BBC ta bankaɗo masu saka ƴanmata yin karuwanci a Kenya

Hotuna biyu na nuna matan da ke da hannu dumu-dumu a wannan harƙallar. Hotuna ne da aka ɗauka daga wani bidiyo da aka naɗa a ɓoye. A hannun hagu mace ce da ke kiran kanta Nyambura,cikin dare tana sanye da kayan sanyi launin madara. A hannun dama kuma Cheptoo ce, sanye da rigar jacket da ake iya gani wajen chasu, kofin gilas a gabanta.
Bayanan hoto, Nyambura (Hagu) da Cheptoo (Dama) sun shaida wa masu bincike yadda suke saka yara cikin harkar karuwanci a Maai Mahiu - wata cibiyar sufuri.
    • Marubuci, Njeri Mwangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye in Maai Mahiu
    • Marubuci, Tamasin Ford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
  • Lokacin karatu: Minti 7

Wani binciken sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya bankaɗo yadda mata da ake kira "madams", da TUrancin Ingilishi, suke sanya ƴanmata ƴan shekara 13 cikin harkar karuwanci a Kenya.

A garin Maai Mahiu da ke yanki mai cike da tsauni a Kenya, manyan motoci na cika tituna dare da rana suna sufurin kayayyaki da mutane daga sassan ƙasar zuwa Uganda da Rwanda da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

Cibiyar sufurin, mai nisan kilomita 50 daga gabashin Nairobi, babban birnin ƙasar wuri ne da ya yi ƙaurin suna kan karuwanci, kuma waje ne na ƙyanƙyasar ƙananan yara da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata.

Wasu masu bincike, da suka yi shigar ɓurtu a matsayin mata masu zaman kansu don neman yadda suma za su zama madams, sun shafe watanni a farkon shekarar nan suna laƙantar yadda ake kwana da mata a biya su a garin.

Bidiyon da suka naɗa a asirce ya nuna wasu mata biyu waɗanda suka ce sun san cewa ya sɓa doka inda kuma suka haɗa masu binciken da ƴanmatan da ke cikin wannan harƙalla.

BBC ta miƙa duka hujjojinta ga ƴansandan Kenya a watan Maris. BBC na ganin cewa madams ɗin sun sauya gari tun lokacin. Ƴansanda sun ce ba a iya gano matan da ƴanmatan da muka naɗa ba. Zuwa yanzu babu wanda aka kama.

Ba a cika samun mutum da laifi ba a Kenya. Ƴansanda na buƙatar jin bahasi daga yaran idan ana son ƙarara ta yi nasara. Galibi ƙananan yara masu rauni suna tsoron su yi bayani gaban kotu.

Bidiyon BBC da aka naɗa kan titi cikin duhu ya nuna wata mace, wadda ta kira kanta Nyambura, tana dariya yayin da take cewa: "Har yanzu yara ne, a don haka, abu ne mai sauƙi a shawo kansu ta hanyar ba su alawa."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Karuwanci sana'a ce a Maai Mahiu; masu manyan motocin ke ingiza sana'ar. Kuma ta haka ne muke cin gajiya. Ya riga ya zama abin da aka runguma a Maai Mahiu," in ji ta, tana mai cewa tana da wata yarinya ƴar shekara 13 wadda ta shafe watanni shida tana aikin.

"Ya kan zama da haɗari idan kana hulɗa da ƙananan yara. Ba za ka iya fito da su cikin jama'a ba. Cikin dare kawai nake iya fita da su a ɓoye," in ji Nyambura.

Harkar karuwanci ga babba ba ya cikin manyan laifukan da aka ambata cikin dokokin Kenya amma an haramta harkar a dokokin jihohi. Ba a haramta a Maai Mahiu ba, wanda ke yankin Nakuru.

A ƙarƙashin dokar penal code, haramun ne ka yi rayuwa bisa kuɗin da ake samu daga harkar karuwanci, ko dai a matsayin mata masu zaman kansu ko kuma masu samun tagomashi daga harkar.

Safara ko sayar da ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara 18, laifi ne da aka tanadar wa hukuncin ɗauri na tsawon shekara 10 ko ɗaurin rai da rai.

