Abubuwan da aka fi dubawa a shafin Google a 2022 a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Google ta bayyana abubuwan da mutane suka fi neman bayani a kansu a shafin na matambayi ba ya ɓata a shekarar 2022 da muke bankwana da ita.
Jerin abubuwan da aka fi neman bayani a kansu a shafin sun haɗa da abubuwan ban sha'awa da ke bayyana ƙaguwarmu ta son sanin su.
Ga dai jerin yadda suke:
Wordle da kurket
Wani wasan gem da wani injiniya Josh Wardle ya ƙirƙirarwa budurwarsa a matsayin kyauta a gare ta, shi ne abin da aka fi neman bayani a kansa a shekarar 2022. a shafin Google.
A yayin da gem ɗin Google ya bazu kamar wutar daji tun bayan sakinsa a watan Oktoban 2021, ga alama ƙaguwar mutane ta son sanin bayani kan gem ɗin ya ƙaru sosai ne bayan da kamfanin New York Times ya nemi sayen Wordle daga wanda ya samar da shi a ranar 31 ga watan Janairun 2022.
Wataƙila mutane sun yi ta neman bayani kan yadda za su samu gem ɗin ne bayan da kamfanin NYT ya nemi sayensa.
Abu na biyu da ya yi zarra wajen neman bayani a kansa a shafin Google shi ne fannin wasanni na kurket, wanda har ya sha gaban kalmar Ukraine da bayani kan rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Wasan kusa da na ƙarshe da aka yi tsakanin Indiya da Ingila a Gasar a Gasar Kofin Duniya ta ƴan shekara 20 ranar 10 ga watan Nuwamba shi ne abu biyu mafi girma da aka fi neman bayanai a kansa a wannan shekarar ta 2022.
Shi ma ɗaya wasan da aka yi tsakanin Indiya da Afirka ta Kudu a wajen gasar, ya zamo na biyar da aka fi neman bayanai a kansa.
A cikin labarai

Asalin hoton, Getty Images
Kutsen da Rasha ta yi a Ukraine shi ne abin da aka fi neman bayanai a kansa a fannin labarai, inda ya sha gaban neman bayanai kan rasuwar Sarauniya Elizabeth da kuma batun zaɓen rabin zango na Amurka da zaɓukan Brazil da Philippines.
Damuwar da aka dinga samu kan ɓarkewar annobar cutar ƙyandar biri ya jawo ta zama ta biyar da aka fi neman bayanai a kanta - yayin da cutar korona kuwa ba ta faɗa ko da a cikin goman farko da aka dinga dubawa a shafin na Google ba.
Rikici tsakanin fitatun mutane

Asalin hoton, Getty Images
Rikici da matsalar da aka samu tsakanin taurarin fina-finan Amurka a wannan shekarar ta 2022 ya zama daga cikin batutuwan da aka fi neman bayanai a kansu a Google.
Johnny Depp, wanda shigar da ƙarar matarsa (wadda ita ma ta yi ƙararsa) da kuma abokin aikinsa ɗan wasa Amber Heard, shi ne mutumin da aka fi neman bayani a kansa.
Wata matsalar da aka sake samu a masana'antar fina-finai ta Hollywood ita ce ta gaba da aka fi neman bayani a kai, wato batun yadda Will Smith ya mari Chris Rock.
Heard da Rock ma su ne na biyar da aka fi neman bayani a kansu a Google.
Fina-finan jarumtaka ma sun hau layi

Asalin hoton, Marvel Studios
Fina-finai jarumtaka sun samu koma baya a 2022 - sun gaza zama cikin waɗanda suka samar da kudi sosai a bana kuma sun sha suka daga fitattun daraktoci irin su Martin Scorsese da Quentin Tarantino.
Amma kuma sun yi zarra sosai wajen neman bayanai a kansu: Love and Thunder da kuma Black Adam su ne fina-finan biyu da aka fi dubawa a Google.
Haka shi ma fim din Top Gun: Maverick ya cancanci yabo.
Fim ɗin wanda Tom Cruise ya fito a ciki - shi ne na uku a fina-finan jarumtaka da aka fi kallo fiye da kowanne a sinimomi a 2022.
Pasoori phenomenon

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu kuma sai batun waƙar daka fi lalube a Googlr a 2022 wacce ita ce ta Pasoori, da wasu mawaƙan Pakistan Shae Gill da Ali Sethi suka rubuta.
Sunan da ta yi ya jawo mata ɗaukaka sosai bayan da aka sanya waƙar a shiirn Miss Marvel na Disney Plus.
Waƙar Pasoori ta kuma zo ta biyu a cikin wadanda aka fi neman bayanai a kansu a jerin wakoƙin gargajiya.
Shirin talabijin mai dogon zango

Asalin hoton, AFP
A cikin shekarar da aka ƙaddamar da wasu shirye-shiryen talabaijin masu dogon zango, diramar yara matasa ta Euphoria ce ta zama kan gaba a waɗanda aka fi neman bayanai a kansu a wannan rukunin.
Shirin ne da ke nuna ƙalubalen da yara matasa ƴan shekaru sha ke sgiga.
Sai kuma shirin House of the Dragon da na Game of Thrones da suke biye da shi.
Amma Lord of the Rings bai ma shiga jerin na goman farko ba.











