Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa sojojin Najeriya ke musanta masaniyar yin sulhu da ƴanbindiga?
A ranar Alhamis ne hedikwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi al'ummomin da ke zaune a garuruwan da ke fuskantar hare-haren ƴanbindiga a arewacin ƙasar da su guji ƙulla sulhu da ƴanbindiga, inda hedikwatar ta ce ba da yawunta ba sannan ba ta da masaniya.
Daraktan da ke kula da sashen watsa labarai na hedikwatar, Manjo Janar Markus Kangye ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da hedikwatar ke yi sau biyu a kowane mako.
"A iya sanina, ba mu taɓa ƙulla wani sulhu da ƴanbindiga ba kamar yadda ake faɗi. Me ya sa al'umma ke son yin hakan? Ba na tunanin suna son samun izini daga wurin sojoji domin yin hakan. Kuma ba na tunanin sojoji suna da masaniya kan hakan." In ji Manjo Janar Markus.
Ana dai ganin bayanin na hedikwatar tsaro ba zai rasa nasaba da bayanan da ke nuna yadda wakilai daga gwamnatin tarayya ke shigewa gaba wajen yin sulhu da ƴanbindigar da ake ganin tamkar ya janyo rashin jituwa tsakanin hukumomin tsaro a Najeriya.
Illar rarrabuwar kan hukumomin tsaro
"Wannan na nuna maka cewa akwai rashin jituwa da rashin yin aiki tare tsakanin sojoji da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro domin muna da bayanan da ke nuna tabbas jami'an gwamnati na shigewa gaba wajen yin wannan sulhu. Mun gani a Birnin Gwari na jihar Kano" In ji Malam Kabiru Adamu, masanin tsaro a Najeriya.
Bayanai na nuna cewa irin wannan tsaka mai wuya da gaba kura baya siyaki da al'ummomin garuruwan da ke fuskantar hare-hare ke ciki ke sa wasu su yi gaban kansu wajen yin sulhu da ƴanbindiga.
Rahotanni dai na cewa al'ummomi da shugabannin garuruwa musamman a wasu ƙananan hukumomin jihar Katsina da suka hada da Batsari da Jibia da Safana sun fara cimma sulhu da ƴanbindiga inda suke shiga yarjejeniyar biyan haraji a tsakaninsu.
"Jama'a sun fuskanci cewa jami'an tsaro na da rauni wajen kare su alhali kullum ana kai musu hare-hare babu ƙaƙƙautawa wannan ne ya sa su yanke shawarar su yi sulhu da ƴanbindigar nan tunda dai an gaza tsare musu rayukansu da dukiyoyinsu. Sannan kuma zancen gaskiya duk abin da za a yi daga ƙarshe dai dole a komawa batun sulhu. Kuma su mutane sun fahimci haka." In ji Malam Kabiru Adamu.
"Ba lallai ne a ce yadda mutanen ke yin sulhu da ƴanbindigar shi ne hanyar da ta dace ta sulhu ba. Su kansu wanda ake shigar da gwamnati da jami'an tsaron, ba ya tafiya yadda ya kamata shi ya sa da an yi kwana biyu sai ka ji an koma gidan jiya," kamar yadda Kabiru Adamu ya yi ƙarin haske.
Illar sulhu ba tare da shigar da masu ruwa da tsaki ba
Malam Kabiru Adamu ya ce akwai babbar illa da ke tattare da yin sulhu ba tare da shigar da masu ruwa da tsaki a sulhu da ƴanbindiga ba ciki har da hukumomin tsaro da ke da masaniya a kai.
"Misali za a iya cimma sulhu tsakanin mutanen gari ko kuma jami'an wata hukuma su shige gaba a samu sulhu ba tare da sanin sauran hukumomin da su ma suke da ruwa da tsaki ba to jami'an da ba su da masaniya za su iya kai wa ƴanbindigar farmaki wanda su kuma abin zai harzuƙa su sai a koma gidan jiya."
Saboda haka ya kamata a shigar da hukuma tun ma kafi a fara maganar sulhu domin gindaya wasu sharuɗɗa." In ji Malam Kabiru Adamu.
Hanyoyin sulhu mai ɗorewa
Masanin ya ce akwai wasu matakan da ya kamata a bi guda bakwai kafin samun sulhu mai ɗorewa da ƴanbindiga.
- Tuntuɓar duk masu ruwa da tsaki da suka haɗa da al'umma da hukumomi da su kansu ƴanbindiga. Ana cimma hakan ne bayan yin bincike na haƙiƙa wajen gano duk wanda ke da ruwa da tsaki a al'amarin domin tabbatar da cewa ba a bar su a sulhun ba.
- Magance matsalar zamantakewa tsakanin al'ummomin da ke da bambancin ƙabila da addini da sauransu kamar batun manoma da makiyaya. Idan har ba a magance wannan matsalar ba to ko an yi sulhu da wuya ya cimma manufar.
- Magance matsaalr talauci: Lallai talauci ya yi kakatutu a irin waɗannan wurare kuma dole ne a magance shi kafin a iya cimma batun sulhu.
- Daƙile bazuwar makamai: Dole ne sai an datse hanyoyin da makamai ke bazuwa a tsakanin al'umma kafin sulhu ya yi tasiri.
- Cire siyasa
- Magance matsalar sauyin yanayi
- Daƙile bazuwar labaran ƙarya da ke tunzura jama'a kai hare-hare.