Da aka tambayi Myambura ko masu amfani da yaran na saka ƙwaroron roba, sai ta ce tana tabbatar da cewa suna samun kariya.

"Wasu yaran na son su samu kuɗi sosai [don haka ba sa amfani da su]. Wasu kuma tilasta masu ake [kar su yi amfani da su]," in ji ta.

A wata ganawar, ta jagoranci masu binciken zuwa wani gida inda wasu ƴanmata uku suka zauna kan kujera, wata kuma a wata kujerar daban.

Sai Nyambura ta fice daga ɗakin, don ta bai wa mai binciken damar yin magana da ƴanmatan su kaɗai.

Sun bayyana yadda ake amfani da su ba ƙaƙƙautawa a kullu yaumin.

"Wani lokacin kana kwana da mutane da yawa. Mazan da ke kwana da mu suna tilasta mana yin wasu abubuwa da hankali ba zai ɗauka ba," in ji ɗaya daga cikin yaran.

Babu alƙaluman na yawan yaran da ake tilastawa yin karuwanci a Kenya. A 2012, rahoton Ofishin Ma'aikatar Harkokin wajen Amurka kan matsalar take haƙƙin bil adama a Kenya, ya ƙiyasta 30,000, ƙididdigar da aka samu daga gwamnatin Kenya da kuma ƙungiyar da ke yaƙi da ɗabi'ar sanya yara cikin harkar karuwanci a Kenya.

Wasu binciken sun mayar da hankali kan wasu yankuna musamman ta gaɓar ƙasar da ya yi fice da ƴan yawon buɗe ido. A rahoton ƙungiyar da ke neman a kawo ƙarshen matsalar bautarwa da aka fitar a 2022, an gano an tilasta yara 2,500 a harkar karuwanci a yankunan Kilifi da Kwale.

Mai bincike ta biyu ta samu yardar wata mata da ke kiran kanta Cheptoo kuma sun gana lokuta da dama da ita.

Ta ce sayar da ƴanmata na nufin za ta samu "kuɗin tafiyar da rayuwarta."

"Kana yin irin wannan sana'ar ne cikin matuƙar sirri saboda an haramta ta," in ji ta.

"Idan mutum ya ce yana son yarinya, ina neman su biya ni. Muna kuma da waɗanda suka saba zuwa da suke dawowa a kai a kai."

Cheptoo ta kai mai binciken zuwa wani wurin chasu domin ta haɗu da ƴanmata huɗu da ke ƙarƙashinta. Ƙaramarsu ta ce shekararta 13. Sauran kuma 15.

Ta fito fili ta yi magana kan ribar da take samu daga gare su, inda ta ce a duk lokacin da ƴanmatan suka samar da 3,000 a kuɗin Kenya, tana samun 2,500 kuɗin Kenya.

A wata haɗuwa da suka yi, a wani gida a Maai Mahiu, Cheptoo ta ƙyale mai binciken da ƴanmata biyu domin su gana.

Ɗaya daga cikinsu ta shaida mata cewa, tana kwanciya da maza biyar kowace rana, shi ne mafi ƙaranci.

Da aka tambayeta me yake faruwa idan ta ƙi kwanciya da manemanta da ba su sa kwaroron roba ba, sai ta ce ai ba ta da zaɓi kan haka.

"Dole na kwanta da su [ba tare da kwaroron roba ba]. Ana kora ta, kuma ba ni da inda zan je. Ni marainiya ce."

Harƙallar karuwanci batu ne mai sarƙaƙiya a Kenya, wata duniya ce inda maza da mata ke da hannu wajen jefa ƙananan yara cikin harkar.

Ba a san yawan ƙananan yaran da aka tilastawa shiga karuwanci a Maai Mahiu ba amma a wannan ƙaramin garin mai yawan al'umma kusan 50,000, abu ne mai sauƙi ka same su.

Wata tsohuwar mata mai zaman kanta da aka fi sani da "Baby Girk", a yanzu tana samar wa ƴanmata mafaka a Maai Mahiu musamman ga waɗanda suka gudu daga harkar karuwanci.

