Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƙwayoyin cutar sanyin al'aura ke barazanar bazuwa a ƙasashen duniya
- Marubuci, Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Cutar snail fever da ake kira da bilharzia wanda ake samu ta hanyar amfani da gurbataccen ruwan rafi ko kogi wanda yake da tsutsotsi da ƙananan dodon koɗi (snails) masu ɗauke da ƙwayar cutar na shiga jikin mutum ne ta cikin fata, sannan ta ɓuya a cikin jini.
Daga bisani ƙwayayenta kan maƙale a cikin hanta, huhu da gabobin al'aura, kuma cutar na iya zama a jiki ba tare da an gano ta ba tsawon shekaru.
Masana kimiyya na gargaɗi cewa cutar bilharzia wata cutar ƙwayoyin tsutsotsi ne da aka daɗe ana yin watsi da ita wanda ka iya sauyawa ta yadda hakan zai ƙara wahalar shawo kanta da kuma hana yaɗuwarta.
Mafi yawan mutane kusan miliyan 250 da ake yi wa maganin cutar a duk shekara na rayuwa ne a Afirka, inda nau'in ƙananan dodon kodi (snails) da ke ɗauke da ƙwayar cutar suke da asali.
Sai dai an ruwaito yaɗuwar cutar a ƙasashe 78 a duniya, ciki har da China da Venezuela da Indonesia.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa wannan lamari abin damuwa ne a matakin duniya, bayan bincike ya nuna cewa ƙwayar cutar na sauyawa ta yadda hakan zai ba ta damar yaɗuwa zuwa sabbin yankuna.
Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da WHO ke bikin Ranar Cututtukan yankuna masu zafi da aka yi watsi da su ta Duniya, wadda ke da nufin jawo hankalin jama'a kan cututtukan da ƙwayoyin ƙananan halittu da ke haifar da cututtuka ke haddasawa.
Cututtukan da waɗannan ƙwayoyin cutar ke haddasawa na shafar fiye da mutum biliyan ɗaya, musamman waɗanda ke rayuwa a yankunan da ke fama da talauci.
Mene ne cutar bilharzia (snail fever)?
Cutar bilharzia na faruwa ne lokacin da mutum ko dabba suka shiga ko yi hulɗa da ruwa da ke ɗauke da ƙananan tsutsotsi (larvae) da kuma ƙananan dodon koɗi (snails) ke saki.
Waɗannan ƙananan tsutsotsi kan fitar da sinadarai da ke narkewa a cikin fata, sannan su shiga jikin mutum ta cikin fata ba tare da an ji ba. Daga nan sai su girma su koma manyan tsutsotsi, su zauna a cikin jijiyoyin jini.
Bayan sun girma, tsutsotsin mata suna sakin ƙwai. Wasu daga cikin ƙwayayen kan fita daga jiki ta hanyar bayan gida ko fitsari, amma wasu kuma kan makale a cikin sassan jiki.
Lokacin da ƙwayayen suka maƙale, garkuwar jiki na ƙoƙarin yaƙar su, wanda hakan ke haddasa lalacewar lafiyayyun gaɓoɓin jiki a kusa da wurin.
Wannan lalacewa na iya jawo matsaloli masu tsanani ga hanta da mafitsara da sauran gaɓoɓi.
Wasu ƙwayayen kan maƙale a cikin ko kusa da gabobin ƙugu, lamarin da ake kira urogenital schistosomiasis wanda ke iya haifar da ciwon ciki da cutar daji kuma a wasu lokuta masu tsanani tana iya kai wa ga mutuwa.
Ana iya warkar da cutar snail fever ta hanyar amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta shawarci mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar da suka haɗa da ƙananan yara da manoma da masu kamun kifi, su riƙa samun wannan magani a duk shekara na tsawon wasu shekaru domin kare kansu.
Sai dai masana kimiyya sun bayyana cewa sabbin nau'ikan ƙwayoyin cutar na iya kaucewa magungunan da ake amfani da su a yanzu.
Daya daga cikin masana da suka yi wannan gargadi ita ce Farfesa Janelisa Musaya, mataimakiyar darakta a Malawi Liverpool a shirin bincike na Wellcome Clinical wadda ta ce wannan na ƙara dagula yaƙin da ake yi da cutar.
Me ya sa cutar ke ci gaba da ɓarkewa a wasu yankuna duk da ana magani?
Ko me ke haddasa ci gaba da ɓarkewar cutar a wasu yankuna duk da ana magani?
