Yadda BBC ta bankaɗo gawurtaccen kawalin da ke tilasta wa ƴanmata karuwanci

- Marubuci, Runako Celina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
- Lokacin karatu: Minti 11
Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da abubuwan da suka shafi batsa
Binciken BBC ya bankaɗo wani mutum mai ci da gumin ƴanmata ta hanyar jefa ƴanmata cikin karuwanci a wani garin da ya fi kowanene ɗaukar hankali a Dubai.
Charles Mwesigwa, wanda ya ce shi tsohon direban motar bas ne a birnin Landan, ya shaida wa wakilinmu cewa yana kai ƴanmata bukukuwan jima'i da za a riƙa kwanciya da su a kan farashin da ya fara daga dala 1,000, yana mai cewa da dama ''kan yi bakin ƙoƙarinsu'' domin jan hankalin samarin.
An shafe shekaru ana ta yaɗa jita-jitar samun bukukuwan jima'i a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Inda aka riƙa amfani da yekuwar #Dubaiportapotty, wanda aka kalla fiye da sau miliyan 450 a kan TikTok, yana da alaƙa da fastoci da fallasa jita-jita na mata waɗanda ake zargi da kasancewa masu son kuɗi a asirce suna ba biyan buƙatun rayuwarsu ta hanyar buƙatun jima'i.
An shaida wa sashen binciken BBC cewa abubuwan da ake yi ma sun fi haka.
Wasu ƴan mata ƴan Uganda sun shaida mana cewa ba su yi tsammanin za su yi wa Mista Mwesigwa aikin jima'i ba.
A wasu lokuta, suna tafiya zuwa UAE ne da kyayyawar niyyar yin ayyuka a wurare kamar manyan kantuna ko Otal-otal.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai wani cikin abokan huldar Mista Mwesigwa da ke yawan neman yin ba-haya a kan matan, a cewar "Mia", wadda muka canza sunanta domin kare ta, kuma ta ce tarkon da Mista Mwesigwa ya ɗana ya kamata.
Mista Mwesigwa ya musanta duka zarge-zargen. Ya ce yana taimaka wa matan ne domin su samu masauki ta hanyar masu gidajen haya, sannan ya ce matan kan bi shi wurin bukukuwan ne saboda yadda yake yawan samun kwangiloli a Dubai.
Mun kuma gano cewa wasu mata biyu masu alaƙa da Mista Mwesigwa sun mutu, sakamakon faɗowa daga gini mai tsawo.
Duk da cewa an ayyana cewa su ne suka kashe kansu, ƴan'uwa da abokan arzikinsu sun ce suna ganin yana da kyau ƴansanda su faɗaɗa bincike kan mutuwar tasu.
Mista Mwesigwa ya ce ƴansandan Dubai sun bincike mutuwar tasu, inda ya ce mu tuntuɓe su domin samun ƙarin bayani. To sai dai ba su amsa saƙon buƙatar hakan da muka aike musu ba.
Ɗaya daga cikin matan da suka rasu, Monic Karungi, ta je Dubai ne daga yammacin Uganda.
Ta riƙa kwana ɗaki guda da wasu gomman matan da ke yi wa Mista Mwesigwa aiki, a cewar ɗaya daga cikin matan mai suna Keira, wadda ta ce ta zauna tare da Monic a wurin a 2022.
"[Wurinsa] tamkar kasuwa yake… Za ka iya samun kusan ƴanmata 50. Ba ta ji daɗin abin da ta gani a wurinsa, saboda ba abin da ta yi zato ba kenan,'' kamar yadda Keira ta shaida mana.
Monic ta yi tunanin a babban kantin sayar da kayayyaki za ta yi aiki idan ta je Dubai, a cewar ƴar'uwarta Rita.
"Shi [Mista Mwesigwa] ya riƙa faɗa a lokacin da na ce masa ina son komawa gida,'' in ji Mia, wadda ita ma ta san Munic a Dubai.
Ta ce a lokacin da ta fara zuwa, ya ce mata yana binta bashin dala 2,711, kuma a cikin mako biyu wannan bashi ya sake ninkuwa.
"Kina son kuɗi domin biyan kuɗin jirgi da biza da wurin kwana da kuma abincin da za ki ci," in ji Mia.
"Hakan na nufin dole ki yi aiki tuƙuru, ka'in da na'in da kuma jan hankalin maza domin su kwanata da ke."
Bayan shafe makonni da yawa bashin da Mista Mwesigwa ke bin Monic ya kai dala 27,000, kamar yadda wani ɗan'uwanta da muna sanya wa suna Macheal ya ce ta faɗa masa. Ya ce ta aika maa da saƙon murya a lokacin da take kuka.

