Shugaba Biden na Amurka ya caccaki Donald Trump

Asalin hoton, OTHERS
Shugaba Joe Biden na Amurka ya takarkare wajen kare salon shugabancinsa a jawabinsa na karshe a kan halin da kasar ke ciki, kafin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.
Jawabin na tsawon sa’a daya, wanda ‘yan jamiyyarsa ta Democrat ke yi masa tafi, ya kasance tamkar yakin neman zabe na hamayya tsakaninsa da Donald Trump inda ya rika caccakar tsohon shugaban na Amurka wanda bisa ga dukkan alamu zai kara da shi a zaben na bana.
A jawabin na Shugaba Biden ya rika koda kansa da kansa game da manufofi da salon shugabancin nasa, wanda karara yana son shawo kan ‘yan jamiyyarsa da Democrats, da ke dari-dari a kansa cewa a shirye yake ya gwabza da Donald Trump.
Shugaban mai shekara 81 ya rika suka ga abokin hamayarsa tsohon shugaban kasar, Donald Trump, na jamiyyar Republican da nuna cewa mutum ne da ke son shugabantar Amurka cike da buri na ramuwar gayya da nifaka, abin da ya ce ba ta yadda za ka shugabanci Amurka da irin wannan nufi.
Ta fannin tattalin arziki, Mista Biden ya ce ya gaji tattalin arzikin da ke dab da rugujewa, bayan annobar Korona, to amma ya farfado da shi har ma a yanzu kasar ta zama abar alfahari da neman koyi ga sauran kasashen duniya.
Mista Biden ya kuma yi alkawarin sake dawo da ‘yancin zubar da ciki a tarayya idan har ya samu goyon bayan majalisar dokoki.
A kan batun shige da fice, Mista Biden ya ce ba kamar Mista Trump ba shi ba zai nuna kyama da tsana da bata baki ba.
Game da harkokin da suka shafi kasashen waje kuwa, Shugaba Biden ya tabattar da cewa ya umarci sojojin Amurka su gina wata tasha ta wucin-gadi a bakin tekun Gaza.
Ya ce wannan zai tabbatar da karuwar kayan agaji ga Falasdinawan da ke zirin Gaza.
Ya kuma gargadi Isra'ila a kan ta daina fakewa da taimakon jin kai a matsayin wani sharadi a tattaunawar neman sulhu.
Sannan ya yi kira ga 'yan jam'iyyar Republicans da su amince da wani kudurin doka da aka dade ana jinkirtawa wanda zai samar da karin kayan yaki ga sojojin Ukraine
Kuma ya yi roko ga ‘yan jamiyyar Republicans da su mara masa baya ya shawo kan matsalar kan iyakar Amurka da Mexico.
Yawanci martanin da abokan hamayyarsa ‘yan Republicans suka yi ga jawabin ya mayar da hankali ne a kan batun shige da fice, abin da ake gani kamar wani rauni ne a bangaren shugaban kasar.
Da take mayar da martani ‘yar majalisar dattawa ta Alabama, ‘yar Republicans Katie Britt, ta ce buri ko mafarkin Amurka ya zama abin tsoro a karkashin mulkin Biden.













