Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan cibiyoyi biyar da aka fi safarar bayi a Afirka
- Marubuci, Isidore Kouwonou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- Lokacin karatu: Minti 6
Bauta da safarar bayi daga Afirka na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a tarihin nahiyar, lamarin da ya sa wasu idan suka yi waiwaiye, suka duba abubuwan da suka faru, sukan shiga damuwa da tausayi.
A ƙididdigar Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), tsakanin mutane miliyan 15 zuwa miliyan 20 ne aka tursasa wa barin ƙasashensu, aka yi safararsu zuwa ƙasashen waje. Daga ciki akwai kusan miliyan 10.5 da suka isa yankin Amurka da Caribbean.
Wannan safarar da aka yi, ta taimaka wajen canja tarihin nahiyar da rusa masarautu, kamar yadda Maryse Condé ta wallafa a littafinta mai sun "Segou," wanda a ciki ta bayyana yanayin kasuwancin bayi a Afirka ta Yamma.
Duk da haramta cinikayyar bayi da aka yi a hukumance, har yanzu akwai alamu da gurabun harkar da ake iya ci gaba da gani ana tuna baya.
Har yanzu akwai wuraren da ake gani a tuna da safarar bayi. Sun zama wuraren da ake zuwa ziyara domin bincike da tuna tarihin abubuwan da suka faru a baya da ma yawon buɗe ido.
Daga tsibirin Gorée a Senegal da Cape Coast ko kuma El Mina a Ghana zuwa House of Slaves a yankin Agbodrafo a Togo da hanyar fitar da bayi da ke Ouidah a Benin da tsibirin Janjanbureh a Gambia, dubban mutane suna zuwa wuraren nan a Afirka domin gane wa idonsu.
1. Tsibirin Gorée a Senegal
A ƙasar Senegal, akwai wurin da ake kira gidan bayi wato House of Slaves da ke tsibirin Gorée a Dakar, babban birnin ƙasar.
An gina wajen ne a ƙarni na 18 a tsibirin, inda turawan mulkin mallaka na Portugal suka gina shi a shekarar 1536.
Duk wanda ya je gidan yana da labari daban yake samu game da wajen, musamman bayan shiga ƙofar da ake kira 'door of no returns' inda daga wajen ne asalin wahala ke farawa.
"Da zarar mutum ya shiga ƙofar wajen, shi ke nan ya yi ban-kwana da Senegal, kuma wataƙila sun tafi ke nan har abada cike da damuwa da baƙin ciki," in ji wani ma'aikacin wajen.
Masu ziyarar wajen da dama na barin wajen da ɓacin rai da tausayi, "masu ziyartar wajen suna zuwa cikin farin ciki, amma idan suka ga yadda wajen yake, suka karanta labarin irin wahalar da mutane suka sha, musamman ganin bayin ma mutane ne irinmu, sai su shiga damuwa da tsausayi, wasu ma har fashewa suke yi da kuwa."
A ziyararsa ta farko a ranar 22 ga Fabrailun 1992, Fafaroma John Paul II ya ce, "baƙaƙen fata maza da mata da yara ƙanana sun fuskanci wulaƙanci a wajen safararsu," in ji shi.
Duk da cewa babu haƙiƙanin alƙaluma, amma ana tunanin dubban mutane ne suke ziyartar wajen a duk shekara, inda masu yawon buɗe ido 700,000 suke ziyartar tsibirin na Goree kusan duk shekara.
Daga cikin fitattun mutanen da suka taɓa ziyartar wajen akwai Nelson Mandela da François Mitterrand da Jimmy Carter da Bill Clinton da George Bush da Lula da Silva da King Baudouin da iyalan Obama da James Brown da Jimmy Cliff da sauran su.
2. Agbodrafo a Togo
Akwai ɗakuna shida da kuma wani babban ɗaki da aka tanada domin zaman masu sayen bayi, gidan bayi na da ke Agbodrafo ko kuma gidan Wood Home (sunan wani ɗan Scotland John Henry Wood wanda ya gina gidan), yana can ne bayan gari ne.
Akwai tafiyar kusan kilomita 50 daga Lome, babban birnin ƙasar.
A shekarar 1835 ne John Henry Wood ya gina gidan, inda ma'aikatar harkokin yawon buɗe ido ta Togo ta ce gidan wani waje ne na adana tarihi da tuna irin damuwar da mutanen baya suka shiga da juriyarsu.
