba zai shara ba." In ji Bala Ibrahim.