Tsohon mataimakin shugaban Amurka ya ƙi mara wa Donald Trump baya

Mr Trump da Mr Pence a 2020

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya ce ba zai mara wa tsohon shugaban kasar Donald Trump baya ba a zaben da za a yi a watan Nuwamba.

Mista Pence, wanda ya kawo karshen yakin neman takararsa a watan Oktoba na shekarar da ta wuce, ya ce da hankali da tunaninsa ba zai mara wa Trump ba ya ba.

Shi dai Mike Pence ya yi biyayya ga Donald Trump a lokacin da suke mulki, shugaban kasa da mataimaki, tsakani da gaskiya, kafin su farraka, su samu sabani shekara uku da ta wuce a lokacin da Mista Pence, kememe ya ki bukatar mai gidan nasa ta yin watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na 2020.

A maimakon haka, Mike Pence ya amince da nasarar da Joe Biden ya samu.

Tun daga nan suka kulla, Donald Trump da magoya bayansa ba su yafe wa Mista Pence ba a kan wannan abu da su a wurinsu suke dauka tamkar cin amana.

''Mike Pence ya ce Shugaba Trump ya nemi da in zabi tsakanin shi da kundin tsarin mulki, na zabi kundin tsarin mulki, kuma a kodayaushe zan yi.''

A wata hira da tashar talabijin ta Fox News , tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce, kada wani ya yi mamakin cewa ya ki mara baya ga Mista Trump.

Ya ce ya yanke wannan shawara ne, ba wai kawai a kan abubuwan da suka faru shekaru uku da ta gabata ba, lokacin da magoya bayan Trump suka mamaye ginin majalisar dokokin Amurkar, suna kira da a rataye Mike Pence.

Ya ce ya yi hakan ne saboda gagarumin bambancin manufa da ke tsakaninsa da Donald Trump.

Tsohon shugaban na Amurka ya samu tarin masu mara masa baya a makonnin nan, wadanda suka hada har da tsofaffin masu hamayya da shi, kamar gwamnan Florida

Ron DeSantis – wanda a baya Trump ya kira shi da maras kwarewa, kuma matacce a siyasa.