Me zai faru bayan gurfanar da Trump?

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya zargi alƙalin da ke masa shari'a Juan Merchan da nuna son rai, bisa tuhumarsa da abin da ya kira marar hujja.

Yayin da yake mayar da martani kan tuhume-tuhumen da ake yi masa, mista Trump ya ce zarge-zargen da ake yi masa maƙarƙashiyar siyasa ce kawai.

"Na gamu da alƙali maƙiyina, wanda iyalansa suka tsane ni'', in ji Trump yayin da yake mayar da martani a gidansa na Mar-a-Lago, bayan kammala zaman kotun.

A ranar Juma'ar da ta gabata Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa alƙalin ''Maƙiyinsa ne''. ba tare yin ƙarin haske ba.

A lokacin zaman kotun mai shari'a Juan Merchan ya gargadi duka ɓangarorin biyu da ke sharia'r da su guji amfani da kalaman da za su iya tayar da hargitsi.

Masu shigar da ƙara sun yi ƙorafin cewa a makon da ya gabata Mista Trump ya yi ta amfani da kamalai masu tsauri.

To sai dai alƙalin bai haramta wa Trump da lauyansa da kuma sauran ɓangaren da ke shari'ar yin magana kan batun a bainar jama'a ba.

Abin da ya faru a cikin kotun

Trump

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da mai shari'a Juan Merchan ya hallara a kotun, kowa ya miƙe ciki har da mista Trump domin nuna girmamawa a gare shi.

Duk da hayaniyar magoya bayansa da ta 'yan jarida da ke gudana a wajen zauren kotun, Alƙali Juan Merchan ya jagoranci shari'ar, ba tare da ya ɗaga muryarsa sosai ba.

An fara shari'ar ne da bayyana matakan da za a bi wajen gabatar da ita, ciki har da ranar da za a koma zaman kotun, da kuma lokacin da aka ware wa lauyoyi domin tattaro hujjoji.

Tsohon shugaban Amurkan ya musanta duka zarge-zarge 34 da aka karanto masa a cikin kotun.

Harabar kotu

Asalin hoton, EPA

Mene ne mataki na gaba bayan tuhumar?

Babu tantama idan aka ci gaba da shari'a, za a kalla a faɗin duniya.

To sai dai bisa ga dukkan alamu, hanyar da aka ɗauko yin shari'ar, na nuna cewa za ta ƙwashe watanni, lamarin da zai sa lauyoyin tsohon shugaban Amurkan su nemi a yi wtasi da ƙarar.

Masu shigar da ƙara za su nemo hujjoji

Ofishin babban alƙalin gundumar Manhattan na gudanar da bincike kan biyan kuɗi ga wata mai shirya fina-finan baɗala da ake tuhumar mista Trump.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu, a yanzu masu shigar da ƙarar za su mayar da hankali wajen tattaro hujjoji da za su gabatar wa kotu.

A ƙarƙashin sabbin dokokin sauye-sauyen da aka yi wa fannin shari'ar ƙasar, wajibi ne mai shigar da ƙara ya kammala tattaro hujjojin da zai gabatar wa kotu cikin kawanaki 35.

Hujjojin kuwa sun ƙunshi tataunawar da jami'an tsaro suka yi da shaidu, da manyan waɗanda ƙarar ta shafa kamar misis Daniels da tsohon lauyan Trump Michael Cohen.

Lauyoyin Trump za su yi ƙoƙarin ganin an yi watsi da ƙarar

Lauyoyi

Asalin hoton, Reuters

Lauyoyin tsohon shugaban Amurkan sun sha alwashin ƙalubalantar zarge-zargen da ake yi masa cikin kwanaki masu zuwa, suna masu cewa tuhumar da ake yi masa ''maƙarƙashiyar siyasa ce''.

Tun daga ranar da aka gurfanar da shi a gaban kotun, lauyoyin na da kwanaki 45, domin kalubalantar tuhume-tuhumen.

Kazalika lauyoyin za su yi yunƙurin ganin an sauya wurin da ake sauraron shari'a zuwa tsibirin Staten daga Manhattan inda ake shari'ar a yanzu.

To sai dai ba lallai ba ne a amince da sauya wa shari'ar matsuguni.