Gidan ya kasance mahaɗa domin safarar bayi, inda turawan Portugal ke amfani da shi wajen tattara bayi kafin a fitar da su, musamman a tsakanin ƙarni na 17 da na 19.
Ma'aikatan gidan ne suke zagayawa da baƙi suna nuna musu yadda gidan yake da labarin alamomin da ke rubuce a wajen.
Da zarar mutum ya shiga zai yi ido biyu da wata bishiyar mangoro, inda bayi suke "wankar tsarki' kafin a fitar da su.
3. Hanyar fitar da bayi daga Ouidah zuwa Benin
Hanyar fitar da bayi da ke Ouidah, tana da nisan kilomita 30 ne daga birnin Cotonu, babban birnin Benin.
A cewar masana tarihin Jamhuriyar Benin, gaɓar tekun Ouidah ta zama wata hanyar da aka tafiyar da bayi daga ƙasashen Afirka zuwa ƙasashen Cuba da Haiti da Brazil da yankin Caribbean.
Jiragen ruwan da aka kwashi bayi daga Ouidah na tsayawa ne a Ghana da Senegal kafin su ci gaba da tafiya zura turai, sannan bayi da yawa suna mutuwa a hanya kafin a ƙarasa.
A cikin tafiyar kusan kilomita 4 a Ouidah, akwai kasuwar sayar da bayi, da ma gwanjonsu, inda a wajen ne turawa suke musayar bayi da wasu kayayyakin buƙata a madadin bayin.
Haka kuma a Ouidah akwai wani gida da idan mutum ya saya bayi, yake saka musu alama ta hanyar nana musu ƙarfe da ake ƙona wuta ya yi ja, inda ake saka lamba domin bambance na kowa.
4. Cape Coast ko El Mina a Ghana
Wani wajen mai matuƙar muhimmanci a tarihin safarar bayi a yankin Afirka ta Yamma shi ne Cape Coast wanda ke da nisan kilomita 150 daga Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
An ƙirƙiri birnin ne a ƙarni na 15, kuma turawan Portugal ne suka gina, kafin ya zama sansanin sojin Birtaniya, sannan daga bisa ya zama cibiyar kasuwancin zinare, sannan daga ƙarshe ya zama wajen cinikayyar bayi.
Akwai gidajen turawa masu kasuwancin baya a saman bene, sai gwamnoni a tsakiya, da kuma sojoji a ƙasa, sai bayi a cikin kejin da ake ɗaure su.
Da zarar jirgin ruwa ya zo, za a ɗaure bayin, waɗanda suka ƙunshi mata da maza da yara za a ɗaure da kaca, sai su bi ta ƙofar ban-kwana su shiga jirgin ruwan da za a tafi da su.
5. Tsibirin Janjanbureh da ke Gambia
Janjanbureh, wanda a baya ake kira da tsibirin McCarthy ko Georgetown, an saka masa sunan ne domin wanda ya assasa shi, wanda baturen Ingila ne mai cinikayyar bayi da ya fara isa yankin.
Wajen na da matuƙar muhimmanci wajen cinikayya da safarar bayi daga nahiyar Afirka zuwa turai.
Wani mai suna Freed ne a shekarar 1823 ya canja sunan zuwa Janjanbureh ko kuma Georgetown bayan an haramta cinikayyar bayi a hukumance a 1807.
Wuri ne mai girman hekta 7, kuma ko yanzu mutum ya shiga, zai ga "ɗakunan bayi" da aka haɗa da katako da kacocin da ake amfani da su wajen ɗaure bayin da aka ajiye a wajen.
Akwai wata bishiya da ake kira "bishiyar tsira", inda bayi suke ɓoyewa da zarar sun samu nasarar tserewa daga iyayen gidansu.
A tsibirin Janjanbureh, kowane gida ko gini ko ma wani abu, akwai abin da yake nufi, kuma yawanci labari ne na tashin hankali da baƙin ciki da ban tsausayi.
Ana tattara bayin da aka kwaso daga wurare daban-daban a wajen, sai a kwashe su zuwa Banjul, babban birnin Gambia, daga can kuma a tafi da su turai.
Ba za a iya bayar cikakken bayani ba a kan cinikayyar bayi da wahalar da suka sha ba tare da ambaton Zanzibar ba, wani wajen mai cike da kayayyakin tarihi. Birnin ma ya kasance wani babban waje a ake bi da bayi zuwa tekun India a ƙarni na 19.
Ta birnin ne aka safarar bayi zuwa India da ƙasashen Laraba da sauran su.