Abin da zai sha bamban idan Amurka ta kai wa Iran hari a wannan karo

    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yadda makeken jirgin ruwan yaƙin Amurka da ake kira USS Abraham Lincoln ya isa sansanin sojin Amurka da ke kusa da tekun Iran, ya sa an fara tunanin ko dai an kusa fara gwabzawa ne.

Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar mafi zafi kuma wanda aka fi amfani da ƙarfi wajen fatattakar masu zanga-zangar a tarihin Iran. Wannan ya sa tura makeken jirgin ya nuna yiyuwar Amurka da Iran na shirye-shiryen nuna wa juna yatsa nan kusa.

Shugabannin Iran sun samu kan su a tsaka mai wuya ne na zanga-zangar yunƙurin kifar da gwamnati da kuma shugaban Amurka, wanda har yanzu ba a fahimci asalin maƙasudin ayyukansa a Iran ba.

Yadda Tehran ta fuskanci matsalolin baya

Yadda Iran take fuskantar barazanar Amurka a wannan karo ya saɓa da yadda aka saba gani tana yi a lokutan baya.

Barazanar shugaban Amurka Donald Trump ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ta Iran ke fama da matsalolin cikin gida. Don haka wani harin da Amurka za ta ƙaddamar a yanzu zai iya ta'azzara lamura ne a ƙasar, da ma yankin baki ɗaya.

A cikin ƴan shekarun nan, Iran na fifita jan-ƙafa da kuma mayar da martani kaɗan.

Bayan hare-haren Amurka a cibiyoyin nukiliyar Iran a ranakun 21 da 22 na watan Yunin 2025, Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari a sansanin sojin Amurka na Al Udeid da ke Qatar a washegari.

A cewar shugaban Amurka, Iran ta aike mata da saƙo gargaɗin yunƙurin kai harin, wanda ya sa ta samu nasarar kakkaɓo makaman ba tare da ɓarna ba.

Aika saƙon yiwuwar kai harin da Iran ta yi ya nuna cewa ba ta son yaƙi ya rincaɓe, kuma ba ta so yaƙin ya yi zafi.

An ga hakan ma a watan Janairun 2020 lokacin wa'adin mulkin Trump na farko. Bayan kashe jagoran dakarun Quds, Qassem Soleimani da Amurka ta yi a kusa da filin jirgin Baghdad a ranar 3 ga Janairu, Iran ta mayar da martani bayan kwana biyar ta hanyar kai hari a sansanin sojin Amurka da ke Ain al-Asad a Iraq.

A lokacin ma Iran ta bayyana wa Amurka yunƙurin kai harin, kuma ba a kashe sojan Amurka ko ɗaya ba.

Amma yanzu alamu na nuna cewa ƙasar na ɗaukar wata dabarar ce daban.

Ƙasar dai na yunƙurin warwarewa ne daga ɗaya daga cikin matsalolin cikin gida da ƙasar ta fuskanta tun bayan juyin juya halin 1979.

Zanga-zangar da aka fara a watan Disamba zuwa farkon Janairu ta yi zafi, inda gwmnatin ƙasar ta yi amfani da ƙarfi wajen tsayar da ita. Ƙungiyoyin sa kai da likitocin ƙasar sun ce an kashe dubban mutane, sannan an raunata da dama, tare da kama wasu.

Har yanzu dai ba a iya tantance adadin waɗanda aka kashe ko raunatawa ko kamawa ba a ƙoƙarin tsayar da zanga-zangar, sannan an katse intanet a ƙasar wanda ya wanzu na kusan mako biyu.

Gwamnatin Iran dai ba ta ɗauki alhakin kashe-kashen ba, inda ta nace cewa akwai hannun "ƙungiyoyin ƴan ta'adda," sannan ta zargi Isra'ila da kitsa hayaniyar.

Duk da cewa zanga-zangar ta lafa, har yanzu akwai alamu da raɗaɗinta domin ba a taɓa samun giɓi da takun-saƙa mai zafi tsakanin ƴan ƙasar da gwamnati ba kamar haka a baya.

Shin Iran na rage zafin kai ne?

Waɗannan abubuwan da suka faru ne ya sa ake ganin hare-haren na Amurka na wannan karon za su sha bamban.

Idan Washington ta kai hari marasa ƙarfi, za ta iya iƙirarin samun nasara ba tare da jefa yankin cikin yaƙi ba.

Idan har aka samu matsala ko kifar da gwamnatin ƙasar Iran mai kimanin mutane miliyan 90, za a sha wahala wajen sauyin gwamnati. Ƙasar za ta iya fuskantar rikicin cikin-gida da tashin-tashina da zai iya shafar yankin baki ɗaya.

Wataƙaila fargabar ɓarkewar matsaloli irin waɗannan na cikin abubuwan da suka sa Tehran ke jan-ƙafa wajen ɗaukar mataki mai zafi.

Manyan kwamandojin dakarun juyin-juya-hali da jami'an tsaron ƙasar da jagororin siyasar sun ce duk wani matakin hare-hare da Amurka ta ƙaddamar, ko mai ƙanƙantarsa, za su ɗauka ne kawai a matsayin ƙaddamar da yaƙi.

Wannan maganar ce ta jefa fargaba a cikin ƙasashen da suke maƙwabtaka da Iran, waɗanda suke da sansanonin sojin Amurka. Da zarar Iran ta kuduri aniyar mayar da martani, ƙasashen ne farko ko da kuwa babu hannunsu kai-tsaye a yaƙin, wanda hakan zai sa yaƙin ya ƙara zafi.

Trump ya san an rage wa Iran ƙarfinta idan aka kwatanta da ƙarfinta kafin yaƙin kwana 12 da Iran, ita kuma Tehran ta san Trump bai shiga fara cikakken yaƙi na gaba-gaɗi ba.

Yadda kowane ɓangare ya fahimci halin da ɗaya ɓangaren yake ciki zai taimaka. Amma kuma zai iya zuwa da rashin fahimta ta hanyar rashin fahimtar asalin manufar kowane ɓangare da ma yanayin ƙarfin gwiwarta.

A wajen Trump, lallai yana buƙatar abin da zai nuna a matsayin nasarar da zai ce ya samu daga Iran.

Ita kuma Iran da shugabanninta, babban matsalar da suke fuskanta ita ce tunanin dabarun da za ta yi amfani da su. Yadda take jan-ƙafa a baya wajen mayar da martani ba dole ba ne ya yi kataɓus a yanzu, musamman idan tana so ta nuna ƙwanji.

Sai dai kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa ma za ta iya barin da ƙura wajen zafafawa tare da ta'azzara matsalar baki ɗaya.