Matar mai shekara 61 ta yi aiki a wannan ɓangare tsawon shekara 40 - farko ta tsinci kanta a harkar tana matashiya ƴar shekara 20. Tana da ciki kuma tana tare da ƙananan yaranta uku bayan ta tsere daga gidan mijinta saboda cin zarafinta.

Ta kai BBC gidanta inda ta haɗa masu binciken da wasu ƴanmata huɗu da dukkansu matan da ake kira madams suka tilasta masu shiga karuwanci a Maai Mahiu a lokacin da suke ƙanana.

Kowace yarinya ta yi bayanin labarinta na rabuwar iyayensu ko kuma irin cin zarafi a gida - sun zo Maai Mahiu domin su tsere daga matsalolin, sai kuma sake tsintar kansu cikin wani zarafin.

Michelle ta bayyana yadda a lokacin da take shekara 12, ta rasa iyayenta sakamakon cuta mai karya garkuwar jiki, aka kuma kore ta inda ta haɗu da wani mutum da ya ba ta wajen zama, daga nan kuma ya riƙa cin zarafinta ta hanyar lalata.

shekara biyu bayan nan, wata mata ta same ta wadda ta kasance madam a Maai Mahiu, inda kuma ta jefa ta cikin harkar kasuwanci.

Lilian, wadda yanzu take shekara 19, ita ma ta rasa iyayenta tun tana ƙarama. Ta samu kanta a wajen wani kawunta wanda yake naɗar bidiyonta a ban-ɗaki yake kuma sayar da hotunanta ga abokansa. Daga nan kuma lamarin ya rikiɗe ya koma yana yi mata fyaɗe.

"Ita ce rana mafi muni a gare ni. A lokacin ina shekara 12."

"Lokacin da ta kuɓuta, wani direban babbar mota ya sake yi mata fyaɗe inda ya kai ta Maai Mahiu. A nan ne, kamar Michelle, ta haɗu da wata mata da ta nuna mata harkar kwana da maza domin a samu kuɗi.

A yanzu da suke zaune a gidan Baby Girl, suna koyon sana'oin hannu - na ɗaukar hoto da gyaran gashi.

Suna kuma taimaka wa Baby Girl a ayyukanta na wayar da kai da take yi wa al'umma.

Nakuru ɗaya daga cikin yankuna mafi yawan masu ɗauke da ƙwayar cutar HIV a Kenya kuma Baby Girl bisa tallafin hukumar Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAID) sun duƙufa wajen ilimantar da mutane kan haɗarin kwana da maza ba tare da kariya ba.

Tana da ofishi a wata cibiyar kula da lafiya ta Karagita kusa da tafkin Naivasha inda take aiki take kuma samar da kwaroron roba da kuma shawarwari.

Sai dai matakin Shugaban Amurka, Donald Trump na janye tallafin da USAID ke bayarwa, na iya kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyarta.

Baby Girl, sanye da rigar sanyi baƙa da farar hula da kuma ɗan kunne launin gwal, tana murmushi yayin da take miƙa kwaroron roba kan wani titi a Naivasha.
Bayanan hoto, A wani ɓangare na ayyukan ƙungiyarta, Baby Girl tana rarraba kwaroron roba a titunan da ke kusa da tafkin Naivasha a yankin Nakuru

"Daga Satumba, za mu rasa aikin yi," kamar yadda ta shaida wa BBC inda ta ƙara da bayyana irin damuwarta kan ƴanmatan da suka dogara a kanta.

"Ka ga irin raunin da waɗannan yara suke da shi. Ta yaya za su iya rayuwa? Har yanzu suna ƙoƙarin warwarewa."

Gwamnatin Amurka ba ta ce komai kan bayanan wannan binciken ba game da irin tasirin dakatar da tallafin. A hukumance an rufe USAID a makon da ya gabata.

Zuwa yanzu, Lilian ta mayar da hankali kan koyon ɗaukan hoto da kuma farfaɗowa daga halin da ta shiga na cin zarafi.

"Kwata-kwata na daina jin tsoro, saboda Baby Girl tana tare da ni," in ji ta. "Tana taimakonmu wajen ganin mun manta da abubuwan da suka faru da mu a baya."