Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Aleem Maqbool
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan Sashen Addini
Yaƙi tsakanin Isra'ila da Gaza na ci gaba da ɗimauta al'ummar duniya baki ɗaya.
A birnin Manchester na Birtaniya - babban birnin da ke da Musulmai da Yahudawa masu yawa - mazauna yankin na cike da taraddadi kan abin da hakan ke nufi ga rayuwarsu.
A ranar Laraba, a tsakiyar Manchester, mutane kusan 1,500 ne suka taru a Dandalin Peter's don tunawa da waɗanda aka kashe a Isra'ila.
An yi ta ɗaga tutocin Isra'ila har aka gama taron. An kuma yi ta nuna hotunan mutanen da suka riga mu gidan gaskiya. Wasu sun zubar da hawaye, amma akasari an nuna goyon baya ne ga Isra'ila.
"Muna ganin duk wani Bayahude na da irin wannan tunanin," in ji Eli Dresner mai shekara 25.
"Mu dangi ɗaya ne, mun fito daga yanki ɗaya. Ko da ban san su ba, idan na ga wani Bayahude, sai na ji ya zama dangina."
Da gagarumar alaƙar tarayyar tarihi da matsananciyar damuwa, wani rukuni na ƙanƙanuwar al'ummar Yahudawan duniya miliyan 16, na nufin da yawa a Birtaniya sun san wasu mutane a Isra'ila.
"Ina da 'yan uwa a Isra'ila da aka kira su, don su taimaka wa ƙasar, kuma kusan kowa a nan yana da wani a can da ya kasa dawowa gida," a cewar Mista Dresner.
Wata ƙungiya mai ba da tsaro ga Yahudawan Birtaniya (Community Security Trust) ta ce ta samu ƙaruwar ƙin jinin Yahudawa ninki shida, idan aka kwatanta da irin wannan makon a bara.
"Wani ya faɗa min cewa an yi musu barazana a tashar jirgin ƙasa jiya," kamar yadda Eli ya bayyana. "Matasa bakwai ko takwas ne suka tunkare shi suna cewa za su zubar da jinin Yahudawa a faɗin Birtaniya."
Ɗan shekara 25, Eli Dresner ya ce mutanen da ya zanta da su, sun faɗa masa cewa ba sa son ganin tashin hankali a birnin.
"Ina da abokan da ke goyon bayan Falasɗinawa kuma mun iya yin tattaunawa ta fahimta da su - saboda mun san juna ne tun kafin lokacin wannan lamari," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
A kusa da Dandalin St Peter's, akwai Cheetham Hill Road da ke arewacin Manchester, wata unguwa mai masallatai da kuma shagunan sayar da kayayyakin abinci na halal na Musulunci.
Ga kuma wuraren ibadar Yahudawa da na shan shayinsu - inda a nan ne Musulami da Yahudawan Manchester ke haɗuwa.
"Mu Musulmai, muna saba zama lafiya da Yahudawan unguwar nan," kamar yadda Talat Ali mai shekara 54 ya bayyana, wanda ya taɓa yin aiki da wasu ƙungiyoyi a Zirin Gaza.
Lokacin da ya ji labarin harin da Hamas ta kai ranar Asabar, Ali ya ce ya aika wa Yahudawa abokansa saƙon alhini da ke Manchester.
Daga nan kuma ya ci gaba da neman jin halin da abokansa ke ciki a Gaza. Ya ce bai samu wani martani ba game da halin da suke ciki.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamar sauran shahararrun Musulmai a Manchester, Ali na fargaba game da goyon bayan Falasɗinawa a kafofin yaɗa labarai, wanda zai iya jawowa a ga kamar yana ƙin jinin Yahudawa ne.
"Akwai fargabar abin da ka iya faruwa," in ji shi, "Ko a yau da na shiga wata ganawa a matsayina na Musulmi tilo a wurin, na ji kamar ana kallo na."
Zara Mohammed, sakatariyar ƙungiyar Musulman Birtaniya ta Muslim Council of Britain (MCB), ta ce kalaman ƙyamar Musulmai ta ƙaru a kwanan nan.
"A safiyar nan ma na samu saƙonni daga wasu masallatai da suka ce an nuna musu tsana kuma suna magana da 'yan sanda," a cewar Zara. "Kuma muna ganin yadda ake ƙyamar Musulunci a intanet."
Ta ce halin da ake ciki a Gaza na tayar da hankula sosai, amma kamar Talat Ali, ta ce tana fargabar yin magana kamar sauran Musulman Birtaniya.
Da aka tambaye ta game da matsayin ƙungiyar MCB kan Hamas sakatariyar ta ɗan yi jim.
"Ni ba kakakin Hamas ba ce, mu ƙungiya ce ta Musulman Birtaniya kuma ba ma goyon bayan ƙungiyoyin ta'addanci, kuma MCB na ganin ta [Hamas] a matsayin hakan kamar yadda gwamnati ke kallonta," a cewarta.
Hatta tambayar da ake yi wa Musulmai a kan Hamas na cikin matsalolin, in ji ta - kuma Musulman Birtaniya da yawa na fuskantar ta.
"Idan Musulmi ne kai kuma kana magana a kan lamarin, sai a ce maka 'kana goyon bayan 'yan ta'adda ne?".
Da yawa daga cikin Musulmai da Yahudawan Manchester sun nuna rashinb amincewa da kafofin yaɗa labarai da kuma irin harshen da ake yin amfani da shi. Da yawa kuma sun nuna fargabar harin ƙyama.











