Muna nan a matsayin shugabannin PDP - Turaki

Lokacin karatu: Minti 2

Jam'iyyar PDP ƙarƙashin shugabancin Kabiru Tanimu Turaki ta yoi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta bayar wanda ya soke babban taron da ta gudanar a birnin Ibadan a cikin watan Nuwamban 2025.

Shugaban jam'iyyar, wanda aka zaɓa a lokacin babban taron na Ibadan, Kabiru Tanimu Turaki ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja cewa za su bi matakan shari'a domin ƙwatar haƙƙinsu.

Ya zargi kotun da tafka kuskure a hukuncin da ta bayar, wanda ya fitar da buƙatar da babu wani ɓangare da ya nemi a biya masa, daga cikin masu jayayya da juna.

A ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026 wata babbar kotun tarayya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta rusa shugabancin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a, Uche Agomoh, ta kuma soke babban taron da jam'iyyar za ta gudanar.

Kotun ta ce an gudanar da babbn taron PDP na Ibadan ne a bisa yi wa umarnin kotu karan tsaye, domin haka duk wata matsaya ko hukuncin da aka yanke a yayin taron ya saɓa doka kuma ba zai taɓa zama gaskiya.

Har ila yau, kotun ta amince da ɓangaren shugabancin riƙon ƙwarya na Mohammed Abdulrahman a matsayin shugaban jam'iyyar, wanda aka ruwaito yana samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike - har sai an gudanar da babban taron jam'iyyar.

Sai dai, a gefe guda ɓangaren Tanimu Turaki ya sha alwashin bin duk matakan da suka dace domin ƙwato ƴancin su.

Farida Umar it ace Mataimakiyar sakataren yaɗa labaran jam'iyyar PDP ɓangaren Turaki ta ƙasa, kuma ta shaida wa BBC cewa a yanzu haka sun riga sun ɗaukaka ƙara kuma suna jiran ranar da kotu za ta kira su domin jin bahasi.

Ta ce ''kamar yadda ka sani, an tafi convention a Ibadan kuma mun bi duk dokokin da ya kamata a bi, kuma an gabatar da mu a matsayin ƴan kwamitin gudanarwa na PDP,''

Ta jaddada cewa suna nan a matsayin shugabannin jam'iyyar PDP da doka ta sani, har sai idan kotun ɗaukaka ƙara ta kammala shari'a kuma ta bayar da hukunci akasin hakan.

Farida Umar ta yi zargin cewa wasu ne ke amfani da kotu wajen ruruta rikici a cikin gidan jam'iyyar PDP don an fahimci cewa ''ita ce jam'iyyar adawa mai ƙarfi a Najeriya.''