Asalin hoton, Family handout
Mia ta shaida mana cewa mafi yawan mazajen da ake hulɗa da su Turawa ne, ciki har da waɗanda ke son biyan buƙatunsu ta wasu hanyoyi.
"Akwai wani mutum da ke yiwa ƴanmatan ba-haya a kansu, sannan ya ce su cinje ba-bahar,'' kamar yadda ta yi ƙarin haske cikin sassanyar murya.
Akwai wata mata da muke kira Lexi, wadda ta ce ta faɗa tarkon wani mutum mai kamanceceniya da labarin Mia, tana mai cewa an yaudareta da samun kuɗi.
"Akwai wani da ya ce: 'Za mu biyaki dirhami 15,000 (dala 4,084) domin mu yi miki fyaɗen taron dangi, mu yi fitsari a fuskarki mu doke ki sannan mu ƙara miki dirhami 5,000 (dala 1,361)" domin mu naɗi bidiyonki a lokacin da kike cin ba-haya.
Wannan ya sa ta yi amanna cewa akwai wariyar launin fata a cikin lamarin.
"A duka lokacin da na ce ba zan iya abin da suke buƙata ba, sai ya zama ni ce ma suka fi sha'awa.Suna son mutumin da zai yi kuka da kururuwa da ma guduwa. Kuma mutumin da suka fi buƙata shi ne baƙin mutum.''
Lexi ta ce ta yi ƙokarin samun taimakon mutanen da take ganin za su iya sanya baki, wato ƴansanda.
To amma ta ce sun faɗa mata cewa: ''Ku Ƴan Afirka ku ke janyo wa kanku matsala. Ba za mu sanya kanmu a ciki ba. Sai kawai suka kashe wayar.''
Mun tuntuɓi Ƴansandan Dubai kan wannan zargi amma ba su mayar da martani ba.
Lexi ta tsallake rijiya da baya, inda ta samu nasarar komawa Uganda, yanzu kuma take taimaka wa ayyukan tallafa wa matan da ke cikin irin yanayin da ta shiga a baya.

Samun Charles Mwesigwa ba abu ne mai sauƙi ba. Mun dai samu hotonsa guda a shafin intanet - an kuma ɗauke shita baya. Yana kuma amfani da sunaye daban-daban a shafukan sada zumunta.
To amma ta hanyar amfani da hanyoyin fasahar zamani da binciken ƙarƙashin ƙasa da kuma bayanai daga tsohon abokin aikinsa, mun yi nasarar gano shi a wata unguwa ta masu hannu da shuni a Dubai da ake kira Jumeirah Village Circle.
Don tabbatar da abin da majiyoyi suka gaya mana game da sana'arsa ta samar da mata don ayyukan lalata - mun aika masa ƴarjarida da ta yi shigar burtu, wadda ta je masa a matsayin mai shirya taruka da ke neman mata don manyan bukukuwa.
Cikin nutsuwa da ƙwarin gwiwa, Mista Mwesigwa ya riƙa yin maganganu game da sana'arsa.
"Muna da ƴanmata kusan 25," in ji shi. "Da dama cikinsu ba su da matsala .... za su iya duk abin da ake buƙata daga gare su.''
Ya bayyana kuɗin da za a biya yanmatan daga dala 1,000 ga kowace a kowane dare, amma idan ana buƙatar wani abu ƙari kan haka, ''za a iya biyan kuɗi''. Ya kuma gayyaci ƴarjaridar don ganin samfurin bukukuwan da yake shiryawa a wani dare.
Da aka tambaye shi game da batun "Dubai porta potty" sai ya ce: Na faɗa miki, ba su da matsala, ba su da matsala tun da har na faɗa miki... za ma aiko miki da hotunansu ki gani.''
A yayin zantawarsa da ƴarjaridar, Mista Mwesigwa ya ce a a baya shi direban bas ne a Landan. Mun kuma ga shaida ƙarara cewa ya taba yin sana'ar aikin a gabshin Landan a 2006.
Ya kuma shaida mata cewa yana ƙaunar sana'ar tasa.
"Ko da caca na ci, na samu miliyoyin fam, zan ci gaba da wannan sana'a.... saboda ta zame mini jiki.''
Troy, wani mutum da ya ce ya yi aiki a matsayin manajan Mista Mwesigwa ya ba mu bayanan yadda ake aiwatar da sana'ar.

Ya ce Mista Mwesigwa na biyan jami'an tsaro a wuraren cashiyar dare domin su bar ƴan matansa su sami abokan hulɗa.
"Na ji labarin nau'in jima'in da ban taɓa ji ba a tsawon rayuwata. Bai damu da hain da za ki shiga ba matsawar bukatun mutanesa masu arziki zza su biya... matan ba su da wata hanyar kuɓuta, akan haɗa su da maaƙa da ƴan ƙwallon ƙafa ko wasu shugabanni.''
Mista Mwesigwa ya samu nasara wajen gudanar da wannan aiki, in ji Troy, saboda ba Troy ba ne kaɗai ake amfani da shi a matsayin direba ba. Ya ce Mista Mwesigwa kuma yana amfani da sunayensu wajen ɗaukar hayar motoci da gidaje, don kada sunansa ya bayyana a cikin takardun.
A ranar 27 ga watan Afrilun 2022, Monic ta wallafa hotonta da ta ɗauka da kanta a Al Barsha - wani ginin matsuguni da ya yi fice tsakanin baƙi a Dubai. Kwana huɗu bayan nan ta rasu. Wannan ya faru ne wata huɗu bayan zuwanta ƙasar.
A cewar Mia, Monic da Mista Mwesigwa sun riƙa samun saɓani a kai a kai a lokacin kafin ta koma gida.
Mia ta ce Monic ta ƙi amincewa da buƙatar Mista Mwesigwa daga nan fice da harƙallarsa.
"Ta ƙara samun wani aikin. Tana cikin murna, tana tunanin ta kuɓuta, rayuwarta za ta dawo yadda take saboda yanzu ta daina sana'ar karuwanci,'' in ji Mia.
Monic ta fice domin komawa wani ginin na daban kusan mintuna goma bayan haka, daga nan ne kuma ta faɗo ƙasa ranar 1 ga watan Mayun 2022.

Asalin hoton, Instagram
Dan'uwan Monic Michael, wanda ke ƙasar UAE a lokacin da ta mutu, ya ce ya yi ƙokarin samun amsoshi.
Ƴansanda sun gaya masa cewa sun dakatar da bincikensu, bayan sun gano ƙwayoyi da barasa a cikin gidan da Monic ya faɗo daga ciki, sai hotunan yatsunata kawai da aka samu a barandar ginin, in ji shi.
Ya samu takardar shaidar mutuwar Monic daga asibiti, amma ba a bayyana yadda ta mutu ba. Kuma danginta sun kasa samun rahoton shan guba daga gare ta ba.
Sai dai wani dan Ghana da ke zaune a gidan ya taimaka masa sosai, in ji shi, inda ya kai shi wani ɓangaren ginin domin ganawa da mutumin da ya ce ubangidan Monic ne.
Michael ya kwatanta lamarin lokacin da ya isa wurin ya ga inda aka ajiye matan.
Ya ce ta cikin giza-gizan hayakin shisha da ke cikin falo, ya hango wani abu kamar hodar iblis a kan teburi da kuma mata ana lalata da su a kan kujeru.
Ya yi iƙirarin cewa ya iske mutumin da muka bayyana da Charles Mwesigwa kwance da wasu mata biyu, kuma lokacin da ya yi yunƙurin kai shi wurin ƴansanda Mista Mwesigwa ya amsa da cewa: "Na shafe shekaru 25 a Dubai. Dubai tawa ce… Babu yadda za a yi a kamani… Mu ne ofishin jakadancin ba wani abin da zai faru.
''Ba Monic ce ta farkon mutuwa ba, haka ma ba ita ce ta ƙarshe ba,'' a cewar Micheal.
Mia da Keira duk sun ce sun shaida wannan tattaunawar kuma dukkansu sun tabbatar da maganarta. Da muka tambayi Mista Mwesigwa me yake nufi da hakan, ya musanta faɗin hakan.
Mutuwar Monic ta yi kamanceceniya da ta Kayla Birungi, wata ƴar Uganda da ke zaune a unguwa ɗaya da ita, kuma ta mutu a shekarar 2021 bayan faɗowarta daga wani babban bene a Dubai wanda muke da shaidar cewa Charles Mwesigwa ne ya kula da shi.
Lambar wayar mai gidanta, wanda dangin Kayla suka ba mu, ta zama ɗaya daga cikin lambobin Mista Mwesigwa.
Troy ya kuma tabbatar da cewa Mista Mwesigwa ne ya kula da gidan, da wasu mata huɗu da muka zanta da su domin gudanar da wannan bincike.

Asalin hoton, Instagram
Ƴan'uwan Kayla sun ce - kamar dai dangin Monic - sun ji labarin mutuwar Kayla, tare da alaƙanta ta da barasa da ƙwayoyi. Sai dai wani rahoton binciken guba da BBC ta gani ya nuna cewa babu wani abu makamancin haka dangane da mutuwarta.
Yayin da dangin Kayla suka sami damar mayar da gawarta zuwa gida da kuma yin jana'izar, ita kuwa Monic ba a mayar da gawar tata ba.
Binciken da muka yi ya gano cewa an binne ta a wani sashe na makabartar Al Qusais ta Dubai da ake kira "The Unknown". Tana da layuka na kaburbura marasa alama, galibi ana zaton na baƙin haure ne waɗanda danginsu ba za su iya mayar da gawarwakinsu ba.
Monic da Kayla sun kasance wani ɓangare na abubuwan da suka haɗa Uganda da Tekun Fasha.
Yayin da Uganda ke kokawa da ƙaruwar rashin aikin yi ga matasa, yin hijira zuwa ƙasashen waje - musamman a ƙasashen Gulf - ya zama wata babbar sana'ar da ke samar da kusan dala biliyan 1.2 na haraji ga ƙasar a kowace shekara.
Amma waɗannan damarmaki cike suke da haɗari.
Mariam Mwiza, 'yar ƙasar Uganda mai fafutukar yaƙi da cin zarafi, ta ce ta taimaka wajen ceto mutane fiye da 700 daga sassan tekun Fasha.
"Muna samun shari'o'in mutanen da aka yi musu alƙawarin yin aiki, an ce, a cikin wani babban kanti, amma daga baya sai a tilasta masa yin karuwanci," kamar yadda ta shaia mana.

Ga dangin Monic, har yanzu suna cikin baƙin cike da fargaba. Fargaba musamman ga sauran iyalai da za su iya samun irin wannan asarar da suka yi, idan ba a yi wani abu ba.
"Dukkanmu muna jimamin mutuwar Monica," in ji ɗan'uwanta Michael. "Amma akwai 'yan matan da ke raye? Suna nan, har yanzu suna shan wahala."
BBC ta nemi Charles Mwesigwa da ya mayar da martani ga zarge-zargen da aka yi a bincikenmu. Ya musanta gudanar da ƙungiyar tilasta karuwanci.
Ya ce: "Duk waɗannan zarge-zargen ƙarairayi ne.
"Na gaya muku ni mai haɗa biki ne kawai, da ke gayyatar manyan masu kuɗi, kuma hakan ne ya sanya ƴanmatan ke yin tururuwa zuwa gareni. Hakan ne ya sa na san ƴanmata da yawa, wannan shi ne kawai."
Ya kuma ce: "[Monic] ta mutu da fasfo dinta ma'ana babu wanda ke buƙatar kuɗinta da zai sa ya ɗauketa. Kafin rasuwarta, sama da makonni huɗu zuwa biyar ban gan ta ba.
"Na san (Monic da Kayla) kuma suna zaune a gidajen haya daban-daban. Idan ba a kama kowa a cikin gidajen biyu ko kuma wani daga cikin masu gidan ba, to akwai dalili. Duka batutuwan nan biyun ƴan sandan Dubai ne suka bincika kuma watakila za su iya taimaka maka."
BBC ta tuntubi ofishin ƴansanda na Al Barsha don neman bayanan da ake tuhumar Monic Karungi da Kayla Birungi, sai dai ba ta amsa wannan buƙata ba ko kuma zargin Monica da Kayla ba a gudanar da bincike mai kyau ba.
BBC ba ta iya ganin wani rahoton binciken guba dangane da Monic Karungi, ko yin magana da mai gidan da take zaune a lokacin da ta mutu.
- Idan kuna da wasu bayanai da za su ƙara wa wannan bincike bayanai, ku tuntuɓe me ta wannan adireshi na email [email protected]
- Ana samun cikakkun bayanai na ƙungiyoyin da ke ba da bayanai game da cin zarafin jima'i ko tare da yanke ƙauna a bbc.co.uk/actionline.