Bincike ya nuna cewa ƙwayoyin cutar ta mutane da na dabbobi suna haɗuwa suna haihuwa tare, abin da ke haifar da sabbin nau'ikan ƙwayoyin cutar mafiya haɗari.
Mutane da dabbobi na iya kamuwa da waɗannan sabbin ƙwayoyin cutar a lokaci guda, lamarin da ke ƙara wahalar shawo kan yaɗuwar cutar.
Masana sun riga sun san cewa ƙwayoyin cutar mutane da na dabbobi na iya haɗuwa, amma ba su da tabbacin ko ƙwayayen halittun biyu na iya rayuwa da yaɗuwa a waje da jikin wanda ke ɗauke da cutar ba.
Don tabbatar da hakan, masana sun ɗauki samfura daga mutane da dabbobi a wasu al'ummomi a Malawi. Sun gano cewa kashi 7 cikin 100 na ƙwayoyin cutar da aka gwada daga ƙwayayen halittun wanda shi ne mafihaɗari, adadi mai yawa fiye da yadda suka zata.
Wannan na nuna cewa ƙwayayen halittun biyu na yawaita kuma za su ci gaba da yaɗuwa.
Farfesa Janelisa Musaya ta ce, idan yaɗuwa na ci gaba haka, wannan babbar matsala ce.
Ta kuma yi gargaɗi cewa, saboda binciken ya shafi wasu wurare kaɗan ne, abin da aka gani na iya zama ƙaramin ɓangare ne kawai na matsalar, domin gwaje-gwaje ba koyaushe ke gano ƙwayayen halittun biyu mafi haɗari ba.
A nan gaba, waɗannan sabbin ƙwayoyin cutar na iya fin ƙarfin tsoffin nau'ikan cutar su mamaye su gaba ɗaya.
Wannan na da hatsari, domin likitoci ba su da cikakken bayani kan yadda za su kula da marasa lafiya da ke ɗauke da waɗannan sabbin ƙwayoyin cutar mafi haɗari.
Saboda haka, Musaya ta yi kira ga masu tsara manufofi da su tashi tsaye tun da wuri, su ɗauki mataki kafin matsalar ta ƙara muni.
Gwaje-gwaje ba ya gano ko cutar ta shafa al'aura
Binciken ya nuna cewa sabbin ƙwayoyin cutar daga ƙwayayen halittun biyu na shafar gaɓoɓin al'aurar, amma yana da wahala a gano wannan nau'in cutar.
Dalilin haka shi ne ƙwayayen halittun biyu ba sa kama da ainihin ƙwayaye idan aka duba su da na'urar ganin ƙananan halittu don haka gwaje-gwaje kan kasa gane su.
Haka kuma, ma'aikatan lafiya na iya ɗaukar alamomin cutar a matsayin cutukan da aka kamuwa da su ta hanyar jima'i (STI).
Idan ba a yi magani ba, cutar na iya haifar da:
- Raunuka a gabobin al'aura
- Rashin haihuwa
- Ƙarin haɗarin kamuwa da cutar HIV
- Ga mata, illolin cutar sun fi tsanani, ta fuskar lafiya da zamantakewa da haihuwa in ji farfesa Janelisa Musaya.
Progress under pressure
Masana sun gano cewa ƙwayoyin cutar da aka samu daga ƙwayayen halittun biyu na iya taimaka wa cutar bilharzua ta kafa kanta a sabbin yankuna na duniya.
Canjin yanayi da tafiye-tafiye da ƙaura na taimaka wa yaɗuwar cutar.
An riga an ruwaito ɓarkewar wannan nau'i a wasu sassan kudancin Turai.
Dokta Amadou Garba Djirmay na Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce wannan lamari babbar damuwa ce a matakin duniya, domin yana iya kawo cikas ga shirin kawar da cutar.
Ya ce a wasu ƙasashe, ko da cutar ba ta yaɗuwa tsakanin mutane, tana nan a jikin dabbobi, abin da ke iya zama barazana ga mutane.
WHO na sauya tsarinta, inda za ta fitar da sabbin shawarwari kan yaƙar cutar a dabbobi, tare da tura gargaɗi ga ƙasashe game da ƙwayayen halittu biyu.
Duk da cewa shirye-shiryen raba magunguna sun rage yawan masu cutar da kashi 60 tsakanin shekarar 2006 da 2024, WHO ta ce raguwar tallafin kuɗi da kashi 41 na barazana ga cigaban da aka samu.
Sai dai Farfesa Janelisa Musaya ta ce har yanzu akwai fata: