Trump ya sake yin nasara a zaben Republican

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Donald Trump ya yi nasara karo na hudu a zaben fitar da gwani na jam’iyyar Republican, inda alkalumman farko na sakamakon zaben South Carolina suka nuna ya doke abokiyar hamayyarsa da kashi 20.

Sai dai Nikki Haley, ta ce za ta ci gaba da fafutika tana mai cewa galibin Amurkawa ba su ra’ayin Mista Trump ko Shugaba Biden.

South Carolina dai ta fada hannun Trump, kamar sauran jihohin da ya lashe kawo yanzu, wanda hakan ke nuna alamun zai lashe sauran zabukan fitar da gwanin na Republican.

Bayan kidaya rabin kuri’un da aka kada, Dolad Trump ne kan gaba da kashi 20 fiye da abokiyar hamayyarsa Nikki Haley

Da yake jawabi na samun nasara, Mista Trump ya ce bai taba ganin hadin kan Republican ba kamar a yanzu, tare da cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa

“Za mu lashe zabe kuma za mu yi nasara da rinjaye da ba za a taba tunani ba fiye da 2016.

Trump ya kuma shaida wa magoya bayansa cewa, "a shirye nake na kalli Joe Biden a ido na ce, an sallame ka a watan Nuwamba."

Nikki Haley duk da ta taya Donald Trump murnar nasara a South Carolina amma ta ce Amurkawa ba su bukatar Trump ko Joe Biden a matsayin shugabanninsu.

Ta ce ba za ta hakura ba daga fafutikarta domin a cewarta “Amurkawa ba za su iya hakuri da gazawar Joe Biden ba a karin wasu shekaru hudu ko kuma sakacin Trump.

Ta kuma kara da cewa ba ta yi tunanin Donald Trump zai iya doke Joe Biden ba a zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.

Nikkey dai ta sha mamaki a South Carolina inda a baya ta ce daya daga cikin kwarin guiwarta – ba ta taba rashin nasara a zabe ba a jihar.

Sai dai kalubale ne gare ta musamman a zaben tsakiyar Maris yayin da Trump ke kara farin jini a Republican duk da kalubalen shari’a shi ma da yake fuskanta.