Biden da Trump sun lashe zaɓen fitar da gwani a Michigan

Asalin hoton, REUTERS
Shugaban Amurka, Joe Biden da abokin karawar sa Donald Trump sun lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyun su, a jihar Michigan.
Sakamakon da aka tattara daga runfunan zaɓen jam’iyyar Democrat da kuma Republican sun nuna cewa ƴan takarar biyu za su kara da juna a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da za a yi cikin watan Nuwamban bana.
Daga alƙalumman da aka tatattara dai, masu zaɓe a jihar Michigan sun zaɓi shugaba mai ci yanzu, da kuma tsohon shugaban Amurkan a matsayin ƴan takarar su a zaɓe mai zuwa.
Sai dai kuma, shugaba Biden ya fuskanci tirjiya daga wasu ƴan jam’iyyarsa masu ƙyamar yadda ya ke goyon bayan Isra’ila a yaƙin da take a Gaza.
Masu sharhi sun ce Mr Biden ya fuskanci wannan tirjiya ne saboda akwai Amurkawa masu tsatson Larabawa masu yawan gaske a jihar Michigan, kuma dama can sun sha alwashin nuna rashin jin daɗin su ga matsayar shugaban Amurkan a kan yaƙin Gaza.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafin sada zumunta, wata mata ƴar asalin Falasɗinu, Rashida Tlaib ta ce ta yi illa ga ƙuri’un da Mr Biden ya samu.
Ta ce: "Ina alfahari da cewa a matsayina na ƴar Demokrat, yau na kaɗa ƙuri’a da ke nuna rashin goyon bayan takarar sa. Dole mu kare dimokuraɗiyyar mu. Dole mu jajirce don ganin gwamnatin mu tana yin abin da muke so. Lokacin da kashi 74 na ƴan Democrat a Michigan suka goyi bayan tsagaita wuta, shugaba Biden bai saurare mu ba. Ta wannan hanya ce za mu yi amfani da turbar dimokuradiyya wajen cewa ya saurari muradun jama’ar Michigan."
A ɓangaren jam’iyyar Republican kuwa, Mr Trump ne ya samu kashi biyu bisa uku, sai kuma Nikki Haley da ke biye da shi a baya, da kashi 30 cikin 100 na ƙuri